An yi sulhu tsakanin Klopp da Salah

Asalin hoton, Reuters
Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce an warware matsalar da ta kunno kai wadda ta kai ga har aka yi cacar baki tsakaninsa da Mohamed Salah.
Salah da Klopp sun tayar da jijiyoyin wuya lokacin da za a saka shi a wasan da suka tashi biyu da biyu da West Ham.
Dan kwallon Masar mai shekara 31, ya ƙi yin magana da ƴan jarida bayan kammala wasan, inda ya ce "Wuta za ta kama idan na yi magana a yau."
Amma a ranar Juma'a, Klopp ya ce "Babu matsala. Komai ya wuce. Ba labari ba ne."
Tuni dai Klopp ya sanar da cewa zai bar kulob ɗin a ƙarshen kakar wasan bana.
Mohammed Salah ne ɗan wasan da ya fi kowanne zura ƙwallo a Liverpool a kakar wasa ta bana, inda ya ci ƙwallo 24 kuma ya taimaka aka ci 12.
Liverpool ce ta uku a kan teburin gasar firemiya.





