An kusa kai Arewa bango - ACF

Barayin daji

Asalin hoton, OTHERS

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

ACF ta bayyana hakan ne a yayin taron kwamitinta na koli na 78 da ta yi a ranar Alhamis , 21 ga watan nan na Agusta, 2025 a birnin Kaduna.

Shugaban kungiyar Mamman Osuman shi ne ya fadi hakan inda ya yi gargadin yana mai cewa yanzu ba lokaci ba ne da yankin zai zauna ya kame bakinsa ya yi shiru yana ganin irin yadda al.'amura ke ta tabarbarewa a yankin.

Ya yi kira ga shugabannin Arewa da 'yan yankin da su tashi tsaye su hada kai ganin yadda harkar tsaro ke kara lalacewa da yadda ake ci da gumin yankin da da kuma yadda matsalar muhalli ke kara zama barazana ga yankin gana daya.

Kungiyar ta ce yanzu ba lokaci ba ne da za ta zauna ta zura ido ko ta kawar da kanta da cewa komai yana tafiya daidai a kasar ba.

Osuman ya nuna takaicinsa kan irin rayukan da ake ci gaba da kashewa a kullum a arewacin Najerriyar.

"Mun rasa yara matasa maza da mata da tsofaffi a sanadiyyar bala'o'i da ambaliya da ayukan miyagu bata-gari da 'yan ta'adda. Halin da muke ciki a yankin babban abin damuwa ne a garemu, wanda a don haka nake kira a garemu mu yi nazari tare da addu'a," ya ce.

A tattaunawarsa da BBC mai bayar da shawara ga kungiyar ta ACF, Bashir Hayatu Gentile, ya ce, a lokacin taron kungiyar ta yi nazari tare da tsokaci kan wadannan abubuwa da suka damu kungiyar na matsalolin da ke addabar yankin.

Ya ce, ''Abubuwa ne sahihai suke ganin yanzu su ne matsalolin 'yan arewa wadanda ake son lalle-lalle a yi kama-kama kuma a yi wa gwamnati tsinke aka lalle ta yi wanui abu na magance wadannan matsaloli.

''Ba abin da ya fi damun Arewa yanzu kamar matsalar tsaro da yadda ake sace-sace da kashe-kashen mutane a kan hakan ne kungiyar ta fitar da matsaya ta ganin lalle yankin ya tashi tsaye ya hada kai tare da ganin matsa wa gwamnati a kan ta kara akimi wajen ganin ta magance wa Arewa wadannan katutun matsaloli,'' a cewarsa.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Gentile ya ce a jawabin da shugaban kungiyar ya gabatar a wajen taron na Kaduna, ya ce, '' A jawabin da ya fitar ya yi kira ga gwamnatin tarayya cewa, lalle-lalle hakurin Arewa ya kusa karewa gwamnati ta sake wasu dabaru don ganin cewa an dakile wannan abin da ke damin Arewa.''

Mai bayar da shawarar ya ce kungiyar ta ACF ta damu ne ganin irin rahoton da kungiyar Amnesty International ta fitar wanda ya nuna cewa : ''A cikin mulkin shekara biyu da Shugaba Tinubu an kashe mutum 10217 kuma dukkaninsu a arewacin Najeriya ne, wannan shi ne ya sa kungiyar ta ACF ta damu.''

Ya ce wannan bayan dimbin mutanen da aka sace ake kuma ci gaba da sacewa da kashewa da tashin garuruwa kusan a kulluma a arewacin Najeriyar.

''Wannan abin da ya fi damu na kwana-kwana nan a karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina, wanda aka shiga masallaci aka samu mutane suna salla da asuba aka kashe su aka kona su. A rahoto da aka fitar shi ne cewa mutum 27 aka kashe amma a labarin damuke samu ma ya fi haka.

Tun da kungiyar Amnesty suka fitar da wannan rahoto babu wani daga cikin gwamnati da ya fito ya karyata wannan rahoto shi ne ya sa ACF take ganin to lalle ya kamata a sauya tsari.