Ba zan manta da Bayern Munich ba - Lewandowski

Asalin hoton, Getty Images
Robert Lewandowski na ban kwana da Bayern Munich, bayan da yake shirye-shiryen komawa Barcelona da taka leda a kakar bana.
A karshen mako Bayern Munich ta sanar cewar ta cimma yarjejeniya da kungiyar Sifaniya, kan cinikin Lewandowski.
Dan kwallon tawagar Poland ya yi godiya a kafar sada zumuntarsa a Instagram ga abokan taka ledarsa a Jamus da mahukuntan Bayern Munich da dukkan wadanda suka marasa masa baya.
Dan wasan ya yi kaka takwas a Bayern da lashe Bundesliga a kowacce kaka da daukar Champions League a 2020.
A zamansa a kungiyar Jamus ya karya tarihin yawan zura kwallaye a raga da lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na duniya na Fifa karo biyu.
Wasu rahotanni da jaridu suka wallafa sun ce mai shekara 33, zai sa hannu kan yarjejeniyar kaka hudu a Camp Nou kan yuro miliyan 45.
Tuni Bayern Munich ta dauki Sadio Mane daga Liverpool a kakar nan, wanda ya maye gurbin Lewandowski
Shi kuwa Serge Gnabry ya saka hannu kan kwantiragin cin gaba da taka leda a Bayern Munich zuwa karshen kakar 2026.










