'Mutane sun wahala a Nijar kuma suna neman wanda za su ɗora wa laifi'

Wani mutum a wata kasuwa da ke Yamai

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana ci gaba da hada-hada a kasuwannin birnin Yamai duk da rufe iyakoki
    • Marubuci, BBC
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, reporter
    • Aiko rahoto daga, Niamey, Niger
  • An wallafa

Ƙasata Nijar ba ta cika kasancewa cikin labarai ba a shafukan jaridu na duniya, amma wannan batu ya canza daga ranar 26 ga watan Yuli.

An fara ne da yaɗa jita-jita cewar ana yunƙurin juyin mulki a fadar shugaban ƙasa.

Nan take na tashi na kama aiki, na fara tuntuɓar mutanen da na sani domin neman gaskiyar lamarin.

Ba a ɗauki lokaci mai tsawo ba - a daren kwamandan dakarun tsaron fadar shugaban ƙasa ya fito ya bayyana cewa, suna tsare da Shugaban Mohamed Bazoum. An kifar da gwamnatin zaɓaɓɓen shugaban ƙasar.

Bayan kwana biyu, Janar Abdourahmane Tchiani ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban ƙasa.

Ban samu isasshen barci ba tsawon mako biyu. Ana son a yi magana da ni daga kowanne sashe na BBC, to amma samu na a waya, ya zama wani abu mai matuƙar wahala.

Bayan kwanaki kaɗan sai lamurra suka fara sauyawa a yadda rayuwa ke gudana.

Babu daɗewa kuma ne aka fara samun sauyi a cikin gari, 'ko dai kuna tare da mu ko akasin haka', yanzu dai sojojin da suka yi juyin mulki su ne ke kan iko, tare da magoya bayansu'.

Lokacin da BBC ta bayar da rahotannin duk abubuwan da ke faruwa ciki har da matakan ƙungiyar Ecowas da na Ƙasashen Yamma da kuma abubuwan da suka haifar.

Aikina nake yi, ina bayar da rahoto cikin gaskiya a kan duk abubuwan da ke faruwa.

Amma wasu daga cikin masu saurare da kallonmu a Nijar sun fi son labaran da suka yi daidai da muradinsu.

Magoya bayan Rasha da magoya bayan Tchiani da masu ƙyamar Faransa waɗannan duka sun bayyana abubuwan da ke faruwa, kuma nan take na fahimci haka.

...

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An girke jami'an 'yan sanda da dama a babban birnin ƙasar
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kan haka sai na fara bibiyar shafukan sada zumunta.

Ana haka sai ran nan sojojin juyin mulkin suka yi barazanar korar 'kafafen watsa labarai na waje'. Na lura akwai matukar hatsarin fita titunan babban birnin ƙasar Yamai, domin yin rahoto a kan zanga-zangar da magoya bayan Tchiani ke yi a lokacin.

Gudanar da aikina ya zama mai wahalar gaske, haka ni ma yanayin da na shiga kenan.

A yanzu nakan kwashe galibin tsawon wuni, ba tare da wutar lantarki ba, tun daga lokacin da Najeriya ta katse wutar.

Ba ƙaramin aiki ne ba samun caji ga ƙaramar kwamfuta da wayata, abin da kan ba ni matsala sosai. Gani nake waɗannan abubuwa tamkar matsalolin 'farkon duniya' sannan idan na kasa yin aikina yadda ya kamata,to, ta wacce hanya jama'a za su san ainihin abin da ke faruwa?

Baya ga waɗannan abubuwa, abinci ma, yana matuƙar wahalar samu saboda takunkuman da Ecowas ta kaƙaƙaba Nijar.

Mutane sun tagayyara kuma a fili take suna neman wanda za su ɗora wa wannan laifi, ga shi kuma kusan kowa na fama da ƙarncin kuɗi. Iya abin da mutum zai iya cirewa kowacce rana a banki, bai fi CFA 50,000 ba.

Ga kuɗin da yawa amma tashin farshin ya karya darajarsu.

...

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu goyon bayan juyin mulki na kaɗa tutoci a lokacin wata zanga-zangar ƙyamar amfani da ƙarfin soji da Ecowas ke son yi da takunkuman da ta sakawa Nijar a ranar 20 ga Agustan 2023.

Hakan ya tilasta mini tsuke bakin aljihu a duk lokacin da na shiga kasuwa.

A da nakan ga fuskokin mutane cikin annuri, amma yanzu duk wannan ta kau. Kowa maganar juyin mulki yake yi, amma kuma ɓangare guda ne ke 'jagorantar' tattaunawar.

Duk wanda ya kuskura ya yi suɓul da baka ya soki juyin mulkin to zai sha duka ko kuma a far wa gidansa.

Ni kaina jikina na ba ni a kowanne lokaci shugabannin sojojin na iya sanyawa a kama ni.

Kullum cikin dare, sai wannan tunani ya zo min a rai amma ko yaushe nakan zama mai hattara.

A duk lokacin da na kasance ni kaɗai a gida, nakan rufe ƙofar sosai kuma ba na buɗewa duk wanda ya ƙwanƙwasa.

Wannan rayuwar nake gudanarwa, kuma duk da haka ina son ci gaba da shaida wa duniya labarin halin da ƙasata ke ciki.