Sarautun ƙasar Hausa da ake dandaƙe namiji kafin a naɗa shi

Wasu ƴan lifida haye akan doki

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Khalifa Shehu Dokaji
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Sarauta a ƙasar Hausa abu ne mai matuƙar muhimmanci, saboda tasirin da take da shi wajen tafiyar da lamurran al'umma.

Tun asali, Hausawa sun kasance suna da tsari na shugabanci ta hanyar sarauta, inda akan wakilta shugabannin da kan jagoranci kowane fanni na al'umma.

Sai dai baya ga sarautu da ake bayarwa da suka shafi wakilci ko mulkin yankunan ƙasa, akwai kuma wasu da ake bayarwa a cikin fada, waɗanda suka shafi tafiyar da lamurran cikin gida.

A mafi yawan lokuta akan bayar da irin waɗannan sarautu ne ga bayi, waɗanda asalin ayyukansu, su ne hidimta wa sarki, iyalansa da kuma sauran mazauna fada.

Sai dai wani abin mamaki ga irin waɗannan sarautu na cikin fada shi ne ba kowa ne ake naɗawa a kowace sarauta ba, har sai idan yana da wasu siffofi ko ɗabi'u.

Akan yi hakan ne kasancewar masu riƙe da wannan sarauta za su riƙa shiga tsakanin matan sarki ko sa-ɗaka na sarki, domin hana su sha'awa ko kuma neman mata a cikin fada.

Shi ya sa akan samu wasu sarautun waɗanda duk da cewa maza ake naɗawa, to amma dole ne sai sun kasance ba za su iya taɓuka wani abu ba ta fannin saduwa da iyali.

Wannan na nufin komai lafiya ko ƙoshin namiji, ba za a naɗa shi wannan muƙami ba sai an dandaƙe shi ta yadda ba zai yi sha'awar mace ba.

A ƙasar Kano, ɗaya daga cikin masarautu mafi ƙarfi a ƙasar Hausa, an fara amfani da irin wannan tsari ne a ƙarni na15 zamanin sarkin Kano Mohamamd Rumfa, bayan da ya kulle kuyangi (Sa-ɗaka) kusan 1,000, a matsayin ƙwarƙwarori baya ga matansa na aure.

Akan yi wa mazan da ake dandaƙewa domin naɗawa sarauta da 'Babann'i, saboda raunin da suke shi. Sai dai tuni aka daina bayar da irin waɗannan sarautu da ke buƙatar dandaƙe maza.

Dr. Nasir Wada Khalil, masanin tarihi kuma mai bincike a jihar Kano da ke Najeriya ya ce 'duk da babu wani cikakken bayani kan tsarin dandaƙe bayi maza a ƙasar Hauasa, amma a mafi yawan lokaci ana yin hakan ne kan bayin da aka sayo ko kuma aka ciyo su a lokacin yaƙi'.

Haka kuma ya ce akwai wasu daga cikin bayin da aka yi wa hakan da suka taso a gidan sarkin na Kano, waɗanda a sanadiyyar haka suka koma sanya kayan mata.

Mece ce dandaƙa ko fiɗiya?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Dr Bashir Yunusa, ƙwararen likitan mafitsara a asibitin Koyarwa na Mallam Aminu da ke Kano kuma farfesa a ɓagaren tiyata a jami'ar Bayero Kano, ya ce dandaƙa shi ne cirewa ko zare ƴaƴan marainan namiji, ko yi musu wani abu ya zamana sun daina amfani, kenan an kashe sha'awar da namiji ke samu da kashi 95%.

Ƙwararren likitan mafitsara ya ce a likitance akan yi wa mutum dandaƙa ne sanadiyyar cutar kansar ƙasan mafitsara, kasancewar kansar na cin abincinta ne daga ƴaƴan maraina, wadda idan ta yaɗu da yawa kuma ta wuce yadda za a cire ta.

Rukunin na biyu da ake yi wa fiɗiya su ne waɗanda ake iya cire musu maraina amma za su iya kusantar iyalinsu, sai dai ba za su iya haihuwa ba.

Har ila yau Dr Yunusa ya ƙara da cewar 'ana iya fidiye mutumin da ba ya son haihuwa, sai dai shi zai fitar da maniyi a lokacin saduwa, inda ba'a cire wa mutum maraina baki ɗaya sai dai babu ƙwan haihuwa.

Ga jerin wasu saratu a ƙasar Hausa da ba a naɗa mutum sai wanda aka fiɗiye ko kuma mata-maza (babanni), da kuma dalilin hakan:

Turaki/ Turakin Soro

Wasu daga cikin manyan bayi a wata fada

Asalin hoton, Getty Images

Sarautar Turaki na cikin sarautu a masarautu irin su Kano, da ke cikin jerin waɗanda ake dandaƙe mutum kafin a nada shi, ko kuma dole sai masu halittar mata-maza, ko wadanda suka rasa mazantakarsu, wanda dukkansu ake yi wa laƙabi da "Babanni".

