Zanga-zangar ƙarancin man fetur a ƙasashe 90

Asalin hoton, Getty Images
Tashin farashin kayan masarufi na tursasa wa mutane yin zanga-zanga a faɗin duniya. BBC ta tattara bayanai kan duk irin waɗannan zanga-zanga ta farashin man fetur da aka gudanar tun daga watan Janairun 2021, inda ta gano cewa zanga-zangar na daɗa ƙaruwa.
Farashin man fetur na shafar ɓangarori da dama na rayuwa - kamar ziyarce-ziyarce, da safarar ababen kayan masarufi, da samar da makamashi.
A ƙasashe da dama na duniya mutane na kiraye-kirayen a samu sauyi. Suna buƙatar a samar da man fetur isasshe ga al'umma kuma cikin farashi mai sauƙi.
A wasu wuraren an gudanar da zanga-zanga cikin lumana, yayin da a wasu wuraren kuma aka far ma kadarorin gwamnati.
A wasu wuraren har an samu asarar rayuka.
Gwagwarmaya kan man fetur
Khadijah Bah, mai shekara 16 tana tsaye inuwar ƙofar gidansu a lokacin da aka harbe ta da bindiga.
Khadija dai ta kwashe kwanaki tana ganin zanga-zangar da ake yi a kusa da gidansu na ƙara girma, a gabashin Freetown, babban birnin ƙasar Saliyo.
Amma a ranar 10 ga watan Agusta sai zanga-zangar ta ƙazance. Inda jami'an tsaro suka fara artabu da masu zanga-zanga, a nan ne harsashi ya samu Khadija. Nan take ta faɗi ƙasa, ta mutu.
Har yanzu mahaifiyar Maria Sesay na cikin kaɗuwa game da rasuwar ɗiyarta. Kahdija, wadda ɗalibar makarantar sakandare ce, babban burinta shi ne ta zamo ma'akaciyar jinya.

"Ina cikin baƙin ciki", in ji mahaifiyar Khadija. "Na yi ta faɗi-tashi wajen kula da yarinyata. To amma yanzu ta rasu. Ina cikin mummunan raɗaɗi."
A tsawon shekaru ba a ga tarzomar da ta yi muni haka ba a wannan ƙasar da ke nahiyar Afirka. Tashin-gwauron-zabi da farashin man fetur ya yi ne ya haifar da rikicin.
Tarzomar da aka samu a babban birnin ƙasar cikin watan Agusta ya yi sun yi sanadiyyar rayukan mutum 25, ciki har da ƴansanda biyar.
Daga watan Maris, farashin man fetur a ƙasar ya kusa ninkawa, daga kuɗin ƙasar Leones 12,000 ($0.86) kan lita ɗaya, zuwa Leones 22,000 ($1.58) a watan Yuli.
A watan Yuli ne babban bankin ƙasar ya fitar da sabbin takardun kuɗi - inda aka cire sifili uku daga kuɗin na Leone - a ƙokarin farfaɗo da darajar kuɗin wadanda tashin farashi ya yi wa illa.

