Laporte zai koma taka leda da Ronaldo

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan baya na Sipaniya Aymeric Laporte ya bar Manchester City zuwa kungiyar Al Nassr da ke buga Saudi Pro League kan kuɗi fam miliyan 23.6.
Dan wasan mai shekaru 29 ya koma City ne daga Athletic Bilbao a watan Janairun 2018 kan farashin fam miliyan 57.
Ya taimaka wa City lashe manyan kofuna 12 amma ya buga wasanni 24 kacal yayin da City ta lashe manyan gasanni uku a kakar wasan da ta gabata.
A cikin sakon bankwana da ya aike a shafukan sada zumunta, Laporte ya gode wa magoya bayansa da abokan wasansa saboda "lokaci ne da ba zai taba mantawa ba" a kulob din.
Laporte ya buga wa City wasanni 180, inda ya zura kwallaye 12, amma bai samudamar buga wasanni da dama ba a kakar bara.
Koci Pep Guardiola ya zabi amfani da ‘yan wasan baya Manuel Akanji da Nathan Ake akai-akai, kuma City ta kashe fam miliyan 77 wajen kawo dan wasan bayan Croatia Josko Gvardiol a farkon wannan watan.
Shi ne babban dan wasa na baya-bayan nan da ya koma Al Nassr, inda zai hade da Cristiano Ronaldo da Sadio Mane, da Marcelo Brozovic da Alex Telles da kuma Seko Fofana a kungiyar.







