An fara yunƙurin kare harshen mutanen Bajju na Najeriya a Turai

Asalin hoton, UGC
An ƙaddamar da wata ƙungiya wadda manufarta ita ce kare al'adu da harshen mutanen Bajju da ke zama a Birtaniya da kuma ƙasashen Turai.
Ƙaddamarwar wadda ta faru cikin ƙarshen mako a birnin Landan na Birtaniya ta samu halarcin ƴan ƙabilar wadanda suke zaune a ƙasar ta Birtaniya da kuma wasu daga Najeriya.
Al'ummar Bajju na cikin ƙabilun da ke zaune a kudancin Kaduna da kuma wasu jihohi na arewa ta tsakiyar Najeriya, kuma harshen na fuskantar barazana daga manyan harsuna kamar Hausa da turancin Ingilishi.
Ƙungiyar ta ce ɗaya daga cikin manufofin kafa ta ita ce tabbatar da cewa matasan ƙabilar da ake haifa a ƙasashen Turai sun riƙe al'ada da harshen na Bajju.
Ƙabilu ƴan Afirka da dama na fuskantar ƙalubalen tabbatar da cewa matasan da ake haifa kuma suke tasowa a ƙasashen Turai sun riƙe al'adu da harsunansu na asali.



























