Me nasarar APC a zaɓen Edo ke nufi ga siyasar Najeriya?

Zaɓaɓɓen gwamnan jihar Edo Sanata Monday Okpebholo tare da magoya bayansa.

Asalin hoton, Adekola Olawale/BBC

    • Marubuci, Isiyaku Muhammed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
    • Aiko rahoto daga, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Sakamakon Zaɓen gwamnan jihar Edo a Najeriya na ci gaba da jan hankali, inda Jam’iyyar APC mai mulki a matakin ƙasa ta doke Jam’iyyar PDP mai mulki a matakin jihar.

Hukumar INEC ta sanar da ɗan takarar APC, Sanata Monday Okpebholo a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen wanda aka yi a ranar Asabar da ta gabata.

Baturen zaɓen, Farfesa Farouk Adamu Kuta ya ce Sanata Monday Okpebholo ya samu ƙuri’a 291,667, sannan ɗan takarar Jam’iyyar Asuerinme Ighodalo ya samu ƙuri’a 247, 274 a zaɓen wanda ƴan takara maza 16 da mace ɗaya suka fafata domin kujerar gwamnan jihar.

Sakamakon zaɓen ya nuna Sanata Okpebholo ya lashe ƙananan hukumomin jihar 11 daga cikin 18, shi kuma Mista Ighodalo ya samu ƙananan hukumomi bakwai.

Tuni dai PDP ta yi watsi da sakamakon zaɓen, inda ta yi zargin an tafka maguɗi, sannan ta yi zargin INEC ta karya wasu ƙa'idojin gudanar da zaɓe.

Haka kuma an samu rahotanni da ke nuna cewa an yi amfani da kuɗi wajen sayen ƙuri'a a zaɓen.

Tun kafin zaɓen ne hankali ya koma kan tsofaffin abokan siyasa Gwamna mai ci a jihar, Godwin Obaseki da Sanata Adams Oshiomole, waɗanda yanzu dangantaka ta yi tsami a tsakaninsu.

Yadda Obasaki da Oshiomole suka nuna ƙwanji

Hotunan Obaseki (a hagu) da Oshiomole (a dama)

Asalin hoton, EDO STATE GOVERNMENT HOUSE

Bayan da Oshiomole ya tsaya kai da fata domin tsayar da Obaseki a zangon mulkinsa na farko, bayan ya samu nasara sai suka fara takun-saƙa, inda a zagaye na biyu Oshimole ya fito da wani ɗan takarar daban, amma a ƙarshe Obaseki ya samu nasarar doke shi, ya lashe zaɓensa karo na biyu.

A lokacin Obaseki ya mayar da akalar yaƙin zaɓensa ne a doron kawo ƙarshen siyasar ubangida a jihar.

A wannan zaɓen, Obaseki ya tsaya wa ɗan takarar PDP Asuerinme Ighodalo, shi kuma Oshiomole ya tsaya wa ɗan takarar APC, Monday Okpebholo.

Wani babban abin mamaki shi ne yadda APC ta samu nasara a ƙaramar hukumar da Gwamna Obaseki ta fito da tazara mai yawa.

Gwamna Obaseki ɗan asalin ƙaramar hukumar Oredo ne. APC ta samu ƙuri’a 30,780, ita kuma PDP ta samu ƙuri’a 24,938, sai kuma LP ta samu ƙuri’a 5389 kamar yadda baturen zaɓen ya sanar.

Shi kuma Adams Oshiomole ya samu nasara a ƙaramar hukumarsa ta Etsako ta Yamma, inda shi ma mataimakin Obaseki, Philip Shuaibu ya fito, inda APC ta samu ƙuri’a 32,107, PDP ta samu ƙuri’a 17,483.

Me nasarar APC a Edo ke nufi a siyasar Najeriya?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

BBC ta tuntuɓi Farfesa Tukur Abdulƙadir, massanin kimiyar siyasa da ke Jami'ar Jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya, wanda ya ce sakamakon zai zo da wani abu daban mai yawa ba.

A cewarsa, “Wannan sakamakon zaɓen ba wai za a ce ya zama daban da sauran na zaɓukan baya ba ne illa dai yanayin guguwar siyasar jihar ta canja.”

