‘Babu abin da nake yi sai kuka’: 'Yan gudun hijirar Afghanistan na cikin garari

- Marubuci, Hafizullah Maroof
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Afghan Service
- Marubuci, Kawoon Khamoosh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Aiko rahoto daga, Kabul
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Rahmatullah ya shafe tswon shekara 46 a Pakistan a matsayin ɗan gudun hijira daga Afghanistan da ba a yi wa rajista ba.
Yana zaune a lardin Khyber Pakhtunkhwa da ke arewa maso yammacin Pakistan, kuma tsawon waɗannan shekaru, shi da iyalansa suna ɗaukar lardin a matsayin gida a gare su.
Sai dai a watan da ya gabata, an ba shi wa'adin kwana 10 da ya tattara kayansa don ficewa daga yankin.
An tilasta masa tare da dubban 'yan gudun hijirar Afghanistan komawa ƙasarsu ta asali, bayan da hukumomin Pakistan suka sanya wa'adi ga 'yan gudun hijira marasa rajista don ficewa daga ƙasar.
“Na shiga matuƙar damuwa. Da ni mahaifiyata ta dogara, kuma ina cikin damuwa kan halin da iyalina za su shiga idan aka ɗaure ni a gidan yari, wa zai kula da su?" in ji shi.
Ya isa kan iyakar Torkham tare da iyalansa 16. Yayin da zafin rana ya kai maki 43 a ma'aunin salshiyos, mahaifiyarsa - wadda ta manyanta - na cikin baro ana turata. Ta fice daga Afghanistan a shekarar 1978, kafin mamayar tarayyar Soviet.
“Na shafe lokaci mai tsawo a Pakistan. Na je ina ƙarama, amma yanzu na komo a dattijuwa,” in ji mahaifiyar tasa, Nournam mai shekara 85.
“Sun doke mu sannan suka fitar da mu daga ƙasar. Muma zaman da muke yi a ƙasar tasu ba zaɓinmu ba ne,” in ji Nournama, yayin da take bayanin yadda aka tilasta musu ficewa daga Pakistan.
Mafi yawan 'yan gudun hijirar na komawa ƙasarsu ta asali da ba su santa sosai ba. Majalisar Dinkin Duniya ta ce Afghanistan na ɗaya daga ƙasashen da al'umominsu suka fi zama 'yan gudun hijira a duniya.
Pakistan ta yi gargaɗin cewa za ta fitar da ƙarin 'yan gudun hijirar Afghanistan miliyan ɗaya da ba su da rajista.
Hakan zai sake tagayyara fararen hula masu yawa a Afghanistan.
Rahmatullah ya ce ya tabbata babu abin da iyalinsa za su samu a ƙasarsu sai baƙin talauci, da rashin matsuguni da rashin aikin yi da yunwa da rashin makaranta ga 'ya'yansa mata. Ya ce iyalinsa ba su da wani zaɓi sai rungumar ƙaddara.
“Abin akwai damuwa. Na tabbata hakan zai cutar da mu. Dole na fara sabuwar rayuwa saboda ba ni da komai” in ji Rahmatullah.

Akwai 'yan gudun hijirar Afghanista da aka yi wa rajista fiye da miliyan huɗu da ke zaune a Pakistan, kamar yadda alƙaluman hukuma suka nuna, sai kuma mutum miliyan 1.7 da ke zaune ba bisa ƙa'ida ba, ciki har da iyalan Rahmatullah.
Pakistan ta fara fitar da 'yan gudun hijirar Afghanistan a watan Nuwamba 2023, bayan abin da ta kira 'ƙaruwar hare-haren kan iyaka'.
Kawo yanzu mutum 700,000 aka fitar daga ƙasar.
Rashin sanin makoma
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
'Yan gudun hijirar na sauka a Afghanistan , sai a yi musu rajista da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar dinkin Duniya da sauran ƙungiyoyi masu zaman kansu.
Sun kuma samu tallafin muhimman abubuwan buƙata irin su layin waya da matsugunan wucin-gadi da abinci da kuɗi.
Daga nan sai su fara tunkarar rayuwar da suka ce ba ta da makoma.
An haifi Rozina Safi, mai shekara 24, ta kuma taso a Pakistan. A watan Janairu ne aka fitar da ita daga ƙasar, kuma tun daga lokacin take ci gaba da rayuwa a wani ƙaramin tanti.
Kusan rabin mutanen da Pakistan ta kora na rayuwa ne a lardin Nangarhar da ke gabashin Afghanistan mai cike da ɗimbin jama'a.
A lokacin da Rozina ta koma Afghanistan ba ta san ko'ina ba. 'Yanuwanta ne suka ba ta ɗan wani wuri a gefen gidansu inda ta kafa tantin da take rayuwa a cikinsa.
A lokacin da muka ziyarce ta a unguwar marasa galihu da take zaune a birnin Jalalabad, mun ga wasu tantuna uku da wasu iyalai huɗu ke amfani da su a wani lambu.
“Nan nake rayuwa tare da surukaina. sun bani aron tanti inda nake zaune tare da 'ya'yana biyu mace da namiji. Ban taɓa tsammanin zan shiga wannan hali ba,” in ji ta.
'Yarta Maryam, mai shekara huɗu na cikin mahaifiyarta lokacin da mahaifinta ya ɓace a Pakistan.
Ba a dai san me ya faru da shi ba, amma Rozina ta ce kama shi aka yi, kuma ba su sake ji daga gare shi ba tun daga lokacin.

