Waiwaye: Naɗin Firaiminista, rashin lafiya da rasuwar Sarauniya da naɗin sabon Sarki

Asalin hoton, PA Media
A cikin makon da muke bankwana da shi ne abubuwa da dama waɗanda tarihi ba zai taba mantawa da su ba musamman a Burtaniya da ma duniya baki ɗaya, suka faru.
Waɗannan abubuwa za su ci gaba da kasancewa a zukatan al'umar duniya da dama, zuwa wasu shekaru masu yawa da ke tafe.
Naɗin sabuwar Firaiminista

Asalin hoton, others
A ranar Litinin ne dai aka sanar da Liz Truss a matsayin wacce ta lashe zaɓen takarar shugabancin jam'iyyar masu ra'ayin riƙau ta Conservatives.
A ranar Talata kuma aka rantsar da ita a matsayin sabuwar Firaiministar Birtaniya abin da ya sa ta zamanto mace ta uku da ta zama Firaiministar Birtaniya bayan da ta maye gurbin Boris Johnson wanda ya yi murabus bayan shan matsin lamba.
Liz Truss ta kasance Firaminista ta 16 da Sarauniyar ta rantsar, Sarauniya ta soma naɗa firaiministoci ne a 1955 lokacin da ta naɗa Anthony Eden, zuwa 2022 lokacin Liz Truss.
Likitoci sun nuna damuwa game da lafiyar Sarauniyar Ingila

Asalin hoton, Getty Images
Kwana biyu bayan rantsar da sabuwar Firaministar, ranar Alhamis kwatsam! sai likitoci suka nuna damuwa game da lafiyar Sarauniyar, inda suka garzaya fadarta da ke Bolmoral a Scotland domin kula da lafiyarta
A wata sanarwar da fadar ta fitar ta ce "Likitocin sarauniyar sun damu kan halin lafiyarta bayan da suka duba ta da safiyar ranar Alhamis, sun kuma ba da shawara cewa likitoci za su ci gaba da kula da ita''.
Daga baya kuma fadar ta fitar da wata sanarwar tana mai cewa "Sarauniyar tana samun sauƙi''.
Yarima Charles da jikanta Yarima William da sauran danginta duk sun hallara a fadar Balmoral domin kasancewa da ita.
Sanarwar rasuwar sarauniya daga Fadar Buckingham

A ranar Alhamis din ne kuma da yamma Fadar Buckingham ta bayyana rasuwar Sarauniyar, a wata sanarwa ta fadar ta fitar ta ce sarauniyar ta mutu 'salin-alin' a fadarta da ke Bolmoral
Sarauniyar ta rasu tana da shekara 96 a duniya, bayan da shafe shekarar 70 tana kan karagar mulkin Burtaniya.
A wata sanarwa, mai Martaba sabon Sarki Charles lll ya ce "Mutuwar mahaifiyata abar kaunata mai martaba Sarauniya, lokaci ne na matukar bakin ciki a gare ni da dukkan iyalaina, muna matukar jimamin rasuwar Basarakiya abar bege kuma mahaifiyata abar kaunata, na sani cewa rashinta zai yi matukar yi wa 'yan kasar nan da Commonwealth zafi''.
Ta'aziyyar shugabannnin kasashen duniya da ajiye furanni a sassa daban-daban na duniya

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A saƙonsa na jimami da alhinin rasuwar Sarauniyar Ingila Elizabeth, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya ji baƙin ciki matuƙa da samun labarin mutuwar Sarauniyar
Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai taimaka masa kan yaɗa labarai Malam Garba Shehu ya fitar jiya Alhamis.
"Ni da iyalaina da al'ummar Najeriya sama da miliyan 200 duk mun ji takaici sosai na rasuwar Sarauniya Elizabeth, wanda hakan ya kawo ƙarshen mulkinta na tsawon shekara 70 mai cike da ban sha'awa da babu irin sa'', in ji Shugaba Buhari.
Shugaba Joe Biden na Amurka ya bayyana marigayiyar a matsayin mai kishin ƙasa da tsayuwar daka.
Shugaba Macron na Faransa ya ce zai tuna da ita a matsayin babbar ƙawa kuma aminiyar Faransa.
Shi ma Shugaban Jamus ya bayyana Sarauniyar a matsayin wadda ta ba da gudummowa a wannan ƙarni.
Shugaba Vladmir Putin na Rasha ya ce ta kasance mai mutunta al'ummarta.
Shi kuwa Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce mutuwar Sarauniya Elizabeth gagarumin rashi ne ga duniya baki ɗaya
Haka kuma an yi ta ajiye furanni a wurare daban-daban a fadin duniya

Asalin hoton, EPA/Shutterstock

Asalin hoton, Reuters
Charles III ya zama sabon Sarkin Ingila

Asalin hoton, others
Rasuwar Sarauniyar Ingila ke da wuya, sai mulkin ya koma kan ɗanta magajinta Charles, tsohon Yariman Wales, ba tare da wani bikin naɗin sarauta ba.
Horon da ya rika samu a matsayin magaji, wanda ya shafe tsawon shekaru 70, ya sanya shi ya zama sabon sarki da ya dade yana shiri, kuma mafi tsufa da ya taba hawa karagar mulki.
Sarkin, mai shekara 73 a duniya, ya shafe tsawon lokacin da mahaifiyarsa ta dauka tana mulki yana kallon yadda aka rika samun shugabannin kasashen duniya, ciki har da Firaiminista 15 na Birtaniya da shugabannin Amurka 14.
An tabbatar da naɗin Sarki Charles lll a hukumance
A ranar Asabar kuma a hukumance aka sanar da naɗin sarki Charles lll a wani biki da aka gudanar a birnin Landan , Yarima William da Firaiminista Liz Truss da kuma Shugaban Cocin Ingila Justin Welby na tsaye suna kallo yayin da ake sa hannu kan sanarwar.
Bayan an kammala sa hannun ne kuma aka karanta sanarwar naɗa Charles lll sabon sarki a hukumance a London da Edinburgh da Cardiff da kuma Belfast inda kuma za a soma harba bindigogi a Hyde Park da kuma hasumiyar birnin Landan da zarar an naɗa sabon sarkin.

Asalin hoton, PA Media

Asalin hoton, PA Media











