Binciken BBC da ya gano miyagun dillalan da ke kai ma'aikata Birtaniya

Hoton bidiyon da aka naɗa a sirri na nuna Dr Kelvin Alaneme yana bayanin yadda yake sayar wa 'yan ƙasar waje aikin yi a Birtaniya
Bayanan hoto, Hoton bidiyon da aka naɗa a sirri na nuna Dr Kelvin Alaneme yana bayanin yadda yake sayar wa 'yan ƙasar waje aikin yi a Birtaniya
    • Marubuci, Tamasin Ford
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Sashen Binciken Gaskiya na BBC da na Africa Eye
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

BBC ta bankaɗo ayyukan damfara na wasu dillalai masu ɗaukar aiki da ke yaudarar 'yan ƙasar waje da ke son yin aikin lafiya a Birtaniya.

Ɗaya daga cikin miyagun wani likita ne ɗan Najeriya da ya yi aiki da hukumar inshorar lafiya ta NHS a ɓangaren nazarin tunanin ɗan'adam wato psychiatry a Turance.

Ma'aikatar Harkokin Cikin Gidan Birtaniya ta aminta cewa ana zalintar mutane, amma binciken sirri na BBC ya gano yadda ake aiwatar da damfarar cikin sauƙi, da kuma samun kuɗi mai yawa.

Abubuwan da binciken sirrin ya gano sun ƙunshi:

  • Sayar da aikin yi ta ɓarauniyar hanya ga kamfanonin aikin lafiya na Birtaniya
  • Ƙirƙiro takardun biyan albashi na ƙarya domin ɓoye wasu ayyukan da babu masu su
  • Sauya dabara daga aikin lafiya zuwa ɓangaren gine-gine, wanda shi me ke fuskantar ƙarancin ma'aikata

Tun bayan da gwamnati ta ɓullo da wani sabon salon bayar da biza - wanda zai bai wa ma'aikatan lafiya damar aiki a Birtaniya - aka fara samun hauhawar damfara. An faɗaɗa tsarin don ya ƙunshi masu aikin kula da tsofaffi a 2022.

Kafin mutum ya nemi bizar, sai ya samo shaida da ake kira "Certificate of Sponsorship" (CoS) daga wani kamfani da ke da rajista a Birtaniya. Wajen neman wannan shaidar ce kuma wasu miyagun dillalai ke damfarar mutane.

"Damfarar da ake yi wajen neman bizar aikin kula da lafiya na da yawa sosai," in ji Dora-Olivia Vicol, shugabar cibiyar Work Rights Centre da ke taimaka wa 'yan cirani nhaƙƙinsu a wuraren aiki a Birtaniya.

"Ina ganin abin fa ya zama matsalar ƙasa baki ɗaya."

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

BBC ta tura 'yanjarida biyu da suka ɓatar da kama domin haɗuwa da dillalan da ke kai 'yan ƙasar waje Birtaniya.

Ɗaya ya hadu da Dr Kelvin Alaneme, wani likita ɗan Najeriya kuma wanda ya kafa kamfanin CareerEdu da ke Harlow Essex.

Shafinsa na intanet ya bayyana sana'arsa a matsayin "wata gada da ke sadar da matasan Afirka da damarmaki", inda ya yi iƙirarin cewa yana da kwastomomi 9,800.

Bayan ya amince cewa 'yarjaridar ta BBC na da alaƙa mai ƙarfi a sashen kula da lafiya, Dr Alaneme ya yi ƙoƙarin ɗaukar ta aiki a kamfaninsa yana mai cewa za a samu kuɗi sosai.

"Kawai ki nemo min wurin aikin kula da tsofaffi. Ni kum zan mayar da ke miloniya," a cewarsa.

A matsayin abokin hulɗa, an bai wa 'yarjaridarmu muhimman bayanai game da yadda dillalai irinsu Alaneme ke aiki. Ya ce zai biya fam 2,000 kan kowane wurin aiki ɗaya da ta samo, sannan zai biya ƙarin kamasho na fam 500.

Daga nan kuma sai ya sayar da guraben aikin ga masu nema a Najeriya.

Karɓar kuɗi don bai wa mutum aiki haramun ne bisa dokokin Birtaniya.

"Bai kamata su [masu neman aikin] biya kuɗi saboda kyauta ne. Ya kamata ya zama kyauta," a cewarsa, yana yin ƙasa-ƙasa da murya.

"Amma suna biya ne suna tunanin ita kaɗai ce hanyar da za su samu."

BBC ta fara bin diddiginsa ne bayan ƙorafe-ƙorafe a dinga yi a kan ayyukansa a intanet.

Praise daga kudu maso gabashin Najeriya kuma mai shekaru kamar 30, ɗaya ne daga cikin mutanen da suka yi ƙorafi kan Dr Alaneme, inda ya ce ya biya shi sama da fam 10,000 don nema masa aiki a Birtaniya.

Ya ce an faɗa masa zai yi aiki da wani kamfani mai suna Efficiency for Care da ke Clacton-on-Sea. Sai bayan ya je ya tabbatar aikin na ƙarya ne.

Praise ya ce ya biya Dr Alaneme sama da fam 10,000 don ya sama masa aiki a Birtaniya
Bayanan hoto, Praise ya ce ya biya Dr Alaneme sama da fam 10,000 don ya sama masa aiki a Birtaniya

"Da na san babu aikin da ba zan zo nan ba," in ji shi. "Aƙalla dai a Najeriya, idan ba ni da kuɗi zan nemi iyayena ko ƙanwata don na je na ci abinci a kyauta. Amma lamarin ba haka yake ba a nan. Za ka yi ta zama da yunwa."

