Mace-macen da suka fi ɗimauta 'yan Najeriya a 2023

Asalin hoton, OTHERS/FACEBOOK
- Marubuci, Umar Mikail
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- An wallafa
Kamar kowacce shekara, mutuwa ba ta bar 'yan Najeriya sun zauna kawai ba a 2023, ba tare da ta raba su da wasu shahararrun mutane ba.
An dai yi rashin 'yan siyasa, da malaman addinai, da 'yan fim, da mawaƙa, da sojoji, da masu ibada, har ma da 'yan jarida a shekarar - wadda ta zo da batutuwa iri daban-daban.
Mutuwar malamai kamar Sheikh Giro Argungun, da mawaƙi Mohbad, da sojoji sama da 36, da masu taron Mauludi a Kaduna, na kan gaba-gaba a rashe-rashen da suka ɗimauta al'ummar ƙasar.
Wannan maƙala ta yi waiwaye game da wasu daga cikin mace-macen da suka fi dugunzuma rayukan 'yan Najeriya.
Sheikh Giro Argungu

Asalin hoton, Facebook
A ranar Laraba, 6 ga watan Satumba Allah ya yi wa fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya Sheikh Abubakar Giro Argungu rasuwa.
An yi jana'izar malamin a ranar Laraba bayan rasuwarsa a babban asibitin gwamnatin tarayya da ke Birnin Kebbi a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin ƙasar.
Sheikh Giro ya rasu ya bar mata huɗu da 'ya'ya 20 da jikoki da dama.
Rasuwarsa ta girgiza 'yan Najeriya saboda shahararsa musamman wajen faɗa wa masu mulki gaskiya. Cikin waɗanda suka yi alhinin mutuwar tasa har da Shugaban Najeriya Bola Tinubu.
"Mutuwarsa babban rashi ne ga ƙasa da al'ummar Musulmai baki daya," in ji Tinubu.
Mohbad

Wata mutuwar da ta ja hankali da tafka muhawara ita ce ta mawaƙi Ilerioluwa Oladimeji Aloba, wanda aka fi sani da Mohbad a jihar Legas da ke kudancin Najeriya.
Mawaƙin ya mutu ne ranar 12 ga watan Satumba kuma aka binne shi washegari a yankin Ikorodu na Legas ɗin.
Sai dai an shafe lokaci mai tsawo mutuwarsa na jawo zazzafar muhawara musamman game da abin da ya yi sanadiyyar mutuwar tasa, inda daga baya 'yan sandan suka bayyana wata ma'aikaciyar jinya a matsayin wadda ake zargi da yi masa allurar da ta yi sanadin mutuwarsa.
Rundunr 'yan sandan Legas ta ce Mohbad ya jikkata ne yayin da suke rikici da abokinsa Primeboy, inda daga baya wani abokin nasa Ayobami Sadiq ya kira ma'aikaciyar jinyar mai suna Feyisayo Ogedengbe kuma ta yi masa allura na'u'i uku, in ji 'yan sandan.
Sunan Mohbad na cikin 'yan Najeriyar da suka fi shahara a shafukan zumunta a 2023, musamman a dandalin X - wanda aka sauya wa suna daga Twitter.
Aminu S. Bono

