An yi safarar sa don cire masa ƙoda yanzu kuma ya shiga ɓuya

Wani da ya sayar da ƙodarsa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani mutum kenan da ya sayar da ƙodarsa yake nuna tabon tiyatar da aka yi masa
An wallafa

Lokacin da wani matashi ɗan Najeriya ya sa ƙafarsa a ofishin 'yan sanda na kusa da filin jirgin saman Heathrow a birnin Landan, shi ne ya haifar da aiwatar da dokar yaƙi da cire sassan jikin mutum a Birtaniya.

BBC ta samu damar gani da kuma tattaunawa da rukunin 'yan sandan da suka yi bincike a kan lamarin.

Daniel na gab da fuskantar abu mafi tsoro a rayuwarsa.

Yana zaune a wani ɗakin ganin likita da ke asibitin Royal Free da ke Landan, yana zantawa da likitoci cikin wani jigari-jigarin Ingilishinsa.

Ɗan shekara 21 ɗin ya je Landan ne daga Legas, saboda abin da aka bayyana masa da cewa "damar da za ta sauya rayuwarsa".

Ya zaci zai samu aiki ne mai tsoka.

Yanzu kuma likitoci na wayar masa da kai game da hatsarin tiyata da kuma buƙatar kulawa a tsawon rayuwarsa.

A lokacin ne Daniel, kamar yadda ya faɗa wa masu bincike, ya gane cewa babu wata maganar aiki, kuma an kai shi Birtaniya ne don ba da gudunmawar ƙoda ga wata wadda bai san ko wace ce ba.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Cikin sa'a, likitocin sun fahimci cewa bai san abin da ke shirin faruwa ba, kuma da alama an tilasta masa ne. Saboda haka sai suka dakatar da aikin.

Bayan ya koma gida, sai wasu mutane guda biyu suka je duba shi. A nan ne kuma ya jiyo ana maganar mayar da shi Najeriya don a cire ƙodar tasa a can.

Kawai sai ya gudu. Bayan shafe kwana biyu yana barci cikin gigita, sai ya shiga ofishin 'yan sanda kuma ya zayyana musu abin da ke faruwa.

Lamarin ya faru ne tun a watan Mayun 2022, amma yanzu Daniel - wanda ba sunansa na gaskiya ba ne - yana zaune a inda yake samun kariyar 'yan sanda.

Shirin BBC na File on 4 ya fahimci cewa lamarin ya ankarar da 'yan sandan Birtaniya game da yunƙurin da wasu suka taɓa yi na cire sassan jikin ɗan'adam.

Sun ƙunshi:

Lamarin wani ɗan Indiya mai shekara 60 da ɗoriya da aka kama a Birtaniya kan zargin haɗa baki don zaluntar wani mutum ta hanyar cire sashen jikinsa. A farkon watan nan ne aka kama shi, amma dai an ba da belin sa.

Wannan wani lamari ne da hukumar Human Tissue Authority, wadda ke ba da izinin yin tiyatar sassan jiki, ta ankarar da 'yan sanda bayan ta ƙi amincewa da buƙatar.

Wasu tsegunguman da hukumomi suka kai wa 'yan sanda na mutanen da suka koma Birtaniya bayan sun biya kuɗin yin tiyata ta hanyar da ta saɓa wa doka a wasu ƙasashen.

A gefe ɗaya, 'yan sandan Birtaniya sun ce suna ci gaba da bincike kan wasu da ake zargi game da lamarin Daniel.

Mutumin da aka yi safarar sa

Lamarin Daniel ya nuna dabarun da masu safarar mutane ke bi wajen shigar da su Birtaniya ta hanyar ɓad-da-kama.

Lokacin da aka bai wa Daniel izinin aiki a Birtaniya yana can Najeriya, sai aka nemi ya je a yi masa gwajin jini. Ya zaci a wajen neman biza ne, amma haƙiƙa ana so ne a ga ko jininsa yana da lafiyar da zai jure tiyatar cire ƙoda.

Sai aka ɗora shi a jirgi zuwa Landan - amma ba tare da kuɗi ba, kuma aka karɓe fasfo ɗinsa. Haka aka dinga bin diddigin duk wani motsinsa.

Daga nan, sai masu safararsa suka gabatar da shi ga wata matashiya 'yar Najeriya, wadda ke fatan za a dasa mata ƙodarsa.

Sonia mai shekara 25 a lokacin, na fama da wani nau'in ciwon ƙoda mai tsanani. Tana buƙatar ƙoda kuma ana yi mata wankin ƙodar tsawon awa biyar a kullum kuma sau uku ko huɗu a mako.

Sonia da Daniel

Asalin hoton, Metropolitan Police

Bayanan hoto, Sonia Ekweremadu tare da Daniel - ba sunansa na gaskiya ba ne - a wani gidan cin abinci

Duk yaudarar ba ta yi nasara ba, kuma Daniel ya garzaya wajen 'yan sanda.

Abubuwan da ya shaida wa 'yan sanda sun kai ga bincike har kan mahaifin Sonia, ɗaya daga cikin manyan mutane a Najeriya.

Yayin zaman kotu a farkon shekarar nan, Ekweremadu ya ce an yi masa rufa-rufa, kuma bai taɓa niyyar cutar da Daniel ba. Hasali ma, an faɗa wa alƙalin cewa sanatan ya sha ba da tallafinsa wajen ƙirƙiro dokokin hana ba da ƙoda don neman kuɗi a Najeriya.

Sanata Ekweremadu shahararren ɗan siyasa ne a Najeriya

Asalin hoton, Met Police

Bayanan hoto, Sanata Ekweremadu shahararren ɗan siyasa ne a Najeriya

Dillali

An faɗa wa kotu cewa ba Daniel ne kaɗai mutumin da aka taɓa kai wa Birtaniya don cire masa ƙoda ba. An yi wata tiyata - ita ma ba bisa doka ba - a 2021.

