Abin da ya kamata ku yi cikin watan Ramadan

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa
A ranar Alhamis ne al’ummar Musulmi suka tashi da azumin watan Ramadana a Najeriya da ma ƙasashe daban-daban na duniya.
Wata ne da Musulmai kan zage damtse wurin ibada da kuma kauce wa abubuwan da aka haramta.
Azumi c2lnvypww0zoaya ne daga cikin ginshiƙan addinin Musulunci guda biyar – wato shahada, salloli biyar, azumin Ramadana, zakka, da kuma aikin hajji.
Shin mene ne abubuwan da ake son musulmi ya rinƙa yi a lokacin azumin Ramadana?
Sheikh Nuru Khalid, fitaccen malamin addinin Musulunci ne a Abuja, ya lissafa su kamar haka:
- Inganta Imani
- Faɗaɗa taƙ'wa
- Kiyaye lokaci wurin al’amuran rayuwa da addini.
- Kiyaye harshe: Sheikh Nuru Khalid ya ce wanda bai kiyaye harshensa ba ba shi da azumi, kamar yadda ya zo a cikin hadisi “Wanda bai bar shaidar zur da aiki da ita ba, Allah ba Ya buƙatar ya bar cin abinci da abin sha.”
- Yawan kyauta da taimako
- Ƙoƙarin yin aiki da Alƙur’ani.

Asalin hoton, Getty Images





