Atletico ta kasa samun tikitin shiga Europa League

Asalin hoton, Getty Images
Atletico Madrid ta kasa samun gurbin shiga Europa League, bayan da ta yi ta karshe a rukuni na biyu a Champions League.
Atletico ta yi rashin nasara a gidan Porto da ci 2-1 ranar Talata a wasan karshe a cikin rukuni a babbar gasar Zakarun Turai ta kakar nan.
Kungiyar Sifaniya ta sa ran kai wa zagayen gaba a Champions League tun bayan da ta tashi canjaras da Bayern Leverkusen a makon jiya.
Porto ta ci kwallon ta hannun Mehdi Taremi da kuma Stephen Eustaquio, sannan Ivan Marcano ya ci gida, kuma hakan bai wa Atletico damar da take bukata ba.
Wannan shi ne karon farko da Diego Simeone ya yi na karshe a teburi a Champions League tun bayan da ya karbi aikin horar da kungiyar a 2011.
Kungiyar ta yi nasara a karawa hudu daga 12 da ta fafata a dukkan wasannin bana, tana ta ukun teburin La Liga da tazarar maki tara tsakaninta da Real Madrid ta daya.
Atletico ta ci karo da koma baya ne, bayan da wasa tsakanin Leverkusen da Club Buges suka tashi 0-0 ranar Talata.
Hakan ya sa Porto da Club Bruges suka kai zagayen gaba, kungiyar Jamus ta uku aka bar ta Sifaniya ta karshen teburi.
Sauran gasar Champions League da aka fitar da Atletico Madrid daga cikin rukuni sune a 2009-10 da kuma 2017-18 - a kakar da ta koma buga Europa ta kuma lashe kofin.