Ya ce ko a wancan zaɓen da aka yi, inda Obaseki ya samu nasara akwai zargin wasu gwamnoni na APC da ba sa ɗasa wa da Oshiomole sun taimaka wajen ba Obaseki nasara.

A game da yadda APC ta samu nasara a kan PDP, Farfesa Abdulƙadir ya ce bai rasa nasaba da ficewar da wasu jiga-jigan PDP suka yi.

“Idan aka yi la’akari da sakamakon zaɓen, PDP ta samu nasara a tsakiya da kudancin jihar, amma ta yi mummunar rashin nasara a arewaci, inda nan ɓangaren da Oshiomole da Philip Shuaibu suka fito. Ita kuma APC ta samu nasara sosai a yankin, sannan kuma ta daga sauran yankuna.

“Wannan shi ne sauyin da aka samu saboda a baya PDP na samun nasara a dukkan ɓangarorin jihar ne.”

Sai dai a cewar masananin, " batun sa hannun gwamnati daga sama a kan nasarar ta APC, zargi ne, “amma kullum al’amarin zaɓe a ƙasar nan cike yake da ƙalubale.”

“Amma wasu na ganin irin yadda Obaseki ya riƙa gallaza wa waɗanda ba sa tare da shi ya taka rawa a rashin nasarar ta PDP,” in ji Farfesa Abdulƙadir, wanda ya yi misali da rikicin da ke tsakanin Obaseki da mataimakinsa, wanda ya sa ya fice daga jam’iyyar.

A ƙarshe masanin siyasar ya ce ba zai yiwu a yi amfani da sakamakon zaɓen na Edo wajen auna yanayin yadda siyasar 2027 za ta kaya.

“Ana iya samun jam’iyya ta faɗi zaben shugaban ƙasa amma ta samu nasara a jiha,” in ji shi, inda ya ce hakan bai rasa nasaba da irin rawar da gwamnan jihar ya taka.

Wannan ne zaɓe mafi muni – PDP

Gwamnan Adamawa Ahmadu Fintiri

Asalin hoton, FACEBOOK/FINTIRI

Jam'iyyar PDP babbar mai hamayya a Najeriya ta caccaki sakamakon zaɓen.

Da yake jawabi a game da zaɓen, Gwamnan Jihar Adamawa Ahmadu Fintiri ya ce bai taɓa ganin zaɓe mai muni kamar wannan ba, inda suka yi zargin an tafka maguɗi.

Fintiri wanda shi ne shugaban kwamitin zaɓen PDP a Edo ya bayyana hakan ne a zantawarsa da BBC.

Ya ce, “Maimakon a samu cigaba na ga abun ya zama kamar rawar ƴan mata. Daga yadda INEC suke gudanar da harkokinsu kana iya ganewa a taƙaice suna tare da wane, haka ƴansanda da sauransu. Kuma bayan an yi zaɓe abin da jama’a suka zaɓa ba shi ba ne ake sanarwa.”

Da aka tambaye shi ko don sun sha kaye ne yake bayyana hakan, sai ya ce yana magana ne a matsayin ɗan kishin ƙasa mai son cigabanta.

“Damuwata Najeriya ce. Idan babu Najeriya ai babu APC babu PDP kuma babu mu. Idan ba mun gyara dimokuraɗiyyar nan ba, duk maganar da muke ta ƙoƙarin kamo wasu ƙasashen a cigaba ba zai samu ba,” in ji Fintiri, inda ya ƙara da cewa, “Ban taɓa ganin irin wannan zaɓen ba a rayuwata ba.”

Ya ce za su koma su duba sakamakon zaɓen domin ɗaukar matakin zuwa kotu domin a cewarsa, na’urorin da aka kawo domin cigaba da gyara harkokin zaɓen sun zama hoto, “Amma muna kira ga yan najeriya su zauna lafiya.”

Shi ma Gwamnan Edo Godwin Obaseki ya yi kira ga mutanen jihar da su kwantar da hankalinsu, inda ya yi zargin cewa an tafka maguɗi.