Muhawarar da ƴan Najeriya ke tafkawa kan jawabin Tinubu

Asalin hoton, Getty Images
Ƴan Najeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan hirar da Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi da ƴan jarida a ranar Litinin a jihar Legas.
Wannan ita ce hira ta farko da shugaba Tinubu ya yi da ƴan jarida tun bayan hawansa mulki a watan Mayun 2023.
Shugaba Tinubu ya taɓo batutuwa da dama da suka jan hankulan ƴan ƙasar kamar janye tallafin man fetir da yayi tun ranar da aka rantsar da shi, da kuma batun haraji da ke neman raba kan ƴan ƙasar, da halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki, da kuma matsalar tsaro da dai sauransu.
Sai dai wasu jawaban nasa, da alamu ba su gamsar da mafiya yawan ƴan ƙasar ba, inda da dama daga cikinsu da kuma wasu masana ke sharhi kan jawabin.
Ga abin da wasu ma'abota shafin X, wanda a baya aka fi sani da Twitter ke cewa;
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Theo Abu Agada ya ce '' shugaba Bola Tinubu ya ce '' ba za a iya ƙawar da cin hanci ba''. Wannan abun kunya ne ya fito daga bakin shugaban ƙasa. Waɗannan kalaman za su ƙara ƙarfafawa ma'aikatan gwamnati satar ƙudi.''
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Shi ko wani mai suna Delong a X, cewa yake yi '' Na saurari hirar Shugaba Bola Tinubu jiya. Ba shi da wani shiri mai kyau ga ƴan Najeriya kuma ba shi da maslaha ga wahalhalun da ƴan ƙasar ke ciki.''
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3
Kawu Garba kuwa cewa yayi '' Shugaba Bola Tinubu ya nuna ƙwarewa da sanin makamar aiki a tattaunawarsa jiya. Ba shakka a shirye yake ya ɗora Najeriya kan tafarkin ci gaba''
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 4
Shi kuma wani mai suna Ibraheem Abdulateef ya ce, '' abu ɗaya da na tabbatar da shi a hirar Shugaba Tinubu shi ne Tinubu ba shugaba ba ne da bai san abin da ke faruwa ba, kuma shi yake jan ragamar gwamnatinsa.''
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 5
Tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya sanata Shehu Sani, a shafinsa na X, ya ce, '' abin da ya fi birgewa a cikin hirar ta shugaban ƙasa shi ne bayyana shirinsa na tattaunawa domin samun maslaha game da abubuwan da suka ja hankali a cikin ƙudurorin haraji. Ikirarinsa na samar da tsaro a mafi yawan yankunan arewa gaskiya ne, sai dai rashin amincewarsa da binciken yadda aka kashe ƙudaden ɓangaren tsaro a gwamnatin baya tamkar taimakawa sata ne.
Yadda masana ke kallon jawabin Tinubu
Farfesa Abubakar Kari, masanin kimiyyar siyasa kuma malami a jami'ar Abuja ya ce a cikin hirar, babu abin da shugaba Tinubu ya yi a cikinsa "sai wasa kansa da kuma kawo hujja kan wasu matakansa da suka janyo cece-kuce da kuma ake ganin sun jefa al'umma cikin uƙuba, maimakon a tunaninsa zai yi amfani da kalaman lalama."
Farfesa Abubakar ya kuma ce tun hawansa mulki, duk tunanin da ake yi cewa "shugaba Tinubu zai faɗi abubuwan da ƴan ƙasar za su ji dadi zuwa yanzu ba a samu ba, inda ya ce sannu a hankali mutane za su daina sauraron sa ko kuma tunanin wani abun kirki zai fito daga cikin jawabinsa.
A fili yake irin matakan da ya ɗauka sun yi tsauri, ƴan Najeriya na ta mutuwa ta fannoni da dama wanda ya kamata a ce wannan ya sa ya sake duba menene alfanu ko muhimmancin matakan da yake ɗauka maimakon ya fito fili yana jaddada cewa sai ya cigaba da aiwatar da su.'' In ji Farfesa kari.