Shiga gida sai da kwale-kwale saboda ambaliya a Kogi

Mutane tsaye a hawa na sama na gidan  Mohammed Sani Gambo
    • Marubuci, Mayeni Jones
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • An wallafa

Najeriya na fuskantar ambaliyar ruwa mafi muni cikin shekara 10, matsalar da ta tilasta wa mutane miliyan 1.4 barin muhallansu. Garin Lokoja da ke yankin tsakiyar Najeriya na daga cikin wuraren da matsalar ta fi ƙamari - sai dai al'umma a wannan yankin na yin iyakar bakin ƙoƙarinsu wajen rage illar matsalar.

A tsawon mako uku, Mohammed Sani Gambo bai iya shiga gidansa sai ta hanyar kwale-kwale.

Masuncin, wanda ke da ƴaƴa 11 na daga cikin waɗanda suka ci sa'a a unguwarsu ta Gadumu. Kasancewar gidansa mai hawa biyu ne, ya samu damar kwashe iyalansa da kayansa zuwa hawa na biyu domin tsere wa ruwa.

"Lokacin da ruwan ya fara ambaliya ba mu zaci zai yi muni ba", in ji shi, "amma bayan kwana ɗaya sai ga shi ko ina ya cika da ruwa."

Mohammed Sani Gambo tsaye a kan kwale-kwale a hanyar shiga gidansa

Yanzu su 27 ne suke rayuwa a ɗakuna biyu da ke can saman gidan nasa. Suna gwamutse da kwanuka da tukwane da katifu, da duk abin da za su iya tseratarwa daga ruwan.

Ya kara da cewa "Yanzu ba iyalina ne kaɗai suke rayuwa a nan ba, na bai wa wasu makwaftana waɗanda ba su da wurin zuwa, wurin kwana. Ba zan iya barin su a tagayyare ba, shi ya sa na ce su shigo ciki."

Ya kwashe sama da shekara goma yana rayuwa a wannan unguwa, saboda haka ya saba da ambaliyar ruwa, to amma ta wannan shekarar ta sha banban.

Ya ce "Yawan ruwan da ya yi ambaliya a wannan shekarar ya zarta na shekarun baya. Wannan karo ya fi yawa. Kuma saboda yawan ruwan mun rinƙa cin karo da macizai da ɓeraye."

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Jihar Kogi ta saba da ambaliyar ruwa

Lokoja, babban birnin jihar yana a mahaɗar koguna biyu mafiya girma a faɗin yammacin Afirka, wato kogin Kwara da na Benuwe. Kogunan sukan cika su tumbatsa a lokutan damina, abin da ke haifar da ambaliyar ruwa.

Hukumomin jihar na cewa rashin bin ƙa'idojin gini na daga cikin matsalolin da ke haifar da ambaliyar.

Sakataren ƙungiyar Red Cross a jihar Kogi, Abdullahi Abubakar ya ce "Ɗaya daga cikin abubuwan da ke sa abin yana yin muni shi ne mutane suna yin gini a kan hanyar ruwa."

"Da zarar ruwan ya janye, sai mutane su sake komawa su tare hanyar."

Ya ce suna ta bai wa gwamnati shawarar ta sake wa al'umma matsuguni ɗungurungum, yadda za su bar kan hanyoyin ruwa.

Sani Gambo ya ce shi da iyalansa za su so su bar unguwar, to sai dai ba su da wurin da za su koma.

"Lokacin da na gina gidan nan nawa komai na tafiya daidai, ina samun amfanin gona sosai, amma yanzu abubuwa sun ja baya, kuɗin shiga sun yi karanci, ba zan iya sake wani gidan ba. Ko sayen fili ma yanzu abu ne mai wahala."

Makwafciyarsa ma Lamine Ibrahim Yusuf tana son sauya unguwa amma ba ta da halin yin hakan. Ta rasa mijinta bayan da cutar korona ta yi ajalinsa, yanzu ta ce ba ta da halin gyara gidanta balle ma ta gina wani gidan na daban.

Lamine Y Ibrahim

Tattalin arziƙin Najeriya na hsa wahala a shekarar da ta gabata.

Duk da cewar a baya Najeriya ta kasance ƙasar da ta fi kowace fitar da ɗanyen mai daga nahiyar Afirka, amma yawan man da take fitarwa ya yi ragu sanadiyyar ayyukan masu fasa bututu da kuma satan mai a yankin Niger Delta.

Hauhawar farashin kayan masarufi ma ya yi tashin da bai taɓa yi ba, mutane na wahala kafin samun abubuwan biyan buƙatu. Wannan ambaliyar ruwa za ta ƙara jefa mutane ne cikin wahala.

Shirin samar da abinci na majalisar ɗinkin duniya a watan jiya, ya ce Najeriya na daga cikin ƙasashe shidda da ke cikin haɗarin faɗawa ƙangin yunwa.

Masana sun ce abubuwan da ke haddasa ambaliyar ruwa a Najeriya suna da sarƙaƙiya, kuma sun haɗa har da rashin kula, da zaizayar ƙasa, to amma sauyin yanayi na ƙara dagula matsalar.

Yayin da ake ci gaba da hasashen samun ƙarin ruwan sama, jihar Kogi za ta ci gaba da kasancewa cikin fargaba, kuma babu sa ran cewar ambaliyar ruwan za ta sassauta.