Matakan da za su sauya rayuwar 'yan Najeriya a 2025

Asalin hoton, UNHCR
Kowace shekara da yadda take zuwa dangane da yadda sauya rayuwar mutane.
Gwamnatocin ƙasashe a matakai daban-daban kan ɓullo da matakai a lokuta da dama da ke sauya rayuwar al'umominsu ta hanyar da ta dace ko akasin haka.
Haka batun yake ma a Najeriya, inda gwamnatin ƙasar ta zo da wasu tsare-tsare da ka iya yin tasiri a rayuwar 'yan kasar a sabuwar shekarar.
To sai dai cire tallafin man fetur da shugaban ƙasar ya yi tun a ranarsata farko bayan rantsar da shi, da kuma barin naira ta nemar wa kanta daraja a kasuwa, sun yi matuƙar tasiri wajen haifar da matsin rayuwa da hauhawar farashi a ƙasar.
Lamarin da ya sa wasu masana ke ganin cewa da wuya duk wasu matakai da gwmanatin ƙasar ta ɗauka su yi tasiri wajen rage matsin rayuwar da ake ciki.
A wannan maƙala mun duba wasu daga cikin tsare-tsare da manufofin gwamnatin Najeriya da za su sauya rayuwar 'yan ƙasar a wannan shekarar ta 2025
Dakta Murtala Adogi Muhammad, shugaban cibiyar System Trategy and Policy, wata cibiya mai zaman kanta da ke taimaka wa manya-manyan ma'aikataun gwamnati da ƙungiyoyi masu zaman kansu da ke tallafa wa Najeriya, ya ce akwai tsare-tsaren da za su sauya rayuwar 'yan Najeriya a 2025.
''Akwai tsare-tsaren da shugaban Najeriya Bola tinubu ke koƙarin ɓullo da su waɗanda kuma in har aka aiwatar da su to ko shakka babu za su sauya rayuwar 'yan Najeriya a a shekarar mai kamawa'', in ji shi.
'Rage hauhawar farashi zuwa kashi 15'

Asalin hoton, Getty Images
Dakta Adogi ya ce a jawabin da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gabatar a gaban majalisar dokokin ƙasar, lokacin da yake gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2025, ya alƙawarta cewa zai rage hauhawar farashin kayyaki a ƙasar zuwa kashi 15 cikin 100.
Hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya dai ya kai kashi 34.60 a watan Nuwamba, kamar yadda alƙaluman da hukumar ƙididdiga ta ƙasar suka nuna.
''To sai dai shugaban ƙasar ya alƙa warta rage alƙaluman zuwa kashi 15 cikin 100, sai dai bai bayyana wani mataki da zai dauka ba wajen cimma hakan'', in ji Dakta Adogi.
Masanin ya kuma ce idan har shugaban ƙasar ya cimma wannan ƙuduri, to haƙiƙa hakan zai yi tasiri matuƙa wajen sauya rayuwar 'yan Najeriya.
'Bai wa ɓangaren tsaro fifiko'

Asalin hoton, Defence HQ/X
A ranar 18 ga watan Disamba ne shugaban Najeriya ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2025, wanda a ciki ɓangare tsaro ya fi samun kaso mai tsaro ya samu kaso mafi tsoka.
A kasafin kuɗin shugaba Tinubu ya ware wa ɓangaren tsaron naira tiriliyan 4.91, fiye da adadin da aka ware wa ɓangaren a kasafin da ya gabata.
Dakta Adogi ya ce ''idan aka aiwatar da wannan kasafi yadda ya dace to ko shakka babu za a samu sauƙin matsalar tsaro da Najeriya ke fuskanta''.
''A yanzu a Najeriya babu abin da yake ci wa 'yan Najeriya tuwo a ƙwarya ba zai wuce matsalar tsaro ba, to indai aka magance wannan to lallai rayuwar 'yan najeriya za ta inganta'', in ji dakta Adogi.
'Tsare-tsaren inganta noma'