Mutumin da ya karɓi waccan ƙodar, da aka dasa masa, na tare da Ekweremadu da matarsa a gaban alƙali. Shi ne Dr Obinna Obeta, dillalin da ya shirya yadda za a ciri ƙodar Daniel.

Dr Obinna Obeta ya san duk yadda ake yi saboda shi ma a asibitin Royal Free aka yi tiyatar cire ƙodar da aka dasa masa.

Alƙalin kotun, Mista Johnson, ya ce an yi wa hukumomi ƙaryar cewa wanda ya ba da ƙodar da wanda aka bai wa a 2021 'yan'uwan juna ne. An ce ɗan ɗan'uwansa ne amma daga baya an gano ba su da wata alaƙa.

KOtun ta kama Dr Obinna Obeta, wanda ya shiga tsakani , da kuma matar sanatan mai suna Beatrice, da laifi

Asalin hoton, Met Police

Bayanan hoto, Kotun ta kama Dr Obinna Obeta, wanda ya yi dillanci, da kuma matar sanatan mai suna Beatrice, da laifi

Tafiya aikin tiyata

A watan Yulin na 2022 ne, aka haramta zuwa wata ƙasa don ba da gudunmawar ƙoda a biya mutum a Ingila da Scotlands da kuma Wales.

An umarci dukkan likitocin ƙoda su sanar da hukuma duk wanda ya nemi kulawa bayan an yi masa tiyatar a wata ƙasa daban.

Wani ƙwararren likitan ƙoda a Birmingham, Adnan Sharif, ya ce abu ne mai wuya a iya ba da shaida amma sun san "ana yi".

"Abin da ake nufi idan aka kama mutum da laifi"

Ba abu ne mai sauƙi ba wajen samun mutum da laifi a ƙarƙashin dokar hana bauta ta zamani.

A lamarin Daniel, 'yan sanda sun zaci binciken zai ɗauke su shekaru masu yawa, saboda waɗanda ake zargi sun fice daga ƙasar.

Amma ranar 21 ga watan Yunin 2022, ɗan sanda Andy Owen ya samu kira a waya cewa Ike Ekweremadu da matarsa Beatrice na kan hanyarsu ta zuwa Landan.

Nan take ya tattara ayarin jami'ansa zuwa Hethrow, inda 'yan sanda ɗauke da makamai suka taso ƙeyar ma'auratan daga jirgi.

Bayan an ƙwace wayoyinsu, an ga hujjar da ta nuna an biya naira miliyan 4.5 a matsayin kuɗin ƙodar.

"Kamar neman dukiya ne," a cewar ofisa Owen. "Na yi ta neman hujjoji a kansu."

Sai dai kuma hukunta hamshaƙin ɗan siyasa irinsa ba abu ne mai sauƙi ba.

'Yan majalisar Najeriya sun so a mayar da shari'ar zuwa Najeriya yayin da ake ƙoƙarin fara ta. Sun kuma so su "samu ganin matashin", in ji Muƙaddashin Sufritanda Andy Furphy.

Bayan neman shawarwari a ɓangaren shari'a, 'yan sanda sun hana su ganin sa.

Shirin BBC na File on 4 ya yi magana da sanatan da ya jagoranci 'yan majalisar zuwa Birtaniya, Sanata Adamu Bulkachuwa, inda suka haɗu da Ekweremadu a gidan yari. Ya ce ya so ya yi amfani da "ƙarfin gwamnati da kuma na difilomasiyya wajen ganin sun sasanta lamarin".

A ranar 23 ga watan Maris aka kama mutanen uku da laifi kan tuhumar da aka yi musu ta zaluntar Daniel. An ɗaure Ekweremadu shekara tara da wata takwas. Matarsa shekara huɗu da rabi. Shi kuma dillalin da ya shiga tsakani, Dr Obeta, shekara 10.

Ba a kama Sonia da laifi ba.

Muƙaddashin Saje Owen na tare da Daniel a kotu.

"Abin da ya ce, 'Me ake nufi da an kama mutum da laifi?' Abin da ya sani ke nan idan ana maganar laifi a kotu."

Mutane sun sauya masa kallo bayan ya yi wannan tambayar da kuma ƙin amincewa da ya yi ya karɓi fansar kuɗi, in ji Det Sgt Owen.

Daniel's brother says his father and their siblings have been crying every day because of Daniel's disappearance
Bayanan hoto, Ɗan uwan Daniel ya ce sun yi ta kuka kowace rana, har mahaifinsu ya kamu da rashin lafiya

Dangin Daniel

A can Najeriya kuma, lamarin ya jefa dangin Daniel cikin tsoro.

Suna fargabar kai musu hare-hare daga magoya bayan ɗan siyasar da ya jawo wa ɗauri.

Filin File on 4 ya haɗu da ɗan uwan Daniel a Legas, inda matashin ke sayar da kayayyakin waya kafin zuwansa Birtaniya.

Ya ce bai sake magana da ɗan uwansa ba tun bayan da ya ɓace a watan Fabrairun 2022, kuma sai a labarai ya ji inda yake.

"Mun yi ta kuka kowace rana, har mahaifinmu ya kama rashin lafiya," in ji shi.

"An yaudari Daniel an ɗauke shi."

Yanzu Daniel na cikin fargaba a rayuwarsa. 'Yan sanda ne ke ba shi kariya a Birtaniya kuma yana ganin ba zai iya komawa Najeriya ba. Ba lallai ma ya sake ganin danginsa ba.

Ya tsira da ƙodarsa kuma ya kafa tarihi a sashen shari'a, amma kuma an lalata masa rayuwa.