Za a kara tsakanin Lewandowski da Haaland a Nou Camp

Lewandowski da Haaland

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Robert Lewandowski da Erling Haaland za su kara ranar Laraba a Nou Camp a wasan tara kudi don taimakawa Juan Carlos Unzue.

Barcelona da Manchester City za su fafata domin taimakawa Carlos Unzuel tsohon dan wasan Barcelona, wanda ya kamu da cutar sanyin lakar jiki.

Haka kuma kudin kallon wasan da za a samu, za a yi amfani da shi wajen taimakawa masu fama da larurar da kuma yin bincike.

'Yan wasan biyu za su hadu a karon farko a lokacin da Lewandowski ke Barcelona, shi kuwa Haaland yana Manchester City.

Dukkansu 'yan wasan na taka rawar gani a kakar bana a sabbin kungiyoyinsu, bayan da Lewandowski ya ci kwallo uku a Barca, Haaland ya zura hudu a City.

Masu cin kwallayen sun fuskanci juna sau bakwai a baya a lokacin da Lewandowski ke Bayern Munich da Haaland a Borussia Dortmund.

Dan wasan tawagar Poland ya ci kwallo tara a haduwar, yayin da Haaland ya zura biyar a raga.

Lewandoski da Haaaland sun kafa tarhin bajinta a gasar Jamus, kafin kowannensu ya koma sabuwar kungiya a bana don gwada wata sa'a.

Dan wasan da ya koma taka leda Barca ya kafa tarhin cin kwallo 41 a wasa 29, ya kuma zura kwallo 43 a shekara daya.

Hakan ya sa ya doke tarihi biyu a bajinta da Gerd Müller ya kafa a baya can.

A kungiyar Borussia Dortmund, Haaland kan ci kwallo a kalla duk minti na 87, shi ne matashin da ya zura 20 a raga a Champions League.

Shi kuwa Lewandowski shi ne mai karan cin shekaru da ya zura kwallo 100 a babbar gasar tamaula ta Jamus.