Asalin hoton, AFP
Kafin Taliban ta karɓe ikon ƙasar a 2021, Rozina ta koma Afghanistan bisa raɗin kanta, to amma ta sake guduwa zuwa Pakisatn bayan Taliban ta ƙwace ikon ƙasar.
Dubban 'yan gudun hijirar Afghanistan ne suka tsere zuwa Pakistan cikin shekara uku da suka gabata.
Bayan ta koma Pakistan Rozina ta riƙa sana'ar ɗinki domin tallafa wa 'ya'yanta, sana'ar da mata irin Rozina ba za su samu damar yi ba a Afghanistan, inda ba a barin mata su yi karatu ko aikin gwamnati.
Mummunan yanayi
Afghanistan na fuskantar gagarumar matsalar jinƙai. Kusan kashi 90 cikin 100 na al'ummar ƙasar na rayuwa cikin talauci.
Rashin aikin yi tsakanin 'yan ƙasar ya tilasta wa dubban 'yan ƙasar tserewa daga cikinta a shekarun baya-bayan nan.
Ƙungiyoyin bayar da agaji na fargabar yawan tserewa daga ƙasar ka iya durƙusar da ita.
Arafat Jamal, sabon daraktan Hukumar Kula da 'Yangudun Hijira na Majalisar Dinkin Duniya a Afghanistan, ya ce tallafin da ƙungiyoyi ke bai wa ƙasar ya ragu da kashi ɗaya bisa uku, kuma akwai buƙatar ƙasashen duniya su talllafa domin magance matsalolin jin ƙai a ƙasar.
“Muna cikin lokacin raguwar tallafi da agajin kuɗi saboda ƙaruwar masu buƙatar tallafin kamar Gaza da Ukraine da Sudan da sauransu'', in ji shi.

Hukumomin Taliban sun ce ba za su iya magance matsalolin jin ƙai da ƙasar ke fama da su ba.
Baz Mohammad Abdul Rahman, daraktan kula da 'yan gudun jihirar Taliban mai kula da lardin Nangarhar ya ce ƙasar na buƙatar tallafi na tsawon shekaru domin magance matsalar kwararar 'yangudun hijirar ƙasar zuwa Pakistan.
''Akwai ƙungiyoyin tallafi kusan 60 zuwa 70 da ke aiki tare da mu. Kuma suna ba mu agaji mai yawa, sai dai baya wadatarwa,” in ji Mista Mr Abdul Rahman.
“Muna buƙatar ci gaba da ba mu tallafi na tsawon aƙalla shekara biyar musamman domin kula da 'yan gudun hijirar da aka tilasta wa komowa daga Pakistan ,” in ji shi.
Majalisar Dinkin Duniya ta kashe dala biliyan 1.8 a Afghanistan tun bayan komawar Taliban mulkin ƙasar, to sai dai majalisar ta yi amanna cewa bai wa ƙasar tallafi a kowace shekara ba zai kawo mafita ga 'yan ƙasar ba.
Rozina na zaune a wata unguwa a wajen birnin Jalalabad, riƙe da 'yarta, Maryam mai shekara huɗu.
“Ina shan wahalar rayuwa ba tare da mijina ba. 'ya'yan kan fita domin barar abin da za su ci da suturar da za su saka. Babu abinda anek iya yi sai kuka. Ina cikin baƙin ciki, to me zan iya yi?











