Abin da muka sani game da jibge jami'an tsaro a fadar sarkin Kano Sanusi

Jami'an tsaro na 'yansanda da aka jibge a fadar masarautar Kano da ke arewacin Najeriya
Bayanan hoto, Wakilin BBC ya ce jami'an tsaron da aka jibge a masarautar Kanon sun hana kowa shiga da fita ta babbar ƙofar gidan sarki a ranar Juma'a ciki har da hakimai
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Da safiyar ranar Juma'a ne mazauna birnin Kano suka wayi gari da tarin jami'an tsaro a fadar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da ke Ƙofar Kudu.

Hakan ya kawo cikas ga zirga-zirga da shige da fice a cikin fadar mai ɗimbin tarihi da kewayenta, inda a nan ne Sarki Sanusi II ke da gudanar da al'amuran mulki.

"Tun da aka fara wannan rikici na masaruta na daɗe ban ga jami'an tsaro masu yawan haka da suka yi kane-kane a fadar sarki ba," a cewar wakilin sashen BBC Pidgin Abubukar Machiɗo.

Baya ga jami'an tsaron ɗauke da makamai, ana iya ganin motocin tarwatsa masu zanga-zanga waɗanda aka jibge a fadar.

Me fadar sarkin ta shirya yi kuma me ta iya yi zuwa yanzu?

Bayanai sun nuna cewa a ranar Juma'a ne aka tsara Sarki Sanusi II zai yi wa ɗaya daga cikin masu riƙe da sarauta mafi girma a masarautar, Wamban Kano Mannir Sanusi, rakiya zuwa Bichi domin kama aiki a matsayin hakimin ƙaramar hukumar.

Bichi na ɗaya daga cikin sababbin masarautu da gwamnatin Abdullahi Ganduje ta ƙirƙira a 2019, wadda kuma Majalisar Dokokin Kano ta rushe a watan Mayun 2023 tare da sauran masarautu huɗu.

Mannir Sanusi ne hakimi na farko da aka naɗa wa Bichi tun bayan sauke Nasir Ado Bayero a matsayin sarkin masarautar ta Bichi.

Sai dai jibge jami'an tsaron ya janyo cikas ga faruwar hakan.

Wakilin BBC Pidgin Abubakar Machiɗo ya ce: "Lokacin da na je na tarar sarki ya riga ya shiga fada. Bayan an yi zama na kamar minti 30 haka, an yi wannan harbe-harben bindiga na al'ada lokacin da yake fitowa.

"Daga nan kuma sai na ga hakimai suna fitowa suna so su fita daga harabar gidan sarki, amma jami'an tsaro ba su bari sun fita ta babbar ƙofar ba. Hakan ya sa ɗaya daga cikinsu ya fita daga motarsa ya tunkari 'yansandan yayin da abokan tafiyarsa suka dinga rarrashinsa, inda daga baya ya koma motarsa.

"Daga baya na ji suna cewa a ɗauko mukullin wata ƙaramar ƙofa. Motocin da na gani sun fita ta wannan ƙaramar ƙofar sun fi 10."

Bayanai sun nuna cewa babu Sarki Sanusi a cikin waɗanda suka yi yunƙurin fita daga fadar.

Sai dai wakilin BBC ɗin ya ce zuwa yanzu babu wani cikakken bayani game da shawarar da fadar ta yanke kan raka hakimin na Bichi zuwa fadarsa.

Me Sarki Sanusi ya ce game da lamarin?

Kamar yadda ya saba lokaci zuwa lokaci, Sarki Muhammadu Sanusi II ne ya jagoranci Sallar Juma'a a babban masallacin Juma'a na birnin Kano.

Yayin da yake gudanar huɗuba, sarkin ya buƙaci mazauna Kano da su yi haƙuri kuma su kwantar da hankalinsu.

"Abubuwan da muke gani, akwai mutane da babu abin da suke nufi da Kano illa su kawo abin da zai haifar da zubar da jini," in ji shi.

"A cikin 'yan watannin baya, wajen kashi shida ko bakwai ana jarrabawa, ana so mutane su fusata su ɗauki doka a hannunsu.

"Jama'a kada a faɗa wannan tarkon. Duk mutumin da ya kawo fitina a Kano, zuwa zai yi ya tafi, dukiyarmu za a ƙona. A daure a yi haƙuri, haƙuri ba tsoro ba ne, a yi addu'a."

Me gwamnatin Kano ke cewa?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A nata ɓangaren, gwamnatin Kano ƙarƙashin jam'iyyar NNPP mai adawa a Najeriya ta ce ta yi "mamaki da ganin wannan mataki da jami'an tsaron suka ɗauka".

Bisa tsarin mulkin Najeriya, kowane gwamna shi ne babban jami'in tsaro a jiharsa, amma kuma ba shi da ƙarfin ikon bai wa 'yansanda da sojoji da sauran jami'an tsaro na gwamnatin tarayya umarni a kowane lokaci.

Sarki Sanusi na samun goyon bayan gwamnatin ta Kano, wadda ta ɗauki matakin rushe masarautun da tsohowar gwamnati ta kafa, wanda hakan ya jawo sauke Aminu Ado Bayero daga kan karagar sarkin Kanon a watan Mayun da ya gabata.

Har yanzu Aminu Ado na kallon kansa a matsayin sarkin Kano, kuma batun yana gaban kotu yanzu haka. Yana zaune a wani ƙaramin gidan sarki da ke unguwar Nassarawa a birnin Kanon, kuma a can ne yake zaman fada.

"Abin da ya ba mu mamaki shi ne, babu wani abu na fargaba ko tashin hankali a jihar Kano," a cewar Sakataren Gwamnatin Kano Abdullahi Baffa Bichi cikin wata hira da gidan rediyon Freedom na Kano. "Wasu tsirarun mutane ne kawai ke so su tayar da zaune a tsaye a Kano waɗanda ke samun goyon baya daga Abuja.

"Sarki ya gayyace mu cewa zai raka hakiminsa ƙasarsa sai muka tashi da jami'an tsaro suna cewa ba za a je ba. Da muka tambaye su sai suka ce umarni aka ba su daga sama."

Sai dai sakataren ya ce suna jiran hukuncin da sarkin zai yanke game da batun. "Duk lokacin da mai martaba ya shirya za mu yi tururuwa mu raka hakimin Bichi," in ji shi.