Asalin hoton, Social Media
Idan akwai mutuwar da ta fi girgiza masana'antar Kannywood a 2023 to ta Aminu S. Bono ce, mai shiryawa da ba da umarni a fina-finai da kuma waƙoƙi.
Shahararren mai ba da umarnin ya mutuwar fuji'a ne a ranar Litinin, 20 ga watan Nuwamba a gidansa bayan ya yanke jiki ya faɗi jim kaɗan bayan ya koma gida daga wurin aiki.
Wata majiya ta shaida wa BBC Hausa cewa ya kira maƙocinsa ya zo ya kai shi asibiti, amma rai ya yi halinsa kafin maƙocin ya isa.
An yi jana'izarsa ranar Talata da misalin ƙarfe 8:00 na safe a unguwar Ɗandago da ke ƙwaryar birnin Kano.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto abokan aikinsa ba su daina miƙa ta'aziyya da yi masa addu'a ba a fina-finansu.
Sojojin Najeriya 36 da aka kashe a jihar Neja
A ranar Alhamis, 17 ga watan Agusta rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da cewa dakarunta 36 suka mutu a jihar Neja da ke tsakiyar ƙasar sakamakon harin 'yan bindiga da kuma hatsarin jirgi.
Mutuwar jami'ai da kuma ƙananan dakarun, ita ce asara mafi girma da rundunar ta yi a 2023, wadda ta ƙunshi faɗuwar jirgin helikwaftanta na MI-171.
Jami'in yaɗa labarai na rundunar, Manjo Janar Edward Buba, ya ce jirgin ya yi hatsari ne a ranar 14 ga watan Agusta lokacin da yake ɗauke da gawar sojoji 14 da kuma bakwai da aka raunata yayin wani harin 'yan fashin daji a yankin ƙaramar hukumar Shiroro.
Gwamnan Ondo Rotimi Akeredolu

Asalin hoton, Ondo State Government
Har yanzu 'yan Najeriya - musamman 'yan jihar Ondo - da ke kudancin ƙasar ba su gama makokin mutuwar Gwamna Rotimi Akeredolu ba, wanda ya rasu ranar Laraba, 27 ga watan Disamba.
Sai dai wani abu da ba za a manta da shi ba shi ne irin dambarwar neman iko da aka shiga a gidan gwamnatin jihar bayan ya kwanta jinya.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ce gwamnan ya rasu ne a ƙasar Jamus.
Ya mutu yana da shekara 67, kuma gwamnatin jihar ta faɗa cikin wata sanarwa cewa cutar kansar mafitsara ce ta yi ajalinsa bayan ya shafe lokaci mai tsawo yana jinya.
Rasuwar tasa na zuwa ne kimanin mako biyu bayan ya rubuta wasikar tafiya jinya, inda ya miƙa ragamar mulkin jihar ga mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa.
Ghali Umar Naabba

Yayin da ake bankwana da shekarar 2023 ne kuma 'yan Najeriya, musamman Kanawa, suka yi rashin tsohon Kakakin Majalisar Wakilai Ghali Umar Naabba.
Bayanan da BBC Hausa ta samu sun tabbatar da rasuwar tsohon kakakin a wani asibiti da ke Abuja babban birnin ƙasar.
Danginsa sun tabbatar wa BBC rasuwar ne da asubahin wannan Laraba, 27 ga watan Disamba.
An yi jana'izarsa da yammacin ranar a Kofar Kudu da ke Fadar Sarkin Kano Aminu Ado Bayero.
Zaɓaɓɓen ɗan majalisa Ismaila Maihanci

Asalin hoton, Facebook/Ismail Maihanci
Rasuwar sabon ɗan Majalisar Wakilan Najeriya daga jihar Taraba, Ismaila Maihanci, ta kiɗima 'yan siyasa da mazauna jihar a watan Afrilu.
Ya rasu ranar Juma'a, 21 ga watan Afirilu makonni ƙalilan kafin a rantsar da shi a majalisa ta 10 a matsayin wakilin mazaɓar Jalingo/Yorro /Zing bayan wata gajeriyar jinya a Abuja.
Wani makusancin zaɓaɓɓen ɗan majalisar ya faɗa wa BBC cewa mutuwar ta ɗimauta iyalansa da kuma makusanta.
Ba don rasuwar tasa ba, zai kasance karon farko kenan da Isma'ila Maihanci, ɗan jam'iyyar PDP, zai je majalisar tarayya bayan ya kayar da mutumin da ke kan kujerar, Kasimu Bello Maigari na APC.
Binta Ola Katsina

