Man Utd na neman Nick Pope, Arsenal na bibiyar Eberechi Eze

Nick Pope

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Golan Ingila mai shekara 33 Nick Pope zai iya komawa Manchester United idan Newcastle ta yi nasarar ɗauko golan Southampton mai shekara 27, Aaron Ramsdale. (Talksport)

Newcastle ta cimma matsaya da Southampton a kan ɗaukar Ramsdale a matsayin aro tare da zaɓin mallakarsa a ƙarshen kakar wasan nan. (Athletic - subscription required)

Manchester United ta kuma shiga zawarcin golan PSG kuma ɗan asalin Italiya, Gianluigi Donnarumma, amma tana kaucewa shiga gogayyar ciniki da Chelsea da kuma Manchester City a kan ɗanwasan mai shekara 26. (Sun)

Arsenal na ci gaba da zawarcin ɗanwasan tsakiyar Ingila Eberechi Eze, mai shekara 27, amma ba ta shirya biyan £60m kan ɗanwasan ba domin haka tana jira har sai Crystal Palace ta karya farashinsa. (Athletic - subscription required)

Manchester City ta ƙi amincewa da tayin £25m da Nottingham Forest ta gabatar mata kan ɗanwasan tsakiyar Ingila mai shekara 22, James McAtee. (Sky Sports)

PSG ta ƙara ƙaimi domin kammala cinikin ɗanwasan bayan Bournemouth ɗan asalin mai shekara 22, Illia Zabarnyi. (Fabrizio Romano)

Borussia Dortmund na bibiyar ɗanwasan tsakiyar Arsenal mai shekara 30, Leandro Trossard, ama akwai wasu ƙungiyoyin gasar Firimiya biyu da ke zawarcin ɗanwasan na Belgium. (Sky Sports Germany)

Lyon na zawarcin ɗanwasan tsakiyar Ingila mai shekara 22, Tyler Morton, kuma tuni ta tuntuɓi Liverpool a kai. (Times)

Everton ta mayar da hankali ga neman anwasan tsakiyar Juventus da Brazil mai shekara 27, Douglas Luiz. (GiveMeSport)

Manchester City ta sanar da golan Jamus mai shekara 32, Stefan Ortega, cewa ba ta buƙatarsa a ƙungiyar bayan ta ɗauko James Trafford daga Burnley. (Fabrizio Romano)