'Dole shugaba Buhari ya tabbatar da an daina kai wa Fulani Makiyaya hari a Najeriya'

Asalin hoton, Getty Images
Wata ƙungiya mai rajin kare 'yanci da ci gaban Fulanin Duniya ta sake nanata kira ga Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, ya kafa hukumar bincike don tantance kisan gillar da wani jirgin sama ya yi wa wasu Fulani a jihar Nasarawa.
A cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa da ta rubuta wa shugaban ƙasar, ƙungiyar mai taken FGDRI a taƙaice, ta yi zargin cewa luguden wutar jirgin sama kan fararen hula da ba su ji ba, ba su gani ba irin wanda aka yi na baya bayannan , shi ne na biyar da ya faru a jihar Nasarawa kaɗai cikin 'yan shekarun nan.
Cikin wasilar kungiyar ta zayyana abubuwan da take so shugaban kasa ya yi a kan wannan hari da aka kai wa mutanensu.
Shugaban kungiyar Salim Musa Umar, ya shaida wa BBC cewa, daga cikin abin da suke so ayi shi ne na farko a san yadda za a yi a kula da iyalan wadanda aka kasha na biyu kuma shugaban kasa ya tabbatar da an dauki Matakan hana afkuwar irin wannan aika-aika a kan Fulani makiyaya anan gaba.
Cikin wasiƙar kungiyar ta bayyana tsananin takaici kan biris da shugaban ya yi game da miyagun kashe-kashen gillar, inda ta ce ba a taɓa zaton haka ba a zamanin mulkinsa.
Salim Musa Umar, ya ce abin da aka yi wa makiyayan zalunci ne, saboda tun da farko shanunsu aka kama sannan suka je har Benue suka biya tarar kudi har naira miliyan 29, kuma a bar su su taho da shanunma su biyo daji aka hanasu, aka ce wai shanunsu ba zasu taka kasar Benue ba, ala tilas suka je su dauko motoci suka zuba shanun suka taho da su.
Ya ce,” Bayan sun kai motoci sun dauko shanun sun dawo Nasarawa, aka kuma biyo su aka hallaka shanun har ma da masu wadanda suka biyo shanun.”
Shugaban kungiyar ta FGDRI, y ace,” Ba sau daya bas au biyu ba, ni da kaina na gana da shugaban kasa a shekarun baya bayannan na kuma fada masa irin illoli da ke tattare da abubuwan da ake mana na kasha mana shanu da mutanenmu, amma ba abin da aka yi akai.”
Ya ce, irin wannan abu ba a jihar Nasarawa ya taba faruwa ba, na yi a Kaduna da Neja, to abubuwan sun yi yawa, shi ya sa muka fito mu fadawa duniya ta hanyar rubuta wannan budaddiyar wasika.
Salim Musa Umar, ya ce, akwai wani dattijo da ya rasa ‘ya’yansa tara a cikin wannan hari da aka kai abin ga tausayi ga kuma takaici, don ko magana ba ya iya yi.
Ya ce, “ Abin haushin ma su wadannan mutane da aka kashe matasa ne majiya karfi da suka je su taimaka a sauke shanun da aka karbo amma aka yi musu wannan aika-aika.”









