Haaland ya zama na farko da ya ci 10 a Premier da fara wasa shida a bana

Erling Haaland

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Aston Villa da Manchester City sun raba maki a wasan mako na shida a gasar Premier da suka fafata a Villa Park.

Manchester City ta fara cin kwallo minti biyar da komawa zagaye na biyu ta hannun Erling Haaland.

Kwallo na 10 da ya zura a raga a wasa shida da fara kakar nan, shi ne kan gaba a yawan cin kwallaye a Premieer a bana.

Wanda yake da tarihin cin 10 a wasan Premier a wasa shida da fara gasar shi ne Mick Qumn na Coventry a 1992.

Saura minti 16 su tashi daga wasan ne Villa ta farke ta hannun Leon Bailey, hakan ya sa suka raba maki a tsakaninsu.

City ta yi wasa 21 a waje ba tare da an doke ta ba kawo yanzu, ta ci karawa 15 da canjaras shida, wadda ta yi canjaras na biyu a bana da cin wasa hudu.

Aston Villa ta kawo kartshen wasa uku ba ta yi nasara ba, wadda ta ci daya tun fara kakar bana.

Ranar 10 ga watan Satumba, Villa za ta ziyarci Leicester City domin buga wasan mako na bakwai a babbar gasar tamaula ta Ingila ta bana.

Manchester City kuwa za ta ziyarci Sevilla, domin buga wasan farko a cikin rukuni a Champions League ranar 6 ga watan Satumba.

Kungiyoyin da Haaland ya ci a Premier a bana:

 

Premier League Lahadi 7 ga watan Agusta            

  • Wasa tsakanin West Ham 0 – 2 Man City – Haaland ne ya ci biyu

Premier League Lahadi 21 ga watan Agusta          

  • Wasan Newcastle 3 – 3 Man City – Haaland ya ci daya    

Premier League Asabar 27 ga watan Agusta         

  • Wasan Man City 4 – 2 Crystal Palace – Haaland ya ci uku rigis       

Premier League Laraba 31 ga watan Agusta         

  • Wasan Man City 6 – 0 Nottingham Forest - Haaland ya ci uku      

Premier League Asabar 3 ga watan Satumba       

  • Wasan Aston Villa 1 – 1 Man City – Haaland ya ci daya