'Ba zan yi shiru ba, ko da za su kashe ni'

Farfesa Ismail Mashal
Bayanan hoto, Farfesa Ismail Mashal
An wallafa

"Ina kira ga iyaye maza su kama hannuwan yaransu mata su kai su makaranta da kansu, koda kuwa ƙofofin makarantun a rufe suke."

Farfesa Ismail Mashal, wanda ya mallaki wata jami'a mai zaman kanta a birnin Kabul, ya ce ya gaji da irin ƙa'idojin da ake ƙaƙaba wa mata a Afghanistan.

Yana bayyana hakan ne tare da nuna takaici kan irin halin da ake ciki, da kuma nuna bijirewa.

Ya shaida wa BBC cewar "ya kamata su rinƙa yin haka a kullum - koda kuwa an haramta. Wannan ne abu na ƙarshe da za su yi a matsayinsu na maza."

"Ba wai ina magana saboda kawai ɓacin rai ba ne - saboda takaici ne. Wajibi ne ga maza su tashi su kare ƴancin mata da yara mata na Afghanistan."

A watan Disamba ne gwamnatin Taliban ta ce ba za a ƙara barin ɗalibai mata su halarci jami'o'i ba, har sai abin da hali ya yi. Gwamnatin ta ce ta ɗauki matakin ne domin ba ta damar samar da tsari na ilimi wanda ya yi daidai da shari'ar musulunci, ciki kuwa har da sauya manhajar karatu.

Jim kaɗan bayan wannan sanarwa sai bidiyon farfesa Mashal ya yaɗu a shafukan intanet, inda ya yaga takardun shaidar kammala karatunsa kai-tsaye a shirin talabijin, yana cewa neman ilimi ba ya da amfani a wannan zamanin a Afghanistan.

Ya ce ba zai yi shiru ba a kan lamarin.

Farfesa Mashal ya ce "alƙalamina shi ne ƙarfina, ba zan yi shiru ba koda za su kashe ni, koda za su gunduwa-gunduwa da ni."

"Na san abin da nake yi yana da haɗari. Kullum da safe nakan yi bankwana da mahaifiyata da matata, nakan ce masu akwai yiwuwar ba zan dawo ba. Amma a shirye nake na sadaukar da raina kan matan Afghanistan, yara da manya, su miliyan 20, da kuma makomar yarana biyu.

Jami'ar da farfesa Mashal ya mallaka na da ɗalibai mata 450, waɗanda ke karatun aikin jarida, da tattalin arziƙi da kuma fasahar kwamfuta.

Ministan ilimi na Taliban ya ce ba za a rinƙa koyar da waɗannan fannoni ga mata ba, domin sun saɓa wa addinin islama da al'adar al'ummar Afghanistan.

Farfesa Mashal yana da wata jami'a a birnin Kabul
Bayanan hoto, Farfesa Mashal yana da wata jami'a a birnin Kabul
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Farfesa Mashal ya ce a yanzu ya rufe jami'arsa, duk kuwa da cewa in da ya so zai iya ci gaba da tafiyar da karatu a jami'ar da ɗalibai zalla.

Ya ce "ko dai a bai wa kowa ilimi, ko kuma a daina gaba ɗaya. Na shiga cikin damuwa tun bayan da na kulle jami'ata.

"Waɗannan mutane na wasa da makomar yaranmu mata. Ɗalibaina kan kira ni su tambaye ni yaushe ne za su koma karatu.

Ba ni da amsar da zan iya ba su. Ba na da bayanin da zan yi wa ƴata ƴar shekara 12 wadda ba za ta iya zuwa babbar makaranta ba a shekara mai zuwa. Tana tambaya na, wane laifi ne ta aikata?"

Ya fuskanci barazana da dama tun bayan da ya bayyana a kafar talabijin da bayanansa. Amma duk da haka kusan kullum farfesa Mashal kan shiga kafafen yaɗa labaru na cikin gida yana bayani. Yana sa ran cewar hanƙoron da yake yi zai yaɗu a faɗin ƙasar.

To amma mece ce yiwuwar cewa maza za su bi sawunsa a wannan ƙasa mai bin al'ada sau-da-ƙafa?

Ko a cikin gwamnatin Taliban akwai waɗanda ke adawa da haramta wa mata zuwa makaranta - sai dai da yawansu ba su fito fili sun bayyana hakan ba.

A matsayin martani ga dokar, matan Afghanistan da dama sun hau kan tituna suna zanga-zanga a yunƙurin ƙwato hakkinsu.

Duk da cewa akasarin waɗanda ke gudanar da zanga-zangar mata ne, ɗalibai maza da manyan malamai sun fara ƙarfin halin fitowa suna faɗin albarkacin bakunansu - wasu ta hanyar ƙin rubuta jarrabawa, wasu kuma ta hanyar ajiye ayyukansu.

Farfesa Mashal ya ce ya kasa gane manufar Taliban na sanya wa mata takunkumi tun bayan karɓe mulki.

Ya ce "ya isa haka, ku ƙyale matan nan haka. Akwai matsaloli da dama da suka kamata a magance. Ba a bin doka a kasar nan, ana rayuwa ce tamkar ta dabbobi."

Farfesan, wanda tsohon ɗan jarida ne ya ce yana magana da ɗalibansa mata a ka-a kai, waɗanda dokar hana ilimin ta dame su sosai, kuma yana jin tsoron halin da za su iya shiga na damuwa.

Ɗaya daga cikin ɗalibansa mai suna Shabnam, wadda take karatun ilimin tattalin arziƙi - fannin da Taliban ta ce bai kamata mata su karanta ba, ta ce ba za ta taɓa mantawa da ranar da sojojin Taliban suka je makarantar suka ce masu ba za su iya ci gaba da ɗaukan darasi ba.

Duk da halin damuwa da Shabnam take ciki, ta yaba wa matakin farfesa Mashal.

Ta ce "wannan lokaci ne da mata, yara da ƙanana na Afghanistan ke ganin cewa kamar an bar su su kaɗai. Babu maza da yawa da suke fitowa su yi adawa da lamarin. Muna jin tsoron kada a cutar da shi, amma kuma muna gode masa saboda goyon bayanmu da yake yi."