Bincikenmu ya nuna cewa Efficiency for Care ya ɗauki mutane kamar 16 aiki a 2022, da kuma 152 a 2023. Amma kuma wata wasiƙa da hukumomi suka aika masa a watan Mayun 2023 ta nuna cewa ya bai wa mutum 1,234 shaidar CoS tsakanin watan Maris na 2022 da Mayun 2023.

An ƙwace lasisin Efficiency for Care na ɗaukar 'yan ƙasar waje aiki a Yulin 2023, abin da ke nufin ba za su iya sake ɗaukar ɗan ƙasar waje aiki ba, amma kuma duk da haka suka ci gaba da yin hakan.

Ya faɗa wa BBC cewa yana musanta batun haɗa kai da Dr Alaneme, kuma ya yi aikinsa bisa ƙa'ida na ɗaukar ma'aikata daga Najeriya da wasu ƙasashen.

A wata haɗuwar ta daban, Dr Alaneme ya bayyana yadda ma yake ɗaukar aikin boge.

Ya ce amfanin samun CoS wadda ba a haɗa ta da wani aiki ba shi ne "mutum zai iya zaɓar duk garin da yake so".

"Kana iya zuwa Glasgow. Ko kuma Landan. Za ka iya zama a ko'ina," a cewarsa.

Amma wannan ba gaskiya ba ne. Idan mutum ya je Birtaniya da bizar aikin kula da lafiya kuma ya ƙi yin aiki a inda aka ba shi, za a iya ƙwace bizarsa kuma ma za a iya korarsa daga ƙasar.

Ya musanta batun cewa kamfaninsa CareerEdu na damfara ne ko kuma mai sayar wa mutane aikin yi. Ya ƙara da cewa kuɗin da Praise ya ba shi wani kamfanin ɗaukar aiki aka bai wa don sama wa Praise ɗin wurin zama da kuɗin motarsa da horarwa.

BBC ta kuma naɗi bidiyon sirri na wani dillalin mai suna Nana Akwasi Agyemang-Prempeh, bayan mutane da yawa sun shaida wa BBC cewa sun biya shi kuɗaɗe masu yawa don nema wa mutanensu aikin da daga baya suka gano na ƙarya ne.

Sun ce takardun shaidar CoS da ya dinga ba su na boge ne, kwafin irin wanda CoS na gaskiya ke zuwa da su.

Wannan matar ta ce ta gabatar da 'yan'uwa da abokan arziki da yawa ga Mr Akwasi Agyemang-Prempeh waɗanda suka biya fam 35,000 kan takardun da aka ba su na jabu
Bayanan hoto, Wannan matar ta ce ta gabatar da 'yan'uwa da abokan arziki da yawa ga Mr Akwasi Agyemang-Prempeh waɗanda suka biya fam 35,000 kan takardun da aka ba su na jabu

Mun gano cewa Mr Agyemang-Prempeh ya fara bai wa mutane takardun aiki a ɓangaren gine-gine na jabu. Ya kafa kamfaninsa na gine-gine kuma ya samu lasisin ɗaukar ma'aikata daga Ma'aikatar Harkokin CIkin Gida.

Ɗanjaridarmu da ya yi shigar burtu a matsayin ɗankasuwa daga Uganda da ke son kawo ma'aikata daga Uganda, ya nemi ji daga wajen Agyemang-Prempeh ko hakan za ta yiwu.

Ya ce zai yiwu amma sai an biya fam 42,000 kan mutum uku.

"Yanzu muatane sun fara komawa ɓangaren kimiyya da fasaha," in ji Agyemang-Prempeh.

Nana Akwasi Agyemang-Prempeh kenan wanda ya koma ɓangaren gine-gine maimakon kula da lafiya
Bayanan hoto, Nana Akwasi Agyemang-Prempeh kenan wanda ya koma ɓangaren gine-gine maimakon kula da lafiya

An ƙwace lasisi sama da 470 na ɓangaren aikin kula da lafiya a Birtaniya daga Yilun 2022 zuwa Disamban 2024. Waɗannan kamfanonin da aka ƙwace wa lasisi, su ne suka ɗauki mutum 39,000 aiki tun daga Oktoban 2020.

Yanzu hukumomi sun ƙwace lasisinsa na ɗaukar aiki. Da BBC ta matsa masa da tambaya, sai ya ce ai shi ma wasu ne suka damfare shi ba tare da sanin cewa takardun jabu yake bayarwa ba.

Wata wasiƙa da ma'aikatar harkokin cikin gida ta aike wa BBC ta ce "yanzu tana da sababbin tsauraran dokoki kan kamfanoni marasa gaskiya da ke zalinci da tsarin biza" kuma za ta "rufe duk kamfanin da yake saɓa dokokin Birtaniya wajen ɗaukar ma'aikata daga ƙasashen waje".

Binciken BBC ya taɓa gano irin wannan zambar a ɓangaren biza da ake zalintar 'yan Kerala a Indiya, da kuma ɗaliban ƙasashen waje a Birtaniya .

A watan Nuwamban 2024, gwamnati ta ƙaddamar da yaƙi kan "miyagun" kamfanoni da ke ɗaukar ma'aikata daga ƙasashen waje. Bugu da ƙari, daga 9 ga watan Afrilu, za a buƙaci kamfanoni su dinga ɗaukar ma'aikata kula da lafiya na ƙasashne waje mazauna Ingila kafin ɗauka daga waje.

Tawagar bincike: Olaronke Alo, Chiagozie Nwonwu, Sucheera Maguire, Nyasha Michelle, da Chiara Francavilla