Man United na zawarcin Osimhen, Chelsea na bibiyar Costa

OsimhenOsimhen

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Idanun Manchester United sun koma kan dan wasan gaban Nepoli da NajeriyaVictor Osimhen mai shekara 26, wanda ya ke zaman aro a Galatasaray, su na fatan dauko dan wasan a karshen kakar da muke ciki. (Mirror)

Manchester United din dai na fatan biyan Wolves sama da fam miliyan 65, a matsayin kafin alkalami kan dan wasan gaban Brazil mai shekara 25, Matheus Cunha. (Telegraph)

Manchester City na sanya ido kan Costa da suke fatan zai maye gurbin mai tsaron ragar Brazil Ederson, dan shekara 31, wanda ya ke tattaunawa da wata kungiyar Saudiyya. (Florian Plettenberg)

Arsenal, da Newcastle da Nottingham Forest ma sun nuna shawa'ar dauko Cunha. (Talksport)

Aston Villa ta shirya tsaf domin fafatawa da Arsenal da Manchester City a kokawar dauko matashin dan wasan tsakiya na Norway mai shekara 18, da ke taka leda a Rosenborg, Sverre Nypan. (Times - subscription required)

Ta yiwu Ange Postecoglou zai bar kungiyar Tottenham ko da kuwa sun daga kofin Europa League , sun kuma samu damar shiga gasar Champions League. (Telegraph - subscription required)

Ana rade-radin ɗaya daga cikin masu horas da Bournemouth Andoni Iraola, da na Fulham Marco Silva da Scott Parker na Burnley zai iya zama wanda zai maye gurbin Postecoglou. (Mail)

Bayer Leverkusen ta tattauna da Manchester City kan daukar dan wasan gaba na Ingila James McAtee, mai shekara 22. (Florian Plettenberg)

Lee Carsley da Danny Rohl da kuma Russell Martin na cikin jerin wadanda Leicester ke nazarin ɗauka domin maye gurbin Ruud van Nistelrooy, idan ta sallame shi daga aiki. (Sky Sports)

Chelsea ta bi sahun masu zawarcin mai tsaron ragar Porto Diogo Costa, mai shekara 25, in da za su fafata da Manchester United a kokarin daukar dan wasan na Portugal. (Teamtalk)