Wasa shida da aka ci Man United kwallaye a Premier duk a Oktoba

Asalin hoton, Getty Images
Ranar Lahadi Manchester City ta doke Manchester United da ci 6-3 a wasan hamayya a gasar Premier League karawar mako na takwas kakar 2022/23.
Phil Poden da Erling Haaland ne kowanne ya ci uku-uku a raga, sai United ta ci kwallo biyu ta hannun Anthony Martial da kuma De Santos.
Magoya bayan United ba za su manta da watan na Oktoba da kuma sakamakon karawar da suka yi a Etihad ba.
To sai dai kuma kafin wannan fafatawar an ci United kwallaye da yawa a gasar Premier kuma a cikin watan Oktoba.
Tun bayan da aka sauya fasalin gasar Premier United a 1992/93 an zazzaga kwallaye da yawa a ragar United a wasa shida kenan kuma duk a cikin watan Oktoba.
Jerin wasannin da aka ci United kwallo da yawa a Premier:
Ranar 20 ga watan Oktoban 1996 - Newcastle 5-0 Man United
Kafin fara wasan a kakar 1996/97 United ta doke Newcastle da ci 4-0 a Charity Shield, karawar da ake yi don bude labulen kakar gasar Premier League.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wata biyu tsakani shi ne suka kara fuskantar juna karkashin jagorancin Sir Alex Ferguson, inda Newcastle ta ci United 5-0 a St James Park.
Tun kan hutu Darren Peacock da David Ginola suka ci kwallo kowanne.
Daga baya Les Ferdinand ya kara, bayan da suka koma zagaye na biyu, sai Alan Shearer ya ci na hudu daga baya Philippe Albert ya kara na biyar
Ranar 3 ga watan Oktoban 1999 - Chelsea - Chelsea 5-0 Man United
United ta ziyarci Stamford Bridge a lokacin da take kan ganiya - bayan da ta yi wasa 29 ba a doke ta ba tun daga Disambar 1998.
A lokacin tana rike da kofin, sai dai cikin dakika 30 da fara wasa Gus Poyet ya zura kwallo a ragar United.
Golan United ne Massimo Talbi ya je ya yi karo da mai tsaron baya Denis Irwin, inda Poyet ya samu kwallo cikin ruwan sanyi ya zura a raga ba kowa a ciki.
Minti 15 tsakani Chris Sutton ya kara na biyu - an kuma bai wa Nicky Butt jan kati, bayan keta da ya yi wa Dennis Wise.
Daga baya Poyet ya ci kwallo tare da Jody Morris, yayin da Henning Berg na United ya ci gida aka tashi karawar Chelsea da nasara 5-0.
Ranar 23 ga watan Oktoban 2021 - Man United 1-6 Man City
Mario Balotelli ne ya fara cin United a wannan wasan na hamayya, haka kuma aka je hutu, kungiyar da Roberto Mancini ke jan ragama tana da 1-0.
Bayan da aka koma zagaye na biyu kuma United tana gara kwallo, sai aka bai wa Jonny Evans jan kati minti biyu da komawa zagaye na biyu, bayan keta da ya yi wa Balotelli.
Daga nan aka ga barakar United, inda Balotelli ya kara, sannan Sergio Aguero ya zura kwallo a raga - wasa ya koma 3-0
Darren Fletcher ne ya zare wa United kwallo daya.
Saura minti daya lokaci ya cika kafin alkalin wasa ya tashi karawar, sai City ta kara uku a raga ta hannun Edin Dzeko da ya ci biyu da kuma David Silva.
Shi ne wasan da aka doke United kwallaye da yawa a gida tun bayan 5-0 da Manchester City ta yi mata a 1955.
Kuma karon farko da aka ci United shida a Old Trafford, tun bayan 6-0 da Huddesfield ta yi da wanda ta sha kashi da ci 7-4 a hannun Newcastle United kwana hudu tsakani duk a 1930.
Ranar 4 ga watan Oktoban 2020 - Man United 1-6 Tottenham
Bruno Fernandes ne ya fara ci wa United kwallo a bugun fenariti a minti na biyu da fara wasa, bayan da Davinson Sanchez ya yi wa Anthony Martial keta.
Daga baya aka bai wa Martial jan kati a minti na 20, bayan ketar da ya yi wa Erik Lamela a lokacin ana cin United 2-1.
Kuma Tanguy Ndombele da kuma Son Heung-min ne suka ci wa kungiyar da Jose Mourinho ke jan ragama kwallayem.
Kafin hutu Harry Kane da Son suka kara cin kwallae, inda Tottenham keda 4-1.
Suna komawa zagaye na biyu Sege Aurier ya kara na biyar, sannan Kane ya ci na biyu a wasan kuma na shida a karawar.
Ranar 24 ga watan Oktoban 2021 - Man United 0-5 Liverpool
Shekara 10 da kwana daya bayan da United ta sha kashi a hannun City 6-1 a Old Trafford.
Sai Liverpool ta ziyarci United a wasan Premier, kuma minti biyar da fara wasa sai Naby Keita ya ci wa Liverpool kwallo.
Diogo Jota ya kara na biyu a minti na 13 daga nan Mohamed Salah ya zura biyu a raga.
Daga nan magoya bayan United suka yi ta yi wa 'yan wasansu ihu tun kan hutu a gaban 'yan kallo 73,000.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Salah ya ci kwallo na uku rigis a karawar - an kuma bai wa Paul Pogba jan kati a wasan.
Wasan da ya ja aka kori kociyan United, Ole Gunnar Solskjaer kenan.











