Me ke talauta 'yansiyasar Najeriya bayan barin mulki?

Siyasa
Bayanan hoto, Al'ummar Najeriya na kallon siyasa a matsayin wadda ke kunshe da munanan siffofi, da suka hada da karya da cin amana da yaudara da munafurci da sauransu.
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Wani bincike da aka gudanar ya gano cewa galibin 'yansiyasar Najeriya da suka riƙe manyan mukamai, kamar 'yanmajalisar dattawa da wakilai da sauransu kan fada cikin talauci lokaci guda da zarran sun sauka daga mukamansu.

Ana danganta karayar tattalin arzikin da suke fuskanta da kashe kuɗi barkatai a lokacin da suke rike da mukaman ta hanyar gina maka-makan gidaje da sayen ababen hawa masu tsada, da kuma rashin kyakkyawan tsari na rayuwa.

Galibinsu kan fuskanci manyan kalubali musamman wajen daukar dawainiyar iyali da abubuwan da suka mallaka, irinsu motoci da na'urorin da suka dasa a gidajensu da ma biyan kuɗin makarantar yara.

Sanata Shehu Sani, ya taba zama ɗan majalisar dattawan Najeriya daga jihar Kaduna, kuma a tattaunawarsa da BBC ya ce abin da ya sa yawancinsu ke faɗawa cikin wannan yanayi shi ne matsaloli na iyalai, abokai da dawainiyar wadanda suka taimaka musu wajen samun kujerar.

Sanata ya kuma ce ga matsalar rashin tsari na fansho kamar tanadin da ake yi wa gwamnoni da shugaban kasa, shiyasa suke talauci nan take muddin babu wani tanadi ko mukami.

Sauyin dabi'u da rayuwar alfarma

g

Wani bincike da masana tattalin arziki suka gudanar, ya nuna abubuwa da dama na taka rawa wajen haifar da talaucin 'yansiyasa, ciki har da kashe kuɗi ba bisa ka'ida ba, da yin kyautar kece raini da gina gidajen da ba a iya tafiyar da su da sauran su.

Dakta Murtala Abdullahi Kwara, malami a sashen nazarin ilmin tattalin arziki a Jami'ar Umaru Musa 'Yar Aduwa da ke Katsina, ya ce akwai wani koyarwa me zaman kanta da ke bayyani kan wannan, saboda dabi'a ce ke sauyawa, lokacin da kake mulki kana kashe kudɗi kwakwalwa ta saba idan ka sauka da wuya ka iya jurewa shiyasa talauci ke zuwa mu su lokaci guda.

Galibin al'umma a Najeriya na yi wa 'yan majalisar kallon wadanda suka tara makudan kuɗaɗe, inda suke yawan dora musu bukatu barkatai, har ma ana fargabar hakan na iya jefa wasu daga cikin 'yan siyasa cikin akidar cin hanci, ko bin hanyoyi masu alaƙa da wata almundahana, domin samun kuɗaɗen da za su ba jama'arsu ko kaucewa faɗawa talauci bayan sun ajiye mukaman.

Sanata Shehu Sani ya ce "daga ranar da aka ce ka zama ɗan majalisa rayuwarka na sauyawa sosai, kama daga hidimar iyali da abokai da sauran jama'a, don haka idan ka bar mulki cigaba da wannan rayuwa na da matukar wahala, shiyasa ake ce mu su sun talauce".

Tsari na rayuwa

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Masana tattalin arziki irinsu Dakta Murtala Abdullahi Kwara, sun zayyano matakan da za su taimaka wa jama'a fita irin wannan tarko na rashi bayan samu.

Ya ce kamata mutane suke tsari da rage wasu abubuwa idan sun sauka gwamnati.

Sai yana da kyau a lokacin da ake kan mulki a yi kokarin kafa kai da hanyoyin samun kuɗi bayan mulki, ba wai mutum ya rinka abubuwa babu hangen nesa ba.

Sannan ya ce samun sana'a da zuba jari a wurare da dama za su taimaka. Kuma a lokacin da ake mulki mutum ya yi tsakatsan-tsan da sannin me ya kamata ya kashe me kuma zai ware saboda gaba.

An dai jima ana tu'ajjubin yadda galibin wasu masu rike da manyan mukaman siyasa ko ayukkan gwamnati kan koma hannu Rabbana, bayan da wannan dama ta wuce.

Sai dai irin wadannan bayanai na masana tattalin arziki, da wadanda suka rike irin wadannan mukamai a gwamnati, za su taka rawa wajen wayar da kan al'umma da ma 'yan siyasar kansu, domin sanin irin matakan da suka fi dacewa su dauka.