Asalin hoton, Facebook
A Kannwood, ana iya cewa rashi na biyu mafi girma da aka yi shi ne na dattijuwa Binta Ola Katsina, wadda ta rasu ranar Alhamis da dare (4 ga watan Oktoba).
Ta rasu ne bayan wata gajeriyar jinya a gidanta da ke cikin birnin Katsina.
Binta Ola ta shafe tsawon shekaru tana gudanar da wasannin kwaikwayo ciki har da wasannin daɓe da na rediyo, kafin ta fara fitowa a fina-finan Kannywood.
Bayanan da BBC ta samu sun ce dattijuwar ta kammala shirye-shirye don bikin Mauludi wayewar garin Laraba, amma sai ta kamu da rashin lafiya cikin tsakiyar dare, kafin rasuwarta.
Dangin marigayiyar sun ce ba su da tabbaci kan ainihin shekarunta a duniya.
Sanata Bello Maitama

Asalin hoton, PM News
Har wa yau a fagen siyasa, a ranar Juma'a, 13 ga watan Oktoba Allah ya yi wa Sardaunan Dutse Sanata Bello Maitama Yusuf rasuwa a jihar Kano.
Marigayin ƙwararran lauya ne wanda ya yi minista a jamhuriya ta biyu kuma ya zama sanata a jamhuriya ta huɗu.
Ya rasu yana da shekara 76 bayan gajeriyar rashin lafiya. Jaridar Aminiya ta ce ya bar mata biyu da 'ƴa'ƴa 10 - maza biyar, mata biyar.
Oladipo Diya

Asalin hoton, Family
A ɓangaren sojin Najeriya, a ranar 26 ga watan Maris ne aka yi rashin tsohon shugaban rundunar sojin Najeriya a zamanin mulkin Janar Sani Abacha, Laftanar Janar Oladipo Oyeyinka Diya.
Janar Diya, wanda shi ne mutum na biyu mafi girman muƙami a zamanin mulkin sani Abacha, yana gab da cika shekara 79 da haihuwa a cikin watan Afrilu lokacin da ya rasu.
An haifi Janar Diya a garin Odogbolu na jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya, kuma yana daga cikin dakarun da suka yi yaƙin basasar ƙaras kafin ya zama babban hafsan sojin ƙasa a shekarar 1993.
Ya kuma riƙe muƙamin mataimakin shugaban majalisar mulkin sojin ƙasar a 1994.
Shahararren ɗan wasan kwaikwayo Samanja

Asalin hoton, Social Media
Shahararren ɗan wasan kwaikwayon nan Usman Baba Pategi, wanda aka fi sani da Samanja Mazan Fama, ya rasu yana da shekara 81, kamar yadda iyalansa suka faɗa wa BBC.
Tsohon ɗan wasan ya rasu ne ranar Lahadi, 13 a garin Kaduna bayan ya sha fama da jinya.
Ɗan marigayin mai suna Mohammed Usman ya faɗa wa jaridar Daily Trust cewa mahaifinsa ya bar mata biyu da 'ya'ya 12.
Samanja ya shahara ne a fina-finan gidan talabijin na NTA a shekarun 1980 zuwa 1990, inda ya taka rawa a matsayin soja.
'Yar jarida Aisha Mustapha

Asalin hoton, NTA
A ɓangaren abokan aiki 'yan jarida ma an yi rashin Aisha Bello Mustapha, shahararriyar mai gabatar da labarai a kafar talabijin ta NTA mallakar gwamnatin Najeriya.
Aisha haifaffiyar birnin Yola ce a arewacin ƙasar kuma sananniyar fuska ga miliyoyin mutane a Najeriya bayan ta shafe shekaru tana gabatar da labarai.
Ta yi ritaya a shekarar 2022.
An yi jana'izarta ranar Litinin, 11 ga watan Disamba a Abuja.










