Turmutsutsu: Gwamnatin APC ce ta jefa jama'a cikin talauci - PRP

Asalin hoton, FCT Police Command
Jam'iyar hamayya ta PRP a Najeriya ta yi Allah-wadarai kan turmutsutsun da ya faru a jihar Anambara da Oyo da kuma babban birnin tarrayar kasar, Abuja, wanda ya yi sandin mutuwar jama'a da dama da su ka je karbar shinkafar shagulgullan Kirstmeti.
A cewar jam'iyyar mawuyacin halin da aka saka 'yan Najeriya a ciki ne ke haifar da irin wannan yanayi.
Kwamared Muhammad Ishak wanda shi ne sakataren watsa labarai na jam'iyyar ya sheda wa BBC cewa wannan irin lamari ba komai yake nunawa ba illa irin bakin talauci da kunci da jama'ar kasar ke fama da shi.
Ya ce ko da ana asamun irin haka a wasu kasashe to bai kamata a ce ana samun irin wannan bala'i ba a kasa kamar Najeriya mai dimbinarziki in banda an jefa mutane cikin mawuyacin hali.
Ishak ya ce abu ne da ya wajaba gwamnatocin kasar a kowane mataki, kama daga kananan hukumomi da jihohi da kuma gwamnatin tarayya su tashi tsaye su ga sun rage wa jama'a radadin talaucin da yake damunsu.
Ya ce matakin farko da gwamnati za ta dauka shi ne ta ga ta tallafa wa iyalan mutanen da lamarin ya rutsa da su : ''Tun da yawanci magidanta ne mata sun bar yara da sauransu, to ya kamata gwamnati ta duba ta ga me ya kamata ta yi musu musamman iyalan da suka bari a baya.''
''Sannan na biyu shi ne babban mataki, wanda ya kamata gwamnati ta dauka na ganin ta rage radadin bakin takauci da kunci da jama'a ke ciki, domin duk lokacin da ka ga a kan shinkafa an je ana turereniya har ana rasa rayuka wannan manuniya ce cewa jama'a na cikin kunci,'' in ji shi.
Ya ce sau da yawa za su fito su ce jama'a suna cikin kunci amma gwamnati za ta fito ta musanta ta ce ba haka ba ne, ta ce tana kokari, talauci na raguwa.
Ya kara da cewa, '' wannan duk shaci-fadi-ne, ga zahiri nan mtane suna mutuwa a layin karbar shinkafa.
Kwamared ya ce kuma wannan ba shi ba ne karo na farko, domin a azumin da ya wuce an rasa dimbin rayuka a wajen rabon kudi naira dubu goma-goma.
Ya ce in dai ba an tashi tsaye an dauki kwakkwaran mataki ba, an rage wa jama'a irin kuncin da suke ciki wannan zai ci gaba da faruwa, ''wanda kuma ba fata muke ba, muna kira ga gwamnati a kowane mataki a tashi a tsaya a magance wa jama'a mawuyacin halin da suke ciki.''
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dangane da martanin da gwamnati ke yi kan sukar da ake mata ta zargin rashin daukar matakin magance wahalhalun da jama'a ke fama da su ya ce ai tun farko ma gwamnatin ce ta jefa mutane da wahalhalun da suke ciki.
''Daga cire tallafin mai da wasu matakai da ta rika dauka shi ya jefa 'yan kasa cikin halin da suke ciki, saboda idan aka yi lissafi kafin zuwan gwamnatin APC gaba daya tun daga ta Muhammadu Buhari rayuwar dan Najeriya da walwalarshi da jin dadainshi ba za ka hada shi da yanzu ba,'' a sakataren na PRP.
Ya kara da cewa, ''sannan in ka dauki gwamnatin Bola Tinubu daga lokacin da ya karba daga wajen Muhammadu Buhari sai abin ya kara lalacewa, aka rika shiga kunci.''
A ranar Asabar da ta gabata ne aƙalla mutum 10 suka mutu, ciki har da ƙananan yara, yayin da da dama suka samu raunuku sakamakon wani turmutsutsu da ya faru a cocin Katolika da ke unguwar Maitama a Abuja.
Lamarin ya faru ne a ranar da safe lokacin da mutane suka yi dafifi a harabar cocin domin karɓar kayan tallafi da ta alƙawarta raba wa marassa ƙarfi da tsofaffi.
Haka a can ma jihar Anambra da ke kudu maso gabashin ƙasar rahotonni sun ce wasu mutane sun mutu bayan wani turmutsutsu da aka yi a wajen rabon tallafi a jihar a ranar ta Asabar.
Lamarin na zuwa ne kwanaki bayan wani turmutsutsun ya kashe ƙananan yara da mata 35 a birnin Ibadan na jihar Oyo, sakamakon wani bikin ƙarshen shekara.
Galibi dai dama a ƙarshen shekara masu hannu da shuni da ƙungiyoyi kan yi rabon tallafi musamman na kayan masarufi ga marassa ƙarfi, domin tallafa musu.










