Yadda ake azabtar da masu aikin gida a Indiya

Hoton hannu da raunuka

Asalin hoton, Deepika Narayan Bharadwaj

Bayanan hoto, An kai yarinyar mai shekara 14 asibiti da raunuka a jikinta
An wallafa

A makon da ya gabata ne ‘yan sanda da wasu jami’ai suka ceto wata yarinya mai shekara hudu da ke aiki a wani gida, a wata unguwa da ke wajen birnin Delhi, wadda aka ji mata raunuka da azabtar da ita a gidan da take aiki.

Kwararru sun ce irin wadannan ma’aikata da ke wankau suna samun kansu cikin akuba saboda babu kuduri da kuma wasu dokoki na shari’a da ke ba su kariya.

Yarinyar wadda aka kai ta asibiti da raunuka ta gaya wa ‘yan sanda cewa mutanen gidan da take aiki ne suka azabtar da ita tsawon wata biyar.

Yar jarida kuma mai shirya fim Deepika Narayan Bharadwaj wadda ta gano yarinyar ta kuma gaya wa ‘yan sanda ta ce tana cikin wani hali na ban tausayi.

Ta ce wata kawarta ce ta ga yarinyar ta fito zubar da shara daga gidan da take aiki, inda ta ga irin yanayi da halin da take ciki, ta ba ta labarinta.

Lokacin da Ms Bharadwaj ta je wajen yarinyar a asibiti ta ce, yarinyar ta gaya mata irin akubar da take sha a gidan.

‘’Ta gaya min cewa kullum sai an lakada mata duka, ba ma sau daya ko biyu ba kusan ko da yaushe sai na yi mata duka idan ba ta gama aikin da aka sa ta ba,’’ in ji ta.

‘Yan sanda sun kama masu gidan da yarinyar take aiki, Manish Khattar da matarsa Kamaljeet Kaur, kuma sun gurfanar da su a kotu a kan laifuka da dama na muzgunawa.

‘Yan sanda sun ce bisa ga dukkan alamu an rika gana wa yarinyar azaba ne ta hanyar amfani da wani abu mai kaifi kamar wuka ko reza da wani karfe mai zafi.

‘Yan sandan sun gaya wa ‘yan jarida cewa suna zargin masu gidan da azabtar da yarinyar a duk lokacin da ba ta yi aikin da aka ba ta ba yadda ya dace.

Hotunan da BBC ta gani na yarinyar bas u da kyawun gani, za su iya tayar wa mutum hankali, saboda haka ne ba a sa su ba a wannan labari.

A bayanin da ya yi wa ‘yan sanda yarinyar ta ce iyayen gidan nata sukan sa ta cire kayanta a lokacin da take wanke da sauran ayyukan gida, sannan sus a ta kwana a kan dabe ba kaya a jikin nata.

BBC ta yi kokarin ji daga bakin lauyoyi masu kare mutanen gidan da ake zargi amma ba su yi magana ba.

Hoton ma'auratan

Asalin hoton, Deepika Narayan Bharadwaj

Bayanan hoto, Ma'auratan da ake zargi da azabtar da yarinyar na hannun ƴan sanda
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tun bayan da labarin zargin ma’auratan na azabtar da yarinyar ya bayyana kamfanonin da suke aiki suka kore su.

Shugabar wata kungiya mai zaman kanta da ke yaki da cin zarafi da safarar mutane Nishi Kant, kungiyar da ke kula da yarinyar a yanzu ta ce magidan bas a ba yarinyar abinci sosai har ma suna tilasta mata cin abinci daga shara.

Ta ce a yanzu suka kokarin gano kawun yarinyar da ya kawo ta wajen wannan aiki, da kuma sanin inda kudin aikinta yake domin sun fahimci cewa ba a biyanta komai

Labarai yarinyar ya tayar wa da mutane da dama hankali a kasar ta India inda aka yi ta yada shi a kafafen watsa labarai.

Sai dai masu rajin kare hakki sun ce wannan abu ne da yake afruwa sosai a kasar da take da miliyoyin yara maza da mata ‘ya’yan talakawa da ke aiki a gidajen attajirai da masu matsakaicin hali.

A shekara ta 2013, ‘yan sanda a Delhi sun kama wata mata mi shekara 50 saboda cin zarafi da azabtar da wata yarinyar mai shekara 15 da ke aiki a gidanta.

An ga rauni da yawa a kan yarinyar da kuma alamar cizo a jikinta.

Haka a shekara ta 2012 ba, na kama wasu ma’aurata likitoci a kan laifin kulle yarinya ‘yar shekara 13 da ke musu aiki a gida, inda suka tafi hutu Thailand.

Makwabtansu ne da suka ji yarinyar tana kuka tana ihu inda take neman a cece ta suka ankarar da ‘yan sanda.

Dukkanin wadannan yara mata da aka samu an ci zarafinsu a gidajen da suke aiki, sun fito ne daga

Jharkhand, daya daga cikin jihohi mafiya talauci a India.

Hoton kafa

Asalin hoton, Deepika Narayan Bharadwaj

Saboda tsananin talauci ‘yan mata suna daina makaranta da sun kai shekaru na balaga.

Daga nan ne kuma sai kamfanoni na bogi wadanda ba su da rijista ke yaudararsu da cewa za su sama musu aiki a Delhi da sauran birane, inda suke ayyuka a yanayi na muzgunawa, in ji Rishi Kant, mai magana da yawun Shakti Vahini.

Alkaluman hukuma sun nuna cewa Indiya tana da masu aikin gida miliyan 4.75, wadanda suka hada da mata miliyan uku.

Amma kuma kungiyar kwadago ta duniya (ILO) ta yi kiyasin cewa yawansu ya kai tsakanin mutum miliyan 20 zuwa 80.

Dokar Indiya ta ce yaran da suka zżarta shekara 14 ma za su iya aikin gida, saboda ba a daukan aikin gida a matsayin mai hadari.

Wannan dai tsari ne da yake taimaka wa iyalai talakawa wadanda ‘ya’yansu ba su da ilimi ko kuma basu yin isa ba a karatu.

To amma kuma hakan yana bayar da kafar ci da gumin yaran, in ji Meenakshi Gupta Jain, da ke da kungiyar Helper4U, wadda kaf ace ta intanet da ke samar da aiki.

Jami’ar ta ce abin da ke sa ake ci da gumin yaran shi ne abu wani kwantiragi da ake kullawa da yaran a kan aikin kan mislai albashi mafi karanci da za a bas u da kariya daga cin zarafi na lalata da sauransu.

Jami’ar ta ce ana azabtar da yara ne saboda suna aiki a cikin gida inda ba a sana bin da ake yi musu ba.

g

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A India an yi kiyasin akwai masu aiki a gida 4.75

Duk da wannan abu da yake faruwa ba kasafai ake maganar halin da masu aiki a gidaje ke ciki ba a Indiya sai dai idan wani abu ne mai tsanani ya faru kuma ya karade kafafen yada labarai

Ms Jain ta ce dole ne a samar da wani tsari da za a rika aikawa da sako tare da wayar wa da al’ummar India cewa yana da muhimmanci a rika mutunta masu aiki a gidaje.

Shi kuwa Mr Kant cewa ya yi dole ne a hanzart kudurin dokar yaki da safarar mutane domin magance wannan matsala ko kuma takaita ta.

Ya ce dole ne a hari wadanda suke dauko yara ‘yan mata masu rauni suna sa su wuraren da ake ci da guminsu, inda za a rika hukunta irin wadannan mutane.