Ko dakarun ƙasa na Isra'ila za su kutsa cikin Lebanon?

Hayaƙi ya turnuƙe a wajen da Isra'ila ta jefa bam a kudancin Lebanon kamar yadda aka ɗauko hoton daga Marjaayoum da ke kudancin Lebanon a ranar 25 ga Satumba.

Asalin hoton, STR/EPA-EFE/REX/Shutterstock

    • Marubuci, Omar Hasan
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Arabic
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Hare-haren Isra'ila a Lebanon sharan fage ne a shirye-shiryen sojojin ƙasa na kutsawa Lebanon, kamar yadda babban hafsan sojon ƙasar ya bayyana.

"Za ka ji ƙugin jiragen sama na soji; hare-hare kawai muke kai wa babu ƙaƙƙautawa. Waɗannan hare-haren za su ba wa sojojin ƙasa damar kutsawa da kuma cigaba da ragargazar Hezbollah," kamar yadda Herzi Helevi ya bayyana wa sojojin.

Yadda hare-haren ke ta'azzara a cikin ƴan kwanakin nan tsakanin Isra'ila da Lebanon ya sa mutane suna waiwayen abun da ya faru a yaƙin shekarar 2006, inda sojojin ƙasa na Isra'ila suka kutsa cikin Lebanon bayan hare-hare ta sama.

Bayan harin 7 ga Oktoban 2023 da Hamas ta kai a Isra'ila, da yadda ƙungiyar Hezbollah ta ƙara ƙaimi wajen kai wa Isra'ila hari daga kudancin Lebanon, lamarin ya ƙara ƙazancewa ta kowane ɓangare.

Don haka idan Isra'ila ta yanke shawarar kutsawa cikin Lebanon, me hakan yake nufi, sannan shin za ta so ta zauna a cikin ƙasar?

Isra'ila na shirye-shiryen kutsawa cikin Lebanon ta ƙasa

Firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya sha nanata alwashin mayar da kusan mutum 60,000 da aka kwashe daga gidajensu a arewacin Isra'ila saboda hare-haren Hezbollah.

A ranar Laraba 25 ga Satumba, sai komai ya fito fili cewa Isra'ila na shirin kutsawa cikin Lebanon ta ƙasa domin sanyaya barazanar Hezbollah a kan ƴan kasarta.

Herzi Halevi ya bayyana wa sojojin ƙasar Isra'ila cewa, "yau ma za mu cigaba, ba za mu tsaya ba; za mu cigaba da kai musu hare-hare ta kowane ɓangare. Abin da muke so a zahiri yake - mu mayar da mutanenmu na arewaci zuwa gidajensu."

Ya ce sojojin "suna shirin saɗaɗawa ne cikin Lebanon, sannan su kutsa cikin ƙauyukan da Hezbollah suke da ƙarfi."

Kafin wannan, a ranar Litinin 23 ga Satumba ce aka ga ta'azzarar hare-hare mafi muni, inda jimillar waɗanda aka kashe ya kai 550 a hare-haren da Isra'ila ta ce ta kai ne a kan ƴan Hezbollah.

Sai da Ma'aikatar Lafiyar ƙasar ta ce an kashe gomman fararen hula da mata da ƙananan yara da masu aikin jinya a hare-haren.

Duk da cewa ana cigaba da hare-haren, masana da dama suna hasashen cewa Isra'ila za ta aika sojoji su kutsa ta ƙasa.

Me yunƙurin Isra'ila na kutsawa Lebanon zai haifar?

Masu aikin ceto suna duba baraguzan wani gini da Isra'ila ta ragargaza a yankin Beirut a ranar 13 ga Agustan 2006. (AFP via Getty Images)

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Yadda yaƙin ya ta'azzara a cikin ƴan kwanakin nan tsakanin Isra'ila da Lebanon ya sa mutane suna tuna abin da ya faru a yaƙin shekarar 2006.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A yaƙe-yaƙen da aka yi a baya a Lebanon, Isra'ila ta yi amfani da hanyoyi da dama domin kutsawa Lebanon ta ƙasa.

