Rebecca za ta zama mace ta farko da za ta yi alƙalancin wasa a Premier

An wallafa

Rebecca Welch za ta zama mace ta farko da za ta busa gasar Premier, inda za ta yi alƙalancin wasan Fulham da Burnley da za a yi ranar 23 ga watan Disamba.

Welch mai shekara 40, ta fara harkokin busa ne a shekarar 2010, a watan Janairun wannan shekarar ta zama mace ta farko da ta busa gasar Championship ta maza.

Sam Allison shi ma zai busa wasa a watan Disambar nan, in da zai zama alƙalin wasa baƙar fata na farko da zai yi hakan cikin shekara 15.

Shi ne zai busa wasa tsakanin Sheffield United da Luton a ranar 26 ga watan Disamba.

Uriah Rennie – shi ne alƙalin wasa baƙar fata na ƙarshe da ya busa gasar – kuma ya yi ritaya ne a 2009. Sai Jarnail Singh wanda yake daga Asia ya yi ritaya a 2010.

“Wannan wani gagarimin lokaci ne ga Rebecca da Sam alƙalai biyu da suka nuna inganci da ƙwarewa”, kamar yadda alƙalin wasa Howard Webb ya shaida wa BBC.

“Sun cancanci wannan damar da aka ba su.”

A watan Yuli, FA ta ayyana shirinta na ɗaukar ƙarin alƙalan wasa da kaso 50 daga cikin “mutanen da a tarihi ba a fiye ba su dama ba nan da 2026,” ana son a ɗauki mata alƙalan wasa 1,000 da maza baƙaƙen fata da ‘yan Asiya 1,000 a dukkan matakai.