Kisan shugaban Hamas ba ya nufin kawo ƙarshen yaƙin Gaza - Netanyahu

Yahya Sinwar

Asalin hoton, YAHYA SINWAR

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya ce mutuwar shugaban Hamas, Yahya Sinwar, a ranar Laraba, ba ta nufin kawo karshen yakin Gaza.

Mutumin wanda aka yi imanin shine ya kitsa harin 7 ga watan Oktoba da ya janyo mutuwar sama da mutum dubu daya da dari biyu a Isra'ila, ya mutu ne sakamakon farmakin da sojojin Isra'ilar suka kai masa a Rafah da ke kudancin yankin.

Mista Netanyahu ya ce mutuwar Sinwar za ta sa haske ya mamaye duhu a gabas ta tsakiya.

Sai dai ya dage cewa Isra'ila za ta ci gaba da fafatawa da dukan karfinta har sai ta ceto yan kasar da Hamas ke rike da su.

Zuwa yanzu dai babu wani martani daga kungiyar ta Hamas game da wannan batu.

A gefe guda rundunar sojojin Isra'ilar ta fitar da wani bidiyo da ke nuna shugaban na Hamas a mintunan ƙarshe kafin ta halaka shi.

Bidiyon wanda wani jirgin sama mara matuki ya nada ya nuna wani mutum zaune da rauni a kan kujera, ya rike itace a tsakiyar wani rushashshen gini, yayin da ya rufe fuskarsa da tutar Falasɗinu.

Kakakin rundunar sojin Isra'ila Daniel Hagari ya ce an kashe karin wasu mutane biyu a yayin farmakin.

Ya ce dakarunsu za su ci gaba da bibiyar sauran shugabannin kungiyar Hamas, kuma matsawar kere na yawo zabo na yawo, wataran za a hadu.

Sai dai yayin da Isra’ilawan ke murnar kisan Yahya Sinwar, iayaln wadan ke tsare a hannun Hamas na ci gaba da bayyana damuwa, kan makomar makusantansu, inda suka yi kira ga hukumomin Isra’ila da su yi amfani da wannan dama don ganin an sami daidaito a sako yan uwan nasu.

Yayin da kisan Sinwar ke zama babbar Asarar ga Hamas, Faldasdinawa a Gaza na cewar dukkan shugabanin kungiyar da aka halaka a baya, maye gurbinsu ake yi don haka ba wani tasiri da hakan zai yi.

Sai dai bayan bullar labarin kisan Yahya Sinwar, Iran ta ce wannan ba zai rage karfin guiwar masu neman yanci a duniya ba, hasalima mutuwar wani tashin wani.

Haka itama Hezbollah da ke Labanon ta ci alwashin ci gaba da kai farmaki kan Isra’ila.

A ranar Laraba ne dai rundunar sojin Isra'ila ta tabbatar da kisan jagoran ƙungiyar Hamas Yahya Sinwar, a wani hari da suka kai kudancin Gaza.

Sojojin na Isra'ila sun ce sun tsananta hare-hare a kudancin Gazan bayan samun cikakkun bayanan sirri da suka ƙunshi bayanan wuraren da manyan shugabannin Hamas ke ɓoye.