Yadda jiragen yakin Najeriya suka kai hari maboyar shugaban kungiyar ISWAP

.

Asalin hoton, NIGERIAN AIRFORCE

An wallafa

Rundunar sojin saman Najeriya ta tabbatar da kai hare-hare a maboyar shugaban kungiyar ISWAP da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Kakakin rundunar sojin saman, ya shaida wa BBC Hausa cewa jami'ansu da hadin gwiwar wasu jami'an tsaro, sun kai hari dajin Sambisa inda shugaban na ISWAP, Fiya Ba Yuram da sauran 'yan kungiyar suke samun mafaka.

Air Commodore Edward Gabkwet ya ce sun kuma kai hari a yankin Tumbuns na Jihar Borno, da ke gabar Tafkin Chadi.

A cewarsa, sun kai harin ne bayan samun labari cewa 'yan ta'adda suna haduwa a yankin inda ya kara da cewa sun kashe da dama daga cikinsu a hare-haren, wadanda aka kai a karshen mako.

Sai dai ya ce kawo yanzu ba su da cikakkun alkaluma kan adadin 'yan ta'addan da suka kashe yana mai cewa "haka kuma ba mu da tabbaci ko mun kashe Fiya Ba Yuram."

"Bayan samun bayanan sirri, an tura jiragen sama a Dajin Sambisa inda aka yi amannar cewa gawutaccen dan ta'addan nan, Fiya Ba Yuram yake buya.

Fiya Ba Yuram shi ne shugaban ISWAP a yanzu a Dajin Sambisa bayan mutuwar Abubakar Shekau.

Yuram na hannun-daman Shekau ne har lokacin da aka kashe shi, kuma bayan mutuwarsa ce ya sauya sheka zuwa kungiyar ISWAP," in ji Air Commodore Edward Gabkwet

Ya kara da cewa sun kai harin Tunbuns ne bayan sun samu bayanai da ke cewa 'yan ta'adda suka yin atisaye da samun horo kan yadda za su kaddamar da hare-hare.

"Bayan kai harin ne wurin ya kaure da ihu na 'yan ta'addan da suka rage wadanda suka yi yunkurin buya a karkashin wasu bishiyoyi da ke kusa, wadanda su ma jiragen sama suka yi musu luguden wuta," in ji shi.