A cewar Dr. Nasir Wada Khalil, 'sarautar Turaki ta samo asali ne daga 'Turaka' kuma ita sarautar babanni ce. Masu rike da irin wannan sarauta su ne ke kaiwa da komowa a tsakanin iyalan sarki, da turakar sarki', in ji shi.

Wasu daga cikin ayyukan Turakin sun haɗa da ɗauko dukkan kayan da suke ɗakin sarki da za a yi amfani da su lokacin rangadi ko wata tafiya. wanda kuma suka haɗa da:

  • Wuƙar yanka
  • Takobi
  • Mafici
  • Kyankyndi
  • Bargon Gabas ko Darduma
  • Mashinfidin karaga da zaa shinfiɗa idan sarki ya tafi rangadi ko wata ziyara. Da makamantansu.

Sai dai masanin tarihin ya ce a yanzu sauratar ta Turaki ta fita daga hannun bayi, ta koma ta ƴaƴan Fulani (ƴaƴan sarki), bayan da Fulani suka hau mullki.

Sallama

Wasu daga cikin ƴan bidiga  yayin wani bikin darba

Asalin hoton, Getty Images

Sallama shi ma na cikin manyan bayi a masrautar Kano kuma an fara naɗa sarautar ne a zamanin Fulani, wato Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi.

Tun asali dai ana yi wa sarautar laƙabi ne da Turakin Soro, kuma bayi ne da ake dandaƙewa ko fiɗiyewa ake bai wa sarautar. Saboda sarauta ce da ke sadar da sarki da cikin gida, wadda ta ƙunshi isar da saƙo tsakanin sarki zuwa ga matansa.

Sai dai a cewar Ibrahim Hussaini da yake yanzu babu irin waɗannan bayi da aka fiɗiye, masu lafiya ne ke riƙe da sarautar.

Inda shi ma Dr. Nasir Wada Khalil, wani mai cike mai zaman kansa, ya ce suna daga cikin bayi na amana, da suke babbanni, su ne ke gabatar da duk wani baƙo da ya zo ganin sarki.

Haka kuma ya ce wasu daga cikin ayyukansa sun haɗa da sanar wa sarki waɗanda suke son ganin shi, waɗanda ba hakimai ba.

Sannan da yawa daga cikin sauran sarautu na fidiyayyun bayin da ake da su a baya sun koma ƙarƙashinsa, wanda shi ke kula da su da ayyukansu, sai dai an raba ayyukan nasu zuwa wasu daga cikin masarautu.

Wasu daga cikin hakiman nasa sun haɗa da:

  • Galadiman Sallama
  • Chiroman Sallama
  • Barden Sallama
  • Garkuwan Sallama
  • Sarkin Fadar Sallama
  • Sarkin Takubba
  • Mabuɗi
  • Mai Tafari
  • Turakin Soro
  • Sarkin gidan Sallama

Sai dai Nasir Wada Khalil ɗin ya ce akwai wasu masarautu a ƙasar hausa da su kuma manyan ƙasa ko manyan mutane ake bai wa sarautar ta Sallama, musamman masarautu Irin su Katsina.

Ko akwai sauran waɗanda ake dandaƙewa a masarautar Kano?

Wasu daga cikin bayi haye akan doki

Asalin hoton, Getty Images

Masanin tarihin Dr. Nasir Wada Khalil, ya ce babu sauran wani bawa da ake dandaƙewa a halin yanzu, ko kuma mata-maza da ke riƙe da wata sarauta yanzu a masarautar Kano.

Haka kuma ya ce 'sallama na ƙarshe da aka yi wanda yake cikin fiɗiyayyu ko babanni shi ne Sallama Abun Faɗa kuma sunansa na gaskiya shi ne Nuhu, wanda ya mutu a shekarar 1973, wanda tun daga wancan lokaci ba a sake bayar da ita ga wani wanda yake fidiƴaye ko mata-maza ba.

Haka nan Khalil ya ce an dai samu bayi Babannin da suka riƙe sarautar har kusan cikin shekarar 1990, wanda tun daga nan ba a sake naɗa wani fiɗiyayyen bawa ba a masarautar ta Kano.

Sauran sarautu da suma suke na rukunin waɗannan bayi na amana sun haɗa da:

  • Kasheka
  • San turaki sai sauran saratun da suke ƙarshin Sallaman na Kano

Sai dai masanin tarihin ya ce a yanzu dukkan sarautun da suke a ƙarƙashin Sallaman a yanzu babu wani wanda yake fidiyayye ko mata-maza, masu haihuwa ne da ke da iyalansu yanzu.

Haka kuma har yanzu ana damawa da su a cikin harkokin sarauta, illa kawai sarautar Kasheka da ita ce kadai har yanzu babu wanda aka naɗa tun bayan mutuwar wanda ke riƙe da ita.