Man City da Arsenal da Liverpool na rige-rigen daukar Rodrygo, Everton na zawarcin Eyong

Rodrygo,

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, ,
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester City na ci gaba da zawarcin ɗan wasa mai kai hari dan kasar Brazil mai shekara 24, wanda Real Madrid ta yi kiyasin darajarsa ta kai yuro miliyan 80. (ESPN), external

Ita ma Arsenal na sha'awar Rodrygo, kuma Liverpool na son daukarsa domin maye gurbin ɗan wasan Colombia Luis Diaz,mai shekara 28,wanda ya koma taka leda a Bayern Munich a farkon bazara . (Teamtalk), external

Ange Postecoglou da Jose Mourinho na cikin wadanda suke neman aiki a Nottingham Forest idan an kori Nuno Espirito Santo. (Sun), external

Real Madrid na zawarcin dan wasan tsakiya na Crystal Palace da Ingila Adam Wharton mai shekara 21. (AS - in Spanish), external

Ga dukkan alamu Aston Villa za ta rasa dan wasa gaba na Senegal Nicolas Jackson, mai shekara 24, saboda kudin fan miliyan 70 da Chelsea ke son a biyata kan iya kawo cikas . (Sun), external

.Ana sa ran dan wasan Kamaru Andre Onana, mai shekara 29, zai ci gaba da zama a Manchester United, duk da rashin tabbas kan makomarsa da kuma rade-radin da ake yi cewa kungiyar na iya daukar golan Royal Antwerp dan kasar Belgium Senne Lammens, mai shekara 23.(Mail), external

Antwerpna son a biya ta kusan fan miliyan 17 domin cefanar da Lammens, wanda kawo yanzu ya kasa yi wa kasarsa ta Belguim wasa . (Sun), external

Tottenham ta shirya tsaf don yin tayin sama da fan miliya 60 ga dan wasa mai kai hari na Machester City da Brazil Savinho mai shekara 21 . (Fabrizio Romano), external

West Ham ta mika tayin neman dan wasan Monaco Soungoutou Magassa, mai shekara 21, kuma tana kokarin kammala cinikin dan wasan tsakiyar Faransa na kasa da 'yan shekara 21.(Guardian), external

Amma Monaco ta ki amincewa da tayin farko, wanda ya kai kusan fam miliyan 14 da kuma karin fam miliyan 2.6 , kodayake suna tsammanin Hammers za ta dawo da wani sabon tayi.

Everton ta tuntubi Villarreal kan yiwuwar kulla yarjejeniya da dan wasan gaban Kamaru Etta Eyong mai shekaru 21. (El Chiringuito - in Spanish)