Fulham tana son Chukwueze, Man Utd da Liverpool na gogayya kan Semenyo

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City na kan gaba a zawarcin ɗanwasan Nottingham Forest mai shekara 25 Morgan Gibbs-White. (Times - subscription required)
Ita kuwa Manchester United tana jagorantar masu zawarcin ɗanwasan Bournemouth mai shekara 25 Antoine Semenyo wanda ɗanwasan gaba ne na Ghana sai dai tana fuskantar gogayya daga kungiyoyin Premier da dama har da Liverpool da Tottenham Hotspur. (Sky Sports)
Manchester United za ta zafafa neman ɗauko ɗanwasan Southampton mai shekara 19 Tyler Dibling idan idan har ta samu tikitin shiga gasar cin kofin zakarun Turai ta hanyar lashe kofin Europa na bana. (ESPN)
Chelsea ta nuna sha'awarta kan ɗanwasan Sporting Viktor Gyokeres mai shekara 26 amma ɗanwasan ɗan asalin Sweden ya fi son ya koma Arsenal. (A Bola - in Portuguese)
Liverpool na bibiyar halin da ɗanwasan Ingila mai shekara 29 Ollie Watkins yake ciki a Aston Villa yayin da suke shirin ɗaukan ɗanwasan Newcastle da Sweden Alexander Isak mai shekara 25. (Football Insider)
Juventus da Inter Milan da Napoli na zawarcin ɗanwasan Manchester United Rasmus Hojlund mai shekara 22 a bazara. (Caughtoffside)
Fulham na nan kan bakanta na ɗauko ɗanwasan AC Milan kuma ɗan Najeriya Samuel Chukwueze mai shekara 25 a wannan bazarar bayan da ta gaza ɗauko shi a watan Janairu.
Chelsea da Newcastle sun tuntuɓi ɗanwasan Bayern Munich mai shekara 28 Kim Min-Jae. (Footmercato - in French)
Everton ta sanya ɗanwasan Monaco da Denmark Mika Biereth mai shekara 22 cikin jerin ƴanwasan da take zawarcinsu a bazara. (Teamtalk)
Tauraruwar ɗanwasan tsakiya na Newcastle Lewis Miley mai shekara 18 na haskawa a wajen ƙungiyoyi da dama na Premier da Bundesliga. (Fabrizio Romano)
Tsohon kocin Liverpool Jurgen Klopp ba shi da burin riƙe wani muƙami a kaka mai zuwa inda ɗan asalin Jamus ɗin mai shekara 57 yake a shirye ya yi fatali da duk wani tayi daga Real Madrid ko Brazil. (Sky Germany - in German)
Ana sa ran Scott Munn zai bar Tottenham bayan shafe shekaru biyu a matsayin babban jami'in ƙwallo na kulob ɗin inda aka ɗora wa ɗan asalin Australiya ɗin mai shekara 51 alhakin matsalolin da ƙungiyar ta fuskanta a wannan kakar. (Mail)














