Mai wasa da wuta da ɗalibai masu zana jarabawa cikin hotunan Afrika na mako

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Wasu daga cikin kayatattun hotunan Afirka na mako;

Mai wasa da wuta ya dauki hankalin mutane, a gundumar Oworonshoki a Lagos,Najeriya, 24 Satumba, 2024

Asalin hoton, Emmanuel Adegboye / EPA

Bayanan hoto, Mai wasa da wuta ya ɗauki hankalin mutane, lokacin bikin kalankuwar zane-zane a ranar Litinin a gundumar Oworonshoki a jihar Lagos cibiyar kasuwancin Najeriya.
Matasan ma'aurata 'yan kabilar Amazigh su na jiran layi ya zo kan su domin yi musu rijistar aure, 21 Satumba 2024.

Asalin hoton, Jalal Morchidi / EPA

Bayanan hoto, Amarya da angonta, sun shirya cikin kyawawan tufafi lokacin bikin aurensu a tsaunin Amazigh da ke kasar Morocco, bayan an yi musu baiko su na jiran ayi rijistar auren na su a ranar Asabar.
Matashiya 'yar Tunusia ta rufe fuskarta da kyalle, sanye da gilashi ta daga tutar kasarta. 22 Satumba, 2024

Asalin hoton, Ben Ibrahim / Getty

Bayanan hoto, A ranar Lahadi ake sa ran 'yan Tunisia za su fita zanga-zangar kin amincewa da sauya dokokin zabe, wanda zai kawo karshen kotunan da ke shari'ar korafe-korafen zabe idan an samu turjiyar amincewa da sakamakon zabe daga 'yan adawa.
Masu zanga-zanga sun fara boren kwanaki uku domin adawa da hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba, ranar 21 Satumba 2024.

Asalin hoton, Francis Kokoroko / Reuters

Bayanan hoto, Masu zanga-zanga sun cika titunann birnin Accra na kasar Ghana, sun fusata kan hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba a kasar.
Matasa na kallon wasan kwallon kafa tsakanin kungiyoyi biyu daga Toubab Dialaw, kusa da birnin, Dakar na kasar Senegal, ranar 25 Satumba 25, 2024

Asalin hoton, Zohra Bensemra / Reuters

Bayanan hoto, Matasa na kallon wasan kwallon kafa tsakanin kungiyoyi biyu daga Toubab Dialaw, kusa da birnin Dakar, na ƙasar Senegal.
A ranar Lahadi, dalibai mata sun dukufa rubuta jarabawa a makarantar Oman, da ke birnin Alkhahira na masar....  ranar 22 September 2024.

Asalin hoton, Mohamed Abd El Ghany / Reuters

Bayanan hoto, A ranar Lahadi, ɗalibai mata sun dukufa rubuta jarabawa a makarantar Oman, da ke birnin Alkhahira na masar....
mai wasa ne ya ke nishadantar da dalibai a wata makaranta da ke babban birnin kasar Algiers, ranar 22 Satumba 2024

Asalin hoton, Billel Bensalem / AFP

Bayanan hoto, ...A dai wannan ranar amma a kasar Algeria, an buɗe makarantu domin fara sabon zangon karatu, anan wani mai wasa ne ya ke nishadantar da dalibai a wata makaranta da ke babban birnin kasar Algiers.
Mawakan gargajiya na kungiyar Isicathamiya, su na rera waka da harshen Zulu, a bikin kalankuwar mawaka a birnin Durban na Afirka ta Kudu, ranar 21, Satumba 2024.

Asalin hoton, Rajesh Jantilal / AFP

Bayanan hoto, Mawakan gargajiya na kungiyar Isicathamiya, su na rera waka da harshen Zulu, a bikin kalankuwar mawaka a birnin Durban na Afirka ta Kudu.
Makadin badujala na kida a wata majami'a da ke kan titin Kamituga a gabashin Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo, a ranar Juma'a. Ranar 20 Satumba 2024.

Asalin hoton, Glody Murhabazi / AFP

Bayanan hoto, Makaɗin badujala na kiɗa a wata majami'a da ke kan titin Kamituga a gabashin Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo, a ranar Juma'a.
'Yan Kenya na kwashe shara a ranar gangamin tsaftar muhalli, ranar 20 Satumba 2024.

Asalin hoton, Gerald Anderson / Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Juma'a mutane sun shiga gangamin Ranar Tsafta ta duniya, ciki har da share birnin Nairobi na ƙasar Kenya da kwashe shara a birnin Nakuru.
Sojoji sun yi Fareti a ranar tunawa da 'yan mazan jiya a Maputo, a ranar 25 Satumba 2024

Asalin hoton, Alfredo Zuniga / AFP

Bayanan hoto, Jagoran makaɗan badujala na soji, ya tsaya tsakiyar sojoji a ranar tunawa da 'yan mazan jiya a Mozambique.
Kungiyar agaji ta Kenya Red Cross, ta jera akwatin gawawwakin daliban a wurin jana'izarsu ranar 26 ga Satumba 2024

Asalin hoton, Monicah Mwangi / Reuters

Bayanan hoto, Aranar Alhamis aka gudanar da addu'o'i, ga daliban nan 21 da gobara ta hallaka a makarntar kwana da ke Kenya, a farkon watan nan. Cikin wadanda suka je har iyaye da 'yan uwan daliban nan.
Ya yin da dusar kankara ta mamaye filin Warden,a yankin Free State a Afirka ta Kudu ranar 21, Satumba 2024.

Asalin hoton, Wikus de Wet / AFP

Bayanan hoto, An samu zubar dusar kankara a yankin Free state da ke Afirka ta Kudu, zubar kankarar ta janyo tsaikon gudanar da harkokin yau da kullum, amma wasu mutane sun yi amfani da damar domin yin mutum-mutumin dusar kankarar.
An dauki hoton tashar motar bus ta Obalende ta sama, ranar 24 Satumba 2024

Asalin hoton, Olympia de Maismont / AFP

Bayanan hoto, Tashar motar Bas kenan a Obalende da ke birnin Lagos din Najeriya, motoci jere reras suna jiran fasinjoji a ranar Talata.