Domin fahimtar abubuwan da za su iya faruwa, zai yi kyau a waiwayi tarihin mamayar Isra'ila a Lebanon na shekarar 1982 da 2006.

  • Yaƙin 1982: Kutsawa baki ɗaya

A shekarar 1982, sojojin Isra'ila sun kutsa cikin Lebanon domin hana Falasɗinawa tsallakowa ta iyakar ƙasar, da kuma kawo ƙarshen zaman Syria da ƙarfin ikonta a Lebanon, da kuma "taimakawa a kafa gwamnati a Lebanon wadda za ta zauna lafiya tare da shiga yarjejeniyar zaman lafiya," - kamar yadda aka rubuta a shafin ayyukan jakadancin Isra'ila na intanet.

A wannan lokacin, ƙasar Falasɗinu, ƙarƙashin Yasser Arafat da ƙungiyarsa ta Palestine Liberation Organisation (PLO) ba su amincewa da Isra'ila, ita kuma Isra'ilar ba ta amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa ba.

Kutsawar ta girmama, inda ta yi amfani da dubban sojoji da ɗaruruwan tankoki da motocin yaƙi.

Sannan kuma a ɗayan gefen, sun aika sojojin sama da na ruwa, inda suka kutsa ta kowane ɓangare har suka kai babban birnin Lebanon na Beirut, suka mamaye birnin.

Sojojin Isra'ila a cikin motocin yaƙi suna wuce gidaje a cikin ƙauyen Bekaa a lokacin mamayar Lebanon ta Yunin 1982

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sojojin Isra'ila a cikin motocin yaƙi suna tafiya a cikin ƙauyen Bekaa a lokacin mamayar Lebanon ta Yunin 1982

Yaya duniya ta kalli mamayar ta 1982?

Tilas jagoran ƙungiyar PLO Yasser Arafat da kusan sojojin Syria 2,000 da suke goya masa suka ja baya daga Lebanon.

Wakilin BBC ya rubuta a wancan lokacin: "Akwai alama Mista Arafat, wanda yanzu ya nufa ƙasar Girka a jirgin ruwa zai samu wata gwamnatin ta Larabawa da za ta karɓe shi bayan zamansa a Lebanon bai yi daɗi ba."

Sai dai ita Isra'ilar ta sha suka daga ƙasashen duniya, domin a Satumban 1982, ƙungiyoyin Kirista masu ɗauke da makami sun yi wa ɗaruruwan Falasɗinawa kisan gilla a Beirut, kuma sojojin Isra'ila na kallo ba su yi komai ba.

  • Yaƙin 2006 : Kutsawar Isra'ila cikin tsanaki

Isra'ila ba ta samu nasarar kutsawa a shekarar 2006 ba sosai kamar yadda ta yi a shekarar 1982, inda dole sojojinta suka tsaya a garuruwan da ba su wuce ƴan kilomita ba a cikin Lebanon.

Mai sharhi kan harkokin siyasa na Isra'ila Yoav Stern ya bayyana wa BBC a ranar 23 ga Satumba cewa ba ya tunanin yunƙurin kutsawa na gaba ba zai iya zama kamar wanda aka yi a shekarar 1982 ba, inda ya ce a wannan karon dole a bi a hankali da tsanaki da lissafi.

Ya bayar da shawarar Isra'ila ta mamaye garuruwan kudancin Lebanon ɗaya bayan ɗaya ne, maimakon kutsawa baki ɗaya a tare. Harin zai yi kama da na 2006, amma zai fi ƙamari, domin zai kai tekun Litani.

Tekun Litani ya daɗe da zama raba-gardama ga duk wanda yake so ya samu iko a kan wasu yankunan Lebanon.

