Waiwaye: Saukar Daurawa da kisan da sankarau ta yi wa dalibai 20 a Yobe
Wannan makala ce da ke duba muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi
Daurawa ya ajiye shugabancin Hisbah a Kano

A ranar Juma'a da safiya ne fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya yi murabus daga muƙaminsa na shugaban hukumar Hisbah a jihar.
Murabus ɗin malamin na zuwa kwana guda bayan da gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya nuna damuwarsa kan salon da hukumar Hisbah ke bi wajen yaƙi da masu aikata baɗala a Kano.
A wani bidiyo mai tsawon ƙasa da minti uku da Sheikh Daurawa ya wallafa a shafinsa na Facebook, malamin ya bayyana cewa kalaman gwamnan sun kashe masa gwiwa kuma a don haka ya ajiye muƙaminsa na jagora a hukumar ta Hisbah.
Gwamnatin Najeriya ta tsare jami'an Binance

Asalin hoton, ALAMY
A cikin makon da muke bankwana da shi din ne kuma gwamnatin Najeriya ta tabbatar wa BBC cewar tana tsare da wasu manyan jami'an shafin hada-hadar kuɗin kirifto na Binance a birnin Abuja.
Hakan na zuwa ne bayan wasu rahotanni da suka ɓulla a daren ranar Laraba da ke nuna cewa hukumomi na tsare da jami'an.
A wata tattaunawa da BBC, Zakari Mijinyawa, shugaban sashen yaɗa labaru na ofishin mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin tsaro, ya ce "ana yi wa jami'an tambayoyi ne ƙarƙashin binciken da hukumomin tsaro ke yi kan daidata kasuwar musayar kuɗi, wanda ofishin na mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro ke jagoranta".
Cutar sanƙarau ta kashe ɗalibai 20 a Yobe

Asalin hoton, AFP
A farkon makon ne kuma dalibai 20 suka mutu sakamakon ɓarkewar cutar sanƙarau a makarantun sakandaren mata guda uku da kwalejin ‘yan mata ta gwamnatin tarayya da ke kananan hukumomin Potiskum da Fika a jihar Yobe.
Kwamishinan Ilimin primary da Sakandare na Jihar, Mohammed Sani-Idris ne ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin, inda ya ce 17 daga cikin ɗaliban da suka mutum ƴan makarantar sakandiren kwana ne, yayin da ragowar ukun ƴan furamare ne.
Kwamishinan ya kuma ce an kwantar da ɗalibai da dama a asibiti amma an sallame su.
Tinubu ya ce a yi aiki da rahoton Oronsaye

Asalin hoton, Tinubu/X
Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin aiwatar da cikakken rahoton Oronsaye wanda tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kafa tun a 2011, a kokarin gwamnati na rage yawan kashe kudaden gudanarwa.
An dai kafa kwamitin ne a lokacin sake fasalin tsarin mulki da kwamitoci da hukumomin gwamnatin tarayya karkashin shugabancin tsohon shugaban ma'aikata na Najeriya, Stephen Osagiede Oronsaye.
Kwamitin ya gabatar da rahoton a ranar 16 ga Afrilu, 2012, inda ya bankado yadda ake gudanar da gasa a tsakanin hukumomi da dama, wanda ba wai kawai ya haifar da rashin kwanciyar hankali tsakanin hukumomin gwamnati ba, har ma ya haifar da almubazzaranci.
NLC ta gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya

Ɗaruruwan mambobin kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC ce suka gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa a Abuja, babban birnin Najeriya da ma sauran manyan biranen kasar.
Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta NLC, kwamared Joe Ajeoro ne ya jagoranci zanga-zangar, inda suka je harabar majalisar dokokin kasar don kai kokensu.
Tun da farko jami'an tsaro da suka haɗa da ƴan sanda da na Civil Defense sun yi ƙoƙarin hana su shiga harabar majalisar, amma ba su yi nasarar hakan ba.