Asalin hoton, Getty Images
Dakta Adogi ya ce gwamnatin Bola Tinubu ta ƙudiri aniyar ingantar harkokin noma domin wadata ƙasa da abinci.
''Gwamnati ta ɓullo da tare-tsaren inganta harkokin noma, ta hanyar fito da shirye-shirye tallafa wa harkokin noma, kamar raba taki da bayar da rance da kayan aiki ga manoma''.
Haka ma gwamnatin Shugaba Tinubu ta ƙullar yarjejeniyoyin noma da kasuwanci da wasu ƙasashen waje, waɗanda masana ke ganin in dai an zartar da su to za su taimaka wa rayuwar 'yan ƙasar.
''Haka ma, kamar yadda na ce maka, shugaban ƙasa ya ware wa ɓangaren tsaro kaso mafi tsoka, kuma matsawar tsaron ya inganta ta harkokin noma za su inganta manoma za su koma gona, abinci zai wadata, wanda kuma shi ne babban abinda 'yan Najeriya ke fatan samun wadatuwarsa domin samun sauƙin rayuwa'', in ji Dakta Adogi.
Ƙudurin haraji

Asalin hoton, Presidency
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wani da zai kasance kan gaba wajen yin tasiri wajen sauya rayuwar 'yan Najeriya shi ne ƙudirin haraji da shugaban ƙasa ke son majalisar dokokin kasar su amince da su.
Ƙudirin ya ƙunshi yadda za a riƙa karɓar haraji da yadda za a riƙa kasafta shi tsakanin jihohin ƙasar da matakan gwamnati daban-daban.
Sabon ƙudirin harajin kamar yadda masana suke bayana ya yi tanadin cewa za a riƙa karɓar harajin kaya na VAT a inda shalkwatar kamfanoni ko bankuna suke, ba inda aka fi amfani da su ba.
Haka ma ƙudirin ya yi tanadin cewa idan aka zo kasafta harajin jihohin, waɗanda suka fi tara harajin su ne za su tashi da kaso mafi yawa fiye da wadanda ba su tara da yawa ba.
Abin da ya sa masana ke cewa jihohin Legas da Rivers da Ogun da Delta za su fi cin ribar hakan saboda yawaitar manyan kamfanoni a jihohin, saɓanin jihohin arewacin ƙasar inda ke da ƙarancin kamfanoni.
''To ka ga a ashe jihohin Legas da Rivers da sauran jihohin da ke da manyan kamfanoni za su amfana, za su samu kuɗi masu yawa, kuma rayuwar al'u,mominsu za ta sauya sosai'', in ji Dakta Adogi.
''Amma saɓanin haka wasu jihohin arewa za su samu ƙarancin kuɗin shiga kuma hakan zai shafi al'umominsu, za a kasa ɗaukar ma'aikata za a kasa gudanar da ayyukan more rayuwa'', in ji shi.
Daina bayar da tallafin aikin Hajji

Asalin hoton, NAHCON
A farkon watan Oktoban 2024 ne gwamnatin najeriya ta sanar da cire hannunta daga aikin hajjin 2025.
Hukumar aikin Hajji ta Najeriya, NAHCON ta ce gwamnatin tarayya ba za ta iya ci gaba da biyan tallafi a aikin hajjin 2025 ba.
Cikin wata sanarwar da mai magana da hukumar, Fatima Sanda Usara ta fitar, ta ce "An daina bai wa jama'a tallafin rangwamen farashin dala ga maniyyata a jihohi da tarayya."
Alhaji Nasidi Yahaya Sulaiman wani masanin harkokin aikin Hajji da Umra ya ce abin da hakan yake nufi shi ne farashin aikin hajji a shekarar 2025 zai fi na kowace shekara.
"Ya danganta da farashin dala tunda farashinta ba a tsaye yake ba. Kenan idan aka tafi a farashin da take kai a yanzu kuɗin kujerar zai iya kai wa naira miliyan 10. Zai ma iya fin hakan idan dalar ta tashi. Misali idan farashin dalar ya kai naira 2000 kamar yadda muka gani a baya to farashin kujerar aikin Hajjin ka iya fin naira miliyan 10."
Ko a aikin hajjin 2024 sai da gwamnatin tarayya ta bayar da tallafin kuɗi har naira biliyan 90 domin gudanar da aikin ibadar ba tare da tsawwalawa ba.
Da ma dai gwamnati na ba da tallafin ne ta hanyar karyarwa da maniyyata farashin dala a babban bankin Najeriya.
Hakan ya sa masana ke ganin kuɗin aikin hajjin wannan shekara ka iya kai wa naira miliyan 10.