Stern ya yi hasashensa ne a kan yadda ƴan Hezbollah suka daɗe a garuruwan kudancin Lebanon, wanda zai hana Isra'ila mamaye waɗannan garuruwan cikin sauƙi.

Shi ma wani mai sharhi a kan harkokin soji, kuma janar mai ritaya, Hisham Jaber ko Isra'ila ta yi mamaya a kudancin Lebanon, ba za ta iya daɗewa a wajen ba.

"Isra'ila ta ga abun da ya faru lokacin da yi yunƙurin cigaba da zama a wuraren da ta mamaya a 2006," in ji shi, sannan ya ƙara da cewa da wahala idan akwai wasu hanyoyin da za ta iya yin mamayar daban.

Jaber ya ce yana tunanin Isra'ila za ta kutsa ne zuwa garuruwan Lebanon da ke bakin boda.

Jaber ya ƙara da cewa Isra'ila za ta ƙarar duk wani yunƙurinta na kutsawa Lebanon, sai ta koma ta cigaba da hare-harenta ta sama, da kuma kashe-kashen ɗauki ɗaya-ɗaya.

Laftanar Janar Herzi Halevi yana magana da sojoji a iyakar ƙasar Lebanon.

Asalin hoton, Israel Defense Forces

Bayanan hoto, Babban hafsan sojin Isra'ila Laftanar Janar Herzi Halevi ya bayyana wa sojoji cewa hare-haren saman sharan fage ne na kutsawa ta ƙasa.

Me kutsawar za ta haifar?

Jaber ya ce yana tunanin kutsawar Isra'ilar ba za ta wuce wasu "ƙananan garuruwa da ke kan iyakar ƙasar ba," amma ya ce akwai yiwuwar za su yi amfani da ƙarfin tsiya wajen kutsawa wajen wasu yankunan daban.

A nasa ɓangaren, shi kuma Stern ya ce yana sa ran kutsawar ta ƙasa za ta kai kudancin ƙasar wato, "yankunan da ke tsakanin Lebanon da Isra'ila da kuma tekun Litani."

Ya ce Isra'ila za ta iya faɗaɗa kutsawar har zuwa cikin Lebanon domin samun fifiko idan an zo batun yarjejeniya a gaba.

Kutsawar ta 1982 an yi ta ne ta yankuna uku, biyu an fara ne daga yankunan da ake kira Galilee Finger da Bekaa Valley a gabashin Lebanon. Na ukun kuma ta kudancin Beiruta.

Mece ce manufar kutsawar?

Dalilin da aka bayyana na kutsawar ta 1982 shi ne tseratar da garuruwan da suke arewacin Isra'ila daga hare-haren rokokin Falasɗinawa ta hanyar tursasa su su ja baya su koma can baya da misalin kilomita 40 (mil 25) daga iyakar Lebanon da Isra'ila.

Isra'ila ta ƙara da cewa tana da burin tarwatsa wasu muhimman kadarorin ƙungiyar PLO, ciki har da hedkwatarta da ke Beirut, da kuma fitar da dakarun Syria daga Lebanon.

Hara-haren Isra'ila na 1982 bai tsaya a kudancin Lebanon ba, sun kai yankunan Bakaa Valley da tsaunin Chouf da Beirut.

Hisham Jaber ya yi amannar cewa kutsawa kaɗan ba zai yi wani tasiri a ƙarshen yaƙin ba.

Amma shi Stern a ɗayan ɓangaren ya yi amannar cewa Isra'ila za ta yi ƙoƙarin kutsawa ta kowace hanya zuwa kudancin Lebanon domin ta tursasa mayaƙan Hezbollah su koma can baya zuwa tekun Litani saboda dalilai guda biyu. : "Domin hana jefa rokoki masu ƙaramin zango zuwa garuruwan Isra'ila, da kuma hana yiwuwar maimaita irin harin da aka mata na 7 ga Oktoba a arewaci."