Arteta ya tafi da Arsenal Dubai

Asalin hoton, ARSENAL
Bayan da ƙungiyar Newcastle ta yi waje da Arsenal a wasan kusa da na ƙarshe a gasar cin kofin Carabao (EFL), a ranar Laraba, kociyan Gunners ɗin ya ɗebi 'yanwasan ya nufi Dubai da su inda za su je su yi atisaye cikin yanayi mai ɗumi su huta da sanyi.
A wani saƙo da ƙungiyar ta sanya a shafinta na intanet, ta tabbatar da cewa tawagar za ta yi bulaguron zuwa Dubai inda take sa ran dawowa kafin wasansu a gidan Leicester, kwana tara nan gaba.
Ƙungiyar ta sanya hotunan tawagar 'yanwasan na Arsenal a lokacin da suke hawa jirgin sama don tafiya atisayen Dubai.
A hoton an ga Bukayo Saka da kuma ɗanbaya Ben White, waɗanda dukkanninsu suna jinya ne su ma za su je Dubai ɗin tare da tawagar.

Asalin hoton, ARSENAL
Newcastle ta fitar da Arsenal ɗin daga gasar kofin na Carabao da ci 4-0, a karawa biyu - gida da waje, inda ta kammala doke su a filinsu na St James' Park, ranar Larabar.
Tun a karawar farko daman Newcastle ɗin ta doke Arsenal a Emirate da ci 2-0.
Da wannan nasara Newcastle za ta kara da Liverpool ko Tottenham - ƙungiyoyi biyun da za su kece raini a san gwani a tsakaninsu, ranar Alhamis ɗin nan.
Rabon da Newcastle ta ci wani babban kofi tun 1969 a gasar Inter-Cities Fairs Cup.
Haka kuma Newcastle ɗin za ta so ta ci gaba da wannan nasara a gasar bayan da ta sha kashi a hannun Manchester City a gasar kofin na EFL shekara biyu baya, kasancewar rabonta da cin wani kofi na gida tun kofin FA da ta ci a 1955.









