Najeriya za ta ranto dala miliyan 600 don sayo jiragen yaƙin soja

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Najeriya ta amince da karbo rancen sama da dala miliyan 600 domin sayen wasu jiragen yaki samfurin Italiya M-346.
Gwamnatin na fatan samun jiragen ga rundunar sojin sama domin kai hare-hare a farkon shekarar 2025.
Najeriya dai ta kara yawan kudaden da take kashe a fannin soji yayin da take yaki da 'yan bindiga tsawon shekaru musamman a arewacin kasar.
Group Kaftin Saddiq Shehu wani masanin tsaro a Najeriya, ya ce duk da wannan yunƙuri na gwamnati na siyen wadannan jirage, har yanzu sojojin ƙasar na buƙatar ƙarin kayan aiki.
Haka kuma masanin ya ce, babbar mastalar da kayan aikin sojin ƙasar ke fuskanta ita ce matsalar rashin iya gyara su, mussaman jirgin saman, wanda idan ya samu wata matsala ba a iya gyara su a nan, wanda haka ke tilasta wa gwamnati siyo wani sabo, maimakon a gyara wanda ake da su.
‘Duk da maganar da ake yi sojojinmu basu da isasun kayan aiki, wasu kayan aikin sun tsufa wasu kuma gyaransu ne mastalar, wanda ka ga mu ba mu yi nisa ba a fannin gyaransu, wanda daga ƙarshe dole a je a siyo sabo, in ji Group Kaftin Saddiq.
Haka kuma ya ce siyo jirgin zai bayar da gudunmawa wajen magance ayyukan Boko Haram da Yan fashin daji.
A cewarsa “Wannan jirgi, ana iya amfani da shi wajen harbo abu daga sama zuwa ƙasa, sannan za a iya amfani da shi wajen bayar da horo ga wadan da za su tuƙa jirgin’ inji shi.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
An dai fara batun siyen waɗannan jiragen yaƙi ne lokacin mulkin gwamantin da ta gabata ta Muhammad Buhari, kwastam sai kuma aka ji gwamantin Bola Ahmed Tinubu ta sanar da amincewa da ciyo bashin kudi don siyo wadannan jirage.
Group Kaftin Saddiq Shehu ya ce ‘shi siyen makami ba abu ne na yanzu-yanzu ba, sai an bi wasu matakai sannan a tsayar da magana.
Haka kuma ya yi jan hakalin cewar kayan aikin soja na da matuƙar tsada, wanda kasafin kudin shekara shekara ake gabatar da su, yawancin kasafin na shekara ba zai yiwu sojoji su iya siyo kayan aikin da suke buƙata da shi ba.
Sai dai Kaftin Saddiq Shehu ɗin ya ce, rashin bincike na daga cikin abubuwan da ke sanyawa a wasu lokuta siyen irin waɗannan jirage masu tsada kan zame mata ƙadangaren bakin tulu, saboda rashin kyakyawan bincike, da ke sanyawa siyen jiragen zame wa Najeriya alaƙakai.
“Kaga akwai wasu jirage da shugaba Buhari ya bayar aka siyo daga Pakistan F17 guda 24 amma a yanzu babu ko da guda ɗaya da ya ke aiki, wanda kaga kenan akwai kanshin gaskiya kan siyensu kan zama alaƙaƙai” a cewar Group Kaftin Saddiq Shehu.









