Phillips zai fayyace makomarsa nan gaba a Man City

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan Manchester City, Kalvin Phillips ya ce zai fayyace makomarsa nan gaba kadan a kungiyar ta Etihad.
Philips ya kasa samun gurbin buga wasa da yawa a City, tun bayan da ya koma kungiyar daga Leeds United, wanda ya shiga wasa canji karo uku a gasar Firimiyar Ingila ta bana.
Sai dai tawagar Ingila ta saka shi wasan da ta doke Italiya 3-1 a fafatawar shiga Euro 2024, ya ce ya kamata ya samu kungiyar da zai riƙa buga wasa kowanne mako.
''Zan sanar da makomata a kungiyar Manchester City a watan gobe.''
Duk da cewar ba ya buga wasa da yawa tun bayan da ya koma City a Julin 2022 kan fam miliyan 45, kocin tawagar Ingila, Gareth Southgate na saka shi a wasannin da ƙasar ke bugawa.
Ya buga wasan da Ingila ta doke Italiya 3-1 ranar Talata ta samu gurbin shiga gasar kofin nahiyar Turai da za a yi a Jamus a 2024, bayan da saura wasa biyu ya rage.
Tun can baya kociyan Manchester City, Pep Guardiola ya ce Philips ya kara kiba, bayan da ya koma Etihad da aka kammala gasar kofin duniya a 2022.
Wasa biyu kacal aka fara da Philips a bara a Premier League, wanda ya canji 'yan wasa a wasu karawar, kuma wasa 221 ya yi a kakar da City ta lashe Champions League da Premier League da kuma FA Cup a bara.










