''Ba matsala koda Enzo ya koma Chelsea bayan zargin wakar wariya''

Enzo Fernandez

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kocin Chelsea, Enzo Maresca ya ce baya jin za a samu wata matsala, idan Enzo Fernandez ya koma Chelsea ranar Litinin.

Chelsea tana Amurka, inda za ta buga wasannin sada zumunta don tunkakar kakar 2024/25.

Ƙungiyar Stamford Bridge ta sanar cewar za ta ɗauki matakin shari’a kan ɗan wasan, bayan wani bidiyon tawagar Argentina da take rera waka, bayan lashe Copa America.

Hukumar ƙwallon kafar Faransa tana zargin ɗan wasan mai shekara 23 da wallafa bidiyon a kafar sada zumunta, mai dauke da cin zarafin kasar.

Waƙar ta ƙunshi waƙoƙin da ke tambayar al'adun baƙar fata waɗanda ke gauraye da 'yan wasan Faransa.

Abokin wasan Fernandez a Chelsea, Wesley Fofana, wanda ya buga wa Faransa wasa daya, ya saka hoton bidiyon a shafin Instagram, yana mai bayyana shi a matsayin "wariyar launin fata da ya kamata a kaucewa hakan".

Fifa ta fara bincike kan lamarin, inda daga baya Fernandez ya nemi afuwa.

Maresca ya ce: "Abu ne mai sauki dangane da dan wasan, wanda ya nemi afuwa kan abinda ya faru. Haka kuma kulob din shima ya yi hakan, don haka ba na jin akwai wani abu zai faru dangane da lamarin. Tuni aka fito fili aka fayyace komai."

Da aka tambaye shi ko za a samu matsala a cikin kungiyar, inda Chelsea ke da ‘yan wasan Faransa bakwai wadanda bakar fata ne, Maresca ya amsa da cewa: “Bana tunanin haka, dukkansu mutane ne, bana jin akwai wani mugun abu ko bakar niyya daga kowannensu.

"Bana tunanin idan Enzo ya dawo za mu sami wani yanayi mara ƙyau, Enzo ya fayyace lamarin, kungiyar ma haka, don haka babu abin da zai faru. Su ba miyagun mutane bane, kuma ƙwararrun ƴan wasa ne.''.

"Komai zai iya faruwa amma bana jin akwai wata matsala ko kadan, na yi magana da Enzo da dukkansu."