Southampton na neman sama da fam miliyan 100 kan Dibling, Sancho na kwaɗayin komawa Dortmund

Jadon Sancho

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jadon Sancho
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Southampton za ta nemi ƙarin fiye da fam miliyan 100 kan ɗanwasa Tyler Dibling mai shekara 19 yayin da kuma Tottenham da Manchester City ke zawarcin ɗanwasan na Ingila. (Telegraph)

Newcastle na kwaɗayin sayen ɗanwasan Liverpool da Ingila Jarell Quansah, 22, inda take fatan fam miliyan 30 zai ja hankalin ƙungiyar ta cefanar da shi. (Times - subscription required)

A hannu guda kuma Newcastle ta dakatar da tattaunawa da Alexander Isak ɗanwasan da Liverpool da Arsenal ke ƙyalla ido a kan shi bayan da ɗanwasan na Sweden mai shekara 25 ya ƙi amincewa da tayin da suka yi tun farko. (Caught Offside)

Bournemouth za ta gana a wannan makon domin tattauna makomar ɗanwasan Hungary Milos Kerkez mai shekara 21 da ɗanwasan gaba na Ghana Antoine Semeno, 25 daidai lokacin da Liverpool ke zawarcinsu. (Teamtalk)

Ɗanwasan Manchester United Jadon Sancho, da a halin yanzu yake zaman aro a Chelsea, ya ƙagu ya koma Bundesliga - burinsa shi ne sake komawa Borussia Dortmund sai dai Bayern Leverkusen ma na kwaɗayin sayen ɗanwasan mai shekara 25. (Bild - in German)

Chelsea, da ke da yarjejeniyar sayen Sancho daga Manchester United, na duba yiwuwar sayen ɗanwasan a matakin dindindin kafin ta cefanar da shi nan take. (Football Insider)

Nottingham Forest na neman tsawaita kwantiragin ɗanwasan Wales mai shekara 23 Neco Williams wanda kwantiraginsa zai ƙare a Yunin 2026. (Fabrizio Romano)

Chelsea ta sake shiga sahun Real Madrid a fafutukar neman sayen ɗanwasa Dean Huijsen mai shekara 19 daga ƙungiyar Bournemouth a wannan bazara. (Sport - in Spanish)

A ranar 30 ga watan Yuni ne kwantiragin Trent Alexander-Arnold zai ƙare amma akwai yiwuwar Liverpool ta samu kuɗin sayen ɗanwasan na Ingila mai shekara 26 idan Real Madrid tana son ya buga mata gasar Fifa Club World Cup da za a soma ranar 14 ga Yuni. (Mail+ - subscription required)

Ƙungiyoyi da dama na zawarcin ɗanwasan Sunderland da Ingila a ƙungiyar ƴan ƙasa da shekara 19, Chris Rigg mai shekara 17 - har da Everton da Tottenham da West Ham gabanin kasuwar musayar ƴanwasa ta bazara. (Sky Sports)

Da alama ƙungiyoyi da dama - Liverpool da Manchester United da Newcastle da Napoli - na zawarcin ɗanwasan tsakiya na Genk Kostantinos Karetsas, 17 a bazara. (Tuttomercato - in Italian)