Kungiyoyi sun kashe fan miliyan 702 kan musayar 'yan wasa

An wallafa

Ƙungiyoyin Ingila sun kashe kashi ɗaya cikin uku na kuɗaɗen musayar 'yan wasa da aka bai wa eja-eja ɗinsu a duniya a musayar da aka yi ta 2023, in ji Fifa.

Alƙaluman sun nuna an samu ƙaruwa da kashi 43 na kuɗin da aka kashe dala miliyan 623 idan aka kwatanta da 493 da aka kashe 2022 kuma ya zarce na 2019 da aka kashe dala miliyan 655.

Kungiyoyin Premeir su ne suka fi yawan kashe kudi a wannan shekarar inda suka kashe dala miliyan 280.

A karon farko an kashe sama da dala miliyan ɗaya kan eja-ejan ƙwallon ƙafar mata.

Eja-ejan 'yan ƙwallon ƙafa na duniya sun kai 3,353 a wannan shekarar in ji wani rahoto.

Rahoton bai sanya sayayyar da aka yi ta cikin gida ba irin ta su Declan Rice da ya koma Arsenal daga West Ham kan fam miliyan 100 sai kuma Moises Caicedo daga Brigton zuwa Chelsea shi ma kan fam miliyan 100.

Harry Kane ya koma Bayern Munich daga Tottenham kan fam miliyan 86 sai kuma Jude Belligham da ya koma Real Madrid daga Dortmund a fam miliyan 89.

Rahoton ya nuna ƙungiyoyin nahiyar Turai ne suka kashe kashi 87 kan eja-eja a 2023.

Ƙungiyoyin gasar Saudiyya sun kashe dala miliyan 86 kan eja-ejan irin na su Ƙarim Benzema da Sadio Mane da Riyad Mahrez da sauran 'yan wasan da suka koma can.

Ƙungiyoyin mata sun kashe kimanin dala miliyan 1.4 kan musaya 125 da aka yi a 2023.