Super Eagles ta ci Sao Tome 16-0 gida da waje
Tawagar kwallon kafa ta Najeriya ta doke ta Sao Tome 6-0 a wasan neman shiga gasar kofin hahiyar Afirka da suka kara ranar Lahadi a Uyo, jihar Akwa Ibom.
Minti na 13 da fara wasa Super Eagles ta fara cin kwallo ta hannun Victor Osimhen, sannan Ademola Lookman ya ƙara na biyu minti na 14 tsakani.
Kwallo na takwas kenan da Osimhen ya ci a wasannin neman shiga gasar kofin nahiyar Afirka don shiga gasar da Ivory Coast za ta karɓi bakunci a 2024.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne ɗan wasan Nottigham Forest Taiwo Awoniyo ya ƙara na uku a raga.
Najeriya ta ci kwallo na huɗu a bugun fenariti, kuma Osimhen ya zura a raga ta tara da ya ci a wasannin shiga gasar kofin Afirka.
Haka kuma shi ne ya ci na biyar na uku rigis a fafatawar, sannan Samuel Chukwueze ya ci na shida, saura minti huɗu a tashi daga gumurzun.
A wasan farko da Najeriya ta je gidan Sao Tome a karawar rukunin farko, ta yi nasarar cin 10- 0 ne.
Tun kan wasan na ranar Lahadi, Sao Tome ce mai riƙe da tarihin rashin ƙoƙari a wasan neman shiga gasar nahiyar Afirka a baɗii, wadda aka ci kwallo 20 a karawa biyar ta cikin rukuni.
Ta kuma yi wasa 17 kan ta je Najeriya da cin karawa daya a dukkan fafatawa da shan kashi a karawa daya.
Wasan da ta yi nasara a cikin fafatawar 17, shi ne wanda ta ci Liberiya 2-1 cikin watan Maris din 2016 a wasannin shiga gasar kofin Afirka.











