''Na san ana auna kwazo na a Man City da Champions League''

Pep Guardiola

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Pep Guradiola ya ce ya kwan da sanin ana auna kwazonsa a Manchester City ko zai iya daukar Champions League a kungiyar.

City ta dauki manyan kofi tara tun bayan da Guardiola ya karbi aikin horar da kungiyar a 2016.

An tambayi Guardiola ko zamansa a City zai zama koma baya idan ya kasa daukar kofin zakarun Turai a kungiyar?

''Ban yanda da wannan batun ba, ko kadan illa dai ana auna kwazon aikin da nake yi a City da kofin zakarun Turai, in ji kocin mai shekara 52.

''Tun kan na fara aiki a Etihad wasu ke cewar na koma kungiyar, domin daukar Champions League.''

City za ta kai quarter finals, idan ta yi nasara a kan RB Leipzig a wasa na biyu a Champions League da za su kara a Etihad ranar Talata.

Sau daya City ta kai wasan karshe a Champions League karkashin Guardiola, inda Chelsea ta yi nasara 1-0 a 2021.

A bara Real ta hana City kai wa zagayen karshe a gasar zakarun Turai.

Guardiola wanda ya lashe Champions League biyu a Barcelona ya kasa dauka a Bayern Munich daga nan ya koma Manchester City da horar da tamaula.

A cikin watan Nuwamba, Guardiola dan kasar Sifaniya ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da koci a Etihad kaka biyu nan gaba.