Emenalo ya nuna shakku kan salah, David de Gea na son komawa wasan Firimiya

An wallafa

Paris St-Germain na sha’awar dan wasan tsakiya na Manchester United da Brazil Casemiro mai shekara 31 wanda kungiyar Al-Hilal ta Saudiyya ta ke zawarcinsa. (Sports Zone, via Sun)

Manchester United na kokarin neman kungiyar da ta sayi dan wasan gaban Ingila Jadon Sancho mai shekara 23, inda rahotani sun ce albashinsa na fam 350,000 a kowane mako,na cikin dalilan da suka sa kungiyoyin ke dari -darin cimma matsaya daukarsa kan fam miliyan 73 . (Sun)

Babban direktan wasan firimiyar Saudiyya Michael Emenalo ya yi ammanar cewa abu ne mai wuya a shawo kan dan wasan gaban Liverpool da kuma Masar Mohamed Salah mai shekara 31 ya koma taka leda a firimiya a watan Janairu. (Sky Sports)

Tsohon mai tsaron ragar Manchester United dan kasar Sifaniya David de Gea, mai shekara 33, ya sake haifar da jita jita game da komawarsa wasan firimiyar bayan sakon da ya wallafa shafukan sada zumunta (Mirror)

Villarreal na son dan wasan bayan Arsenal dan kasar Portugal mai shekara 32 Cedric Soares (ESPN)

Kocin Tottenham Ange Postecoglou na neman dan wasan da zai saka a tsakiyar baya a kakar mussyar 'yan wasa a Janairu. (Standard)

Komawar Tosin Adarabioyo fagen atisaye bayan ya murmure daga raunin da ya samu ya sa dan wasan Fulham da Ingila mai shekara 26 na jan hankalin kungiyoyi gabanin kasuwar cefanar da ‘yan wasa a watan Janairu. (Mail)

Arsenal da Tottenham dukkaninsu sun tura wakilai domin kallon dan wasan tsakiya Belguim Arthur Vermeeren mai shekara 18 da ke taka leda a Royal Antwerp wadanda suka sami galaba a kan Barcelona a gasar zakarun Turai.(90 Min)

RB Leipzig ta sake tuntubar Liverpool domin ta na son dan wasan gefe dan kasar Portuguese Fabio Carva mai shekara 21 ya ci gaba da taka mata leda , duk da cewa Liverpool na son ya dawo bayan wa’adin da ta bada shi aro ya zo karshe. (Fabrizio Romano)

Kocin Barcelona Xavi, mai shekara 43, na fuskantar matsin lamba a Nou Camp bayan shan kaye sau biyu a jere inda ba bu wani a cikin mambobin kwamitin gudanarwa na kungiyar da ya mara masa baya (AS - in Spanish)

Dan wasan tsakiya Ecuador mai shekara 16 Kendry Paez zai yi atisaye da Chelsea a makon gobe. Kungiyar ta dauko shi ne daga Independiente del Valle a bazara bayan da suka cimma matsaya a kan cewa zai fara taka leda a kulob din bayan ya cika shekara 18 da haihuwa. (Telegraph - subscription required)