United za ta sayar da Greenwood, Aston Villa na zawarcin Gallagher

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United na son sayar da ɗan wasan gaban Ingila Mason Greenwood, mai shekara 22, wanda aka alaƙanta shi da Napoli da Juventus da kuma Atletico Madrid bayan ya taka rawar gani a zaman aro da ya yi a Getafe. (Talksport)
Borussia Dortmund kuma ta shiga jerin ƙungiyoyin da ke fafatukar ɗaukar Greenwood. (Mirror)
Aston Villa na sha'awar sayen dan wasan tsakiya na Chelsea da Ingila Conor Gallagher, mai shekara 24, kuma zata iya amfani da ɗan wasan Colombia Jhon Duran, mai shekara 20, a wani ɓangare na yarjejeniyar. (Telegraph)
Dan wasan gaban Brentford da Ingila Ivan Toney, mai shekara 28, na ɗaya daga cikin ƴan wasn gaba biyu da Tottenham ke zawarci a bazara (Football Insider)
Kocin Ipswich Kieran McKenna ne kan gaba a cikin ƴan takarar wanda zai maye gurbin Mauricio Pochettino a Chelsea, wanda har yanzu ba a gama tantance makomarsa ba. (Guardian)
Everton ta shirya karbar tayi kan ɗan wasan baya Jarrad Branthwaite, mai shekara 21, yayin da Manchester United da Manchester City da Tottenham ke sha'awar ɗan wasan. (Mail)
Kocin Brighton mai barin gado Roberto de Zerbi kan gaba cikin waɗanda Bayern Munich ke zawarci don maye gurbin Thomas Tuchel. (Bild)
Tuni dai Bayern da De Zerbi suka yanke shawarar ƙin aiki tare, a cewar daraktan kulob ɗin Max Eberl. (Fabrizio Romano)
Kocin Barcelona Xavi ya ce har yanzu yana samun goyon bayan ƙungiyar duk da rahotannin da ke cewa za a kore shi. ((Times).
Newcastle da Everton da Crystal Palace suna sha'awar sayen ɗan wasan tsakiyar Ingila Kasey McAteer, mai shekara 22, wanda ke shirin shiga shekarar ƙarshe ta kwantiraginsa da Leicester City. (Football Insider )










