An cire wannan labarin: 'Mun bibiyi rayuwar yara uku da suka tsira a yaƙin Gaza. Ga abin da muka gano'

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

An sake wallafawa ranar 21 ga watan Fabarairu:

Tun bayan fitar da wannan rahoton na musamman, BBC ta gane cewa mahaifin yaron da ya jagoranci rahoton, mai suna Abdullah, ya yi aiki a matsayin ƙaramin minista a gwamnatin da Hamas ta jagoranta a Gaza.

Rahoton ya fito da labarai masu muhimmanci da suka kamata a fito da su – labaran halin da yara ke ciki a Gaza.

A game da ayar tambayar da ake ci gaba da ɗorawa kan wannan rahoto, BBC ta wallafa bayani na baya-bayan nan a shafinmu na yin gyara da kuma fayyacewa, inda muka yi bayani kan cewa ba za a samu rahoton a shafinmu na iPlayer ba yayin da muke ci gaba da bincikenmu tare da kamfanin da ya naɗo rahoton, saboda haka ne muka cire labarin.