Asalin hoton, AFP
Daga baya an shawo kan tarzomar bayan gwamnati ta ayyana dokar ahan-fita a birnin. An kuma datse intanet domin hana masu zanga-zanga aikewa da saƙonnin sake haɗa wata zanga-zangar.
Daga baya shugaban Saliyo Julius Maada Bio ya bayyana zanga-zangar a matsayin wani yunƙuri na hamɓarar da gwamnatinsa. Sai dai mutanen ƙasar da dama sun musanta hakan, sun shaida wa BBC cewar suna gudanar da zanga-zangar ce domin nuna adawa da tashin farashin man fetur da na abinci.
To amma ba Saliyo ce kawai ke fama da waɗannan jerin zanga-zanga kan tsadar rayuwa ba.
Matsalar mai ta zama ruwan-dare
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Bayan nazari kan alƙaluman da shirin Armed Conflict Location and Event Data Project (Acled) kan zanga-zanga a ƙasashen duniya, BBC ta gano cewar tsakanin watan Janairu zuwa Satumba na wannan shekara mutne a kasashe sama da 90 da wasu ƙarin yankuna sun hau kan tituna domin nuna adawa da farashi da kuma ƙarancin man fetur.
Kashi ɗaya bisa uku kuma su ne waɗanda ba a yi zanga-zanga a cikin su ba ko sau ɗaya a 2021. Misali, a Spaniya ba a yi zanga-zanga ba a 2021, amma ɗaiɗaikun mutane sun yi tattaki har sau 335 a cikin watan Maris na wannan shekara.
Baya ga Antarctica, babu nahiyar da ba a samu zanga-zanga kan man fetur ba a cikin wata uku da suka gabata.
A Indonesia an gudanar da zanga-zanga kan man fetur sau 600 a cikin wannan shekarar, a 2021 kuwa sau tara ne kawai aka yi.
A Italiya an yi irin wannan zanga-zanga sau 200 cikin wata takwas na 2022, a bara kuwa sau biyu kawai aka yi. A Ecuador kuwa an yi irin wannan zanga-zanga sau 1000 kan matsalar man fetur a watan Yuni kaɗai.
Wani abu da ya fi bai wa Henry Wilkinson mamaki, wanda shi ne shugaban tattara bayana na Dragonfly, wata ƙungiyar taro, shi ne inda ake ci gaba da zanga-zangar.
"Abin da ya sha banban shi ne ana samun zanga-zanga a wuraren da ba a samu a baya. Yaƙin Ukraine ya bayar da nasa gudumawar. Samun mafita kan matsalar zai warware wasu rikice-rikicen da ake fama da su a duniya." a cewarsa.
Dalilan da suka haifar da matsalar
Yaƙin Ukraine ɗaya ne kawai daga cikin matsalolin da ke ingiza tashin farashin mai.
Ɗanyen mai ya yi arha a farkon ɓullar annobar korona saboda an rufe kamfanoni da dama wanda ya rage buƙatar da ake da ita ta makamashi. To amma bayan lamurra sun fara daidaita sai buƙatar makamashi ta ƙaru, masu samar da ɗanyen man su ta ƙoƙarin ganin sun cimma yawan man da ake buƙata, wanda ya tayar da farashin.
Yanzu haka darajar dalar Amurka ta ƙaru fiye da kowane lokaci idan aka kwatanta ta da kuɗaɗen man yan ƙasashe kamar 'fan', da 'yuro', da 'yuan', da 'yen'. Ana cinikayyar ɗanyen man da ake samar da man fetur ne da dalar Amurka. Saboda haka idan darajar kuɗin ƙasa ta yi rauni, hakan zai ƙara munana farashin man fetur.
A ƙarshe, yaƙin Ukraine ya sanya ƙasashe da dama sun dakatar da sayen mai daga Rasha. Hakan ya sanya buƙatar mai daga wasu ƙasashen ta ƙaru, abin da ya haifar da tashin farashi.
Matsalar tattalin arziƙi ta koma ta siyasa
A cikin ƙasashe 92 da suka fuskanci tarzoma sanadiyyar farashin man fetur, Sri Lanka ce lamarinta ya janyo hankalin duniya a wannan shekarar bayan da gagarumar zanga-zangar da aka gudanar ta kawo ƙarshen gwamnatin shugaba Gotabaya Rajapaksa.
Al'ummar Sri Lanka na fama da mummunan tsadar rayuwa yayin da farashin mn fetur da na abinci da magunguna suka tashi a ƙasar, wadda tashin farashi ya fi na kowace ƙasa muni a nahiyar Asia.

Wimala Dissanayaka, mai shekara 48 ta tana sayar da kayan miya a unguwar masu kuɗi ta Thalawathugoda da ke birnin Colombo. Ta ce yanzu iyalanta suna rayuwa ne hannu-baka hannu-ƙwarya.
"Farashin kaya sun yi mummunan tashi. Rayuwa na kara tsada amma kuɗaɗen shigarmu na nan yadda suke." a cewarta.
"Ina da yara uku kuma farashin sufuri ya yi matuƙar tashi, yanzu yaro ɗaya kan kashe 100 rupee ($0.27) domin zuwa makaranta. Saboda haka ina kashe 600 rupee ($1.66) ke nan kan yara uku a kowace rana.
Wimala ta ce yanzu ba ta iya cika tankin ƙaramar motarta domin ɗaukan kayan gona daga gona zuwa kasuwa. Saboda haka yanzu sai dai ta ɗauki hayar mota tare da sauran ƴan kasuwa.
"Abubuwa sun yi tsada, masu sayen kaya ba su son kashe kuɗi sosai. Waɗanda a baya suke sayen 500 grams ko kilogiram ɗaya na kayan miya, yanzu sai dai su sayi na gram 100 ko gram 250. Haka nan wadanda a baya suke zuwa a cikin mota ko babur yanzu sai ka ga sun zo a ƙafa ko kuma su turo baro."
Ba a san ranar samun sauƙi ba
Yayin da gwamnatoci a faɗin duniya ke ta hankoron ganin sun nemo mafita game da matsalar tattalin arziƙi, mtane na ci gaba da gudanar da zanga-zanga. Wasu har suna rasa rayukansu.
Binciken BBC ya gano cewa a cikin wata tara da suka gabata. sama da mutum 80 ne suka mutu sanadiyyar zanga-zangar tsadar mai. Waɗannan sun haɗa da na ƙasashen Argentina, da Ecuador, da Guinea, da Haiti, da Kazakhstan, da Panama, da Peru, da Afirka ta kudu, da kuma Saliyo.
Idan muka waiwaya birnin Freetown, abubuwa sun lafa a birnin, yawancin kasuwanni sun buɗe. Amma ga Abdul, mahaifin Kahdija da ɗaukacin iyalansa , rayuwa ba za ta sake dawo kamar yadda take ba a baya.
"Ɗiyata yarinya ce mai cike da buruka. Yanzu ta mutu," a cewarsa.











