Nunes ya shiga yajin aiki kan komawa Man City daga Wolves

Matheus Nunes

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Za a ci tarar dan wasan Wolves, Matheus Nunes bayan da ya yi baya zuwa atisaye a kokarin da yake yi na komawa Manchester City.

Wolves sun yi watsi da tayin Fam miliyan 47 da City ta yi kan dan wasan na Portugal mai shekara 25 a makon da ya gabata.

Kungiyar na tsammanin wani sabon ingantaccen tayi kafin a rufe kasuwar cinikin 'yan wasa ranar Juma'a.

Nunes bai halarci atisaye a ranakun Lahadi da Litinin ba, kuma bai samu izinin yin haka daga koci Gary O'Neil ba.

An fahimci cewa Wolves na son sama da fam miliyan 60 kan Nunes, wanda ya bayyana bukatarsa ta komawa kungiyar Pep Guardiola.

Wolves ta dauko dan wasan ne kan kwantiragin shekaru biyar a bazarar da ta gabata, inda ta biya Sporting Lisbon fam miliyan 38.

Nunes ya kasance babban jigo a zango na biyu na kakar wasan da ta gabata yayin da Wolves ta kare a mataki na 13 